← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 131

Sashe 85

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna tace, "Haba Binta kin bani mamaki wallahi, na d'auka kece mace ta farko da zakiyi shaida halayen Rauda na kamun kai amma sai gashi kece kika fara furta kalma mara dad'i a kanta. Gaskiya baki kyauta ba bai kamata ki d'auki zugar shaid'an ba har ki furta wannan kalamai akan Rauda." Yaya Shamsiyya duk da k'irjin ta da yake bugawa tace, "Abinda na gani kenan Inna, Umma bai kamata kiyi saurin yadda da abinda akayi kuskure wajan yin sa ba."

Umma dai kanzil bata ce ba Yaya Babba kuma Yaya Ummi da Yaya Nafisa sunyi shiru basa iya cewa komai kowa zuciyar sa cike da tsoro jiran dawowar Baba kawai akeyi.
"Tana ina dan Ubanta!" Baba ya fad'a da k'arfin gaske yana shigowa hannun sa rik'e da zarbad'ed'iyar bulala ya k'arasa wajan Rauda da ta rasa hankalin ta na wucin gadi.

        K'arfi ya saka ya finciko ta babu zato babu tsammani ya ta fara jin saukar bulala, dukan shine ya dawo da ita hankalin ta ta fara kuka yana dukanta duk ta inda yaso amma ta daure hawaye kawai take yi bata ihu. "Ni zaki tonawa asiri Rauda? Me kike nema kika rasa a gidan nan da zaki bari wani yayi miki ciki?. Bikin ki saura kwana goma sha hud'u ki rasa abinda zaki zo mana dashi sai ciki Rauda?" Ya fad'a yana dukan ta da iyakacin k'arfin sa ta ko ina ita kuma tana kuka.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!!" duka matan suka fad'a suna mik'ewa tsaye Umma kuwa kukan tane ya k'aru Inna na zaune kusa da ita dan ta rasa ma bakin magana.  Sautin bulalar Baba kawai ake ji a falon ganin dukan da Baba yake mata yayi yawa zai iya jawo mata matsalar Yaya Fariha ta k'arasa ta rik'e bulalar tana kuka tace, "Dan Allah Baba ka bar dukan ta haka, zama ya kamata muyi muji taya aka samu cikin duka ba shine mafita ba."

Baba yana wuci muryar sa na rawa yace, "Fariha ko ki sakar min bulalar nan kona had'a dake" ya fad'a yana fincikar bulalar ya cigaba da dukanta zuwa lokacin fatar hannun Rauda da bayan ta da k'afafun ta duk sun fashe suna jini amma bai daina dukan ta ba. Sai a sannan ta fara kuka sosai har muryar ta ta dashe sabida kuka Yaya Fariha ta shiga tsakiya wai ko Baba zai daina dukanta amma sai ya had'a da ita dole tayi tsalle ta koma gefe taga ya ajjiye bulalar ya rik'e fuskarta yana marin ta ta ko wanne b'angare.

Bakin ta da hancin ta suka fashe amma Baba bai daina dukan ta ba ganin hakan ya saka matan tasowa a guje suka janyeta suka tura ta d'aki suka kulle k'ofar dukkan su kuka suke har babar Yayar su, Yayar mu ta kalli Baba tana kuka tace, "Kayi hak'uri dan Allah mu zauna da ita aji waye yayi mata cikin, wannan dukan zaka iya kashe ta."

Umma da take zaune tace, "in ta mutu sai me? Mutuwar itace ta dace da rayuwarta a yanzu. Bikinta sati biyu fa kacal ya rage da wanne ido zamu kalli Anas muce masa ciki ne da ita? Me muka yi mata tayi mana wannan sakayyar? Me ta nema ta rasa a gidan nan da zata je ta bawa wani kanta?. Duk lokatun baya da suka wuce batayi ba sai yanzu da yake tana son......." kasa k'arasawa Umma tayi sabida kuka da jirin da take ji duk da a zaune tane.

       A guje Yaya Nafisa tayi kan Umma ganin kamar zata kifa ta rik'e ta tace, "Dan Allah Umma ki daina kuka, k'addara ce ta same mu muyi rokon Allah ya bamu ikon cinye jarabawar."  Umma tace, "So take ta kashe ni kawai Nafisa so take taga an fita da gawata daga gidan nan, in ba haka ba me take so wanda bata dashi a cikin gidan nan?, ina tarbiyyar da ilimin nata suke?. Tsakanina da Rauda Allah ya......." da sauri suka dakatar da Umma wajan fad'in, "Kar ki furta Umma dan Allah kiyi hak'uri, ku tsaya muji uzurin ta wataƙila fyad'e akayi mata."

       Baba ya cillar da bulalar yana wuci ya zauna a kan kujera ya hard'e yatsun sa waje daya yana kallon wani wajan daban yana maimaita kalmar ciki a zuciyar sa, "Rauda tana da ciki kuma cikin shege a cikin gidana, bikinta saura sati biyu taje tayo min ciki dan ta wulaƙanta ni a duniya" sai kuma ya zabura ya sake nufar k'ofar d'akin da suka saka ta da sauri sukayi saurin tarewa yace, "In baku bani hanya ba wallahi zan had'a daku na zane."

"Kayi hak'uri Baba in ka sake dukanta mutuwa zatayi" Yaya Ummi ta fad'a tana kuka sosai. Baba yace, "ta mutu d'in mana daman raywuata bata da amfani a yanzu, gwara ta mutu nasan mutuwa tayi da abinda zai faru nan gaba."

"Asslamu alaikum" aka fad'a daga k'ofa aka shigo duk suka kalli wajan aka amsa a ciki banda Baba da ko gezau baiyi ba balle ya juya, Kawu Badamasi ne da Kawu Mansur suka shigo Yaya Nafisa tace, "Gwara da kuka Baba zai kashe Rauda." Kawu Badamasi yace, "Adamu zo ka zauna ka bar wajan nan."

