Sashe 92
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaban sa ya fad'i jin abinda tace ya zaro idanu yace, "Mama da gaske ya farka? Abbana ya tashi har yana tafiya?. Zanje na ganshi Mama" ya fad'a zai fita tayi saurin dawo dashi tace, "karka sake kaje inda yake, koda wasa kar ka nuna kasan ya tashi bana so yasan na fad'a maka ka rufa min asiri" ta fad'a tana kuka sosai ya rik'e ta hankalin sa duk ya tashi ya zaunar da ita yace, "Shikenan Mamana kwantar da hankali ki babu abinda zai faru, ki daina kuka dan Allah" ya fad'a yana rik'e da ita gabad'aya jikin sa yayi sanyi.
Kuka take sosai yana rik'e da ita har sai da yaga kukan nata ya tsaya Suhaima ta shigo yace ta kula da ita shi kuma ya fita. Har zaije inda mahaifin na yake sai ya tuna mai tace masa sai ya fasa dan baya son abinda zai haifar mata da matsala kamar yadda tace.
*☆☆☆*
"Inna da gaske fa ni ina sonshi zan aure shi indai kin amince" Rahma ta fad'a tana kallon Inna. Inna tace, "kin amince fa kika ce Rahma? Kuna jin abinda take cewa ko?" Inna ta fad'a tana kallon Yayar mu da Yaya Nafisa da Yaya Fariha da kuma Yaya Shamsiyya.
Yayar mu tace, "To Inna tunda tace tana son sa shima kuma yace zai aure ta basai ayi ba. In kika duba Inna samari wahala suke yanzu, y'ay'an masu kud'i ma da kyau da komai suna zaune babu mijin aure ina ga mu y'ay'an talakawa?. Tunda har ya furta a bashi d'in kar mu bari ya sub'uce mana kinga har yanzu fa babu wanda yake zuwa wajan ta."
Yaya Shamsiyya tace, "Nima dai abinda na gani kenan. Tunda kowa yasan asalin yaron nan me zai hana baza'a barta ta aure shi ba tunda dai yana so itama tana so?, mun san sai yafi son Rauda da ita tunda tun farko ita yake so amma duk soyayyar da yake mata in Allah ya rubuta Rahma ce matar sa babu wanda sai canja hakan."
Yaya Nafisa tace, "Inna kawai a amince ayi abin nan, sai mu cigaba da mata addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi." Inna ta sauke numfashi tana kallon su tace, "dukkan ku kun goyi bayan ta aure shi kenan?."
Yaya fariha tace, "To meye aibun hakan Inna?."
"Amma kun san Rauda yake so ba ita ba, bakwa tunanin gori wata rana?."
Yayar Mu tace, "Allah zai kiyaye babu abinda zai faru in sha Allah Inna." Inna tayi shiru kafin tace, "Yanzu dukka sai na fito na cewa y'an uwana zan aurar da Ita nan da kwanaki kad'an masu zuwa? Hakan ai abin kunya ne."
"Babu kunya a ciki Inna, wacece bata da budurwa a cikin y'an uwan naki Inna? Ko wacce kuma burin ta taga ta kawar da ita daga gaban ta tayi aure; mu mun samu meyasa zamu watsar da samun gefe?."
Inna tace, "Shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi." Suka amsa da amin Yayar Mu tace, "Zan sanar da Baba ta amince kema kin amince ayi komai a gama." Inna bata ce komai ba suka cigaba da hira kafin su je wajan Umma.
*Bayan kwana biyu.*
Biki ya gabato ya rage saura kwana biyu kacal d'aurin aure amarya tana ta shagali abinta tunda suka had'u da Anas sau daya bai sake zuwa ba dan jinyar kansa yake dauriya kawai yake yi yana zuwa amma bawai don son ransa ba. Da ya saka addu'a da neman zab'in Allah a kan gaba sai komai yake barin zuciyar sa a hankali yaji yana karb'ar Rahma matsayin mata a gare shi.
A cikin kwanakin dai suna waya kuma babu laifi yana jinta a ransa yana k'ok'arin nuna mata yana son auren nata yana nuna mata ya karb'i k'addarar da Allah ya k'addaro musu itama kuma tana nata k'ok'arin.
Rauda ta tattara komai nata Umma ta tura ta Bauchi gidan yayar ta tace sai an gama komai na biki ta dawo.
Ana ta shagalin biki dangin Umma dana Baba dana Inna kowa yana nuna tasa bajintar daman gidan Amarya an gama zuba komai dan Umma bata ce uffan akan kayan Rauda da suke gidan ba tace dukkan su d'aya ne ita da Raudan.
Ranar lahadi da misalin k'arfe sha d'aya na safe a masallacin cikin gari dubban jama'a suma shaida daurin auren Anas da Rahma akan sadaki naira dubu d'ari. Bayan d'aurin aure ya watse ango yazo gidan su amarya kamar yadda al'ada ta tanada yayi namijin k'ok'ari wajan kawar da komai a zuciyar sa duk da Raudan bata nan.
Anyi shagali sosai kamar ba gidan Baba dan abinda Asad ya aiko dashi a bikin kad'ai ya isa ayi komai na bikin harda canji, aljihun Baba cike yake taf shiyasa da ance babu abu kaza zai bayar a haka aka gama taron biki aka kai amarya gidan ta kowa ya watse.
*Matar mutum kabarin sa.*🥵🥵
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: *Arewabooks @nanahaleema11*
*73*
Kallon Baba Anas yake yi bakin sa yana rawa alamun yana so yayi magana amma bashi da k'arfin guiwar yin maganar sai kallo da yake bin Baba dashi idanun sa kamar zasu fad'o kasa sabida tashin hankali da firgici. Ganin yanayin da ya shiga ya saka Baba sake tausasa murya yace, "Anas nasan dole kaji babu dad'i akan abinda na fad'a maka amma ina so ka fahimce ni wallahi bamu yi maka haka da wata manufa ba, Allah ya sani badan wannan maganar ba auren ka da Rauda yana nan babu fashi. K'addara ta riga fata Anas dukkan mu babu wanda yaji dad'in wannan abinda ya faru, amma babu yadda zamuyi da ikon Allah. Kayi haƙuri bamu yi dan mu wulaƙanta ka ba Anas."
Runtse ido Anas yayi jin abinda Baba ya sake fad'a ya tabbatar masa da ba mafarki yake ba da gaske ne abinda yake faruwa, da gaske ne Raudan sa tana da miji babu damar ya aureta ya sake rasata a karo na biyu. Shiru yayi ya kasa magana jikin sa har rawa yake yi kansa na k'asa idanun sa sun cika da ruwan hawaye ya rasa abinda yake masa dad'i.
Ba k'aramin tausayi ya bawa Baba ba zuciyar sa ta karye dan Allah kad'ai yasan abinda yake ji a cikin zuciyar sa a wannan lokacin hakan ya saka yace, "Sai hak'uri Anas. In kaga abu ya tunkaro bawa gadan-gadan zai same shi sai ya kubce to ka tabbatar ba alkhairi bane a tare dashi, in kaga kana kaucewa abu Allah yana sake mayar dakai wajan koda baka so to tsaya a inda Allah ya kaika wataƙila alkhairi ne a gare ka. Kayi hak'uri nasan akwai ciwo kasancewar ka jima kana son Rauda amma Allah bai rubuta kai mijin ta bane shiyasa ake ta samun akasi a ko wanne lokaci."
Kai Anas yake girgizawa nan take ruwan da ya taru a idanun sa ya sauko kan kuncin sa, hawaye yake wani yana bin wani kansa a k'asa har lokacin Baba ya zuba masa ido kawai shima ji yake kamar yayi masa kukan sabida tausayi zuciyar sa ta karye. Baba yace, "Abinda yasa banyi magana da wakilan ka ba na neme ka kai tsaye ina dan na sanar dakai da kaina kar kaji maganar a bakin iyayen ka kaga kamar an yaudare kane. Amma kayi hak'uri wallahi ita kanta Raudan tana sonka so mai tsanani, auren wani da yake kanta ya saka dole take k'ok'arin cire ka a zuciyar ta kodan gudun fad'awa fushin ubangiji."
Muryar sa na rawa yace, "babu komai Baba, haka Allah ya tsara babu wanda ya isa ya canja faruwar sa. K'addarata kenan zanyi......." ya kasa k'arasawa muryar sa ta sark'e ya sake saukar da kansa k'asa sabbin hawaye suka sake wanke masa fuskar sa. Baba yayi shiru yana kallon ikon Allah ganin namiji mai kyau da kud'i kamar Anas yana kuka da ya rasa y'ar talakawa Rauda. Lallai lamarin soyayya sai dai a barshi, duk wanda kaji yana cika baki a kan soyayya tabbas bai tab'a d'and'ana d'acin sa bane. Duk wanda yasan so yasan ya zafin sa yake, kana tare da wanda kake so d'in ma rad'ad'in sa yana damun zuciyar ka ina ga ka rabu dashi?.
Sai da ya tsaigata kuka sannan ya share idanun sa yace, "Baba babu komai na d'auki hakan matsayin jarabawar ubangiji ina rok'on sa da kyawawan sunayen sa da ya bani ikon cinyewa." Baba yace, "Amin Anas. Kayi hak'uri haka Allah yake tsarin sa, babu ta yarda za'ayi jarabawar wanda ya halicce mu tazo mana da sauk'i dole sai ta tab'a mana zuciya da gangar jiki kodan mu k'ara imani dashi nan gaba. Jarabawar duniya ma wacce wani ne a duniya zai baka sakamako in ka shige ta