Baba yace, "in ba kashe yarinyar ciki nayi ba hankalina bazai kwanta ba."
"Kasheta ba shine mafita ba, kazo ka zauna kawai." Kai ya girgiza kai ya juyo da baya ya zauna akaan kujera suma duk suka zauna Kawu Mansur yace, "Nafisa ce ta kira mu ta sanar damu abinda yake faruwa shiyasa muka taso muka zo dan a kamo bakin zaren, duka ba shine magani ba a halin da ake ciki."

Kawu Badamasi ya kalli Umma da take kuka yace, "Haba Binta kiyi hak'uri mana ki daina wannan kukan komai zaiyi daidai in Allah ya amince."
"Meye zaiyi daidai d'in? Ciki fa tayi ba gwara a kashe ta d'in a huta ba."
"Haba haba, me kike cewa haka kamar ba ke ba? Dan Allah ki kwantar da hankalin ki."

Kawu Badamasi yace, "Adamu ba'a neman mafita da duka, ka sassauta zuciyar ka dan Allah a kira ta a tambaye ta wanda yayi mata cikin." Baba ya kalle shi yace, "Bikin ta saura sati biyu yau, da wanne ido zan kalli wanda zata aura nace masa ciki ne da Rauda dan Allah?" Baba ya fad'a muryar sa na rawa kamar zai yi kuka.

Kawu Mansur yace, "in kuma cikin nasa ne fa? Rauda tana da wanda take saurara ne in ba shi ba?." Dukkan su gaban su sai da ya fad'i Baba ya girgiza kai yace, "Anas bazai tab'a aikata wannan d'anyen aikin ba na tabbatar da hakan, sai dai wani daban amma bashi ba."

Kawu Badamasi yace, "Tana ina?." Yayar mu tace, "Tana cikin d'aki Baba yayi mata duka sosai."
"Kuje ku bata magani tasha in anjima zamu dawo sai ta sanar damu koma waye yayi mata cikin. Dan Allah kar wanda ya sake dukan ta, kar kuma wanda yayi mata wata maganar ku k'yaleta taji da abinda take ji itama dan na tabbata babu wanda a cikin ku ya kaita jin ciwon abinda ya faru."

     Rauda da take jin duk abinda da ake cewa kanta ya sake yin nauyi hawayen ma sun tsaya cak tana kwance a kan tiles tana jan numfashi dak'yar kamar zai bar jikinta, kalmar Allah ya isa da Umma taso furta mata tafi komai d'aga mata hankali ta juya idanu bakinta duk jini haka hancin ta zuciyarta na rawa. Me zatayi me kuma zata ce? Da wanne ido zata kalli iyayenta?, da wanne ido zata kalli Anas?. Sai hawaye sharrr tuna yadda yake ta shirin zuwan bikin nan yanzu ashe maaa tana da ciki. "Na shiga uku!" Ta furta kanta na bala'in sarawa gefen idanun ta yayi ja jini ya taru a ciki sabida marin da tasha wajan Baba.

      K'ofar aka bud'e daidai lokacin da take kwara amai tana daga kwance da sauri sakayo kanta suka kamata suka ga tana son kwacewa Yaya Ummi tace, "wayyo ciwon jikin ki ko? Sannu" suka kamata zuwa kan gado suka zaunar, Yaya Ummi ta cire mata hijjabin jikinta Yaya nafisa ta d'ebo ruwa aka goge aman da tayi ta jingina a jikin Yaya fariha tana sauke ajiyar zuciya.

Dukkan su kuka suke tausayin ta ya dirar musu a zuciya Yaya Fariha tace, "Jikinta yayi zafi fa sosai." Yaya Nafisa ta k'araso ta goge mata hancin ta da bakinta da suke a fashe tace, "Ki daina kuka Rauda komai ya faru da Allah jarabawa ce, Allah zai tona asirin wanda yayi miki fyad'e in sha Allah."

Yaya fariha tace, "A bata magani tasha ko zazzaɓin zai sauka." Yaya Ummi tace, "Ina da sudrex a jaka ta bara na d'auko" ta fad'a tana mik'ewa. Yaya Fariha tace, "A'a Yaya Ummi in tasha sudrex zata iya yin miscarriage yayi k'arfi sosai sai dai normal p.c.m." Yaya Nafisa tace, "To ya zube mana, ni naso ma dukan nan da tasha ya zube wallahi kowa ya huta." Akan mudubi Yaya Ummi taga p.c.m ta d'auko aka bata tasha tana sauke numfashi jikinta duk ya fashe sabida duka.

     Kuka ta fashe dashi ta kank'ame Yaya Fariha tana kuka sosai duk suma sai suka sake fashewa da kuka Yaya Fariha itama ta rik'e ta tace, "Ki daina kuka Rauda, ki daina kuka dan Allah." Kukan take sosai ta kasa magana sai kanta da yake harbawa tana jan numfashi kamar zai bar jikinta.

    Yaya fariha ta kwantar da ita suka suka zauna a gefen ta suna ta rarrashin ta duk da ta kasa magana, Yaya fariha ta mik'e tace, "Bara na bawa Ummulkhairi ta siyo mata maganin ciwon jiki" ta fad'a tana fita falon.
Kamar gidan makoki haka falon yake Umma na zaune zazzaɓi ya rufe ta Inna ta kalli Fariha tace, "zo ki duba Umman taku." K'arasowa tayi ta tab'a jin Umma tafi zafi zau ta d'auke hannun ta ta d'auki biro da takarda ta rubuta maganin da za'a siyo har da allurar da zatayi Umma.
Chapter 85 · 0% Book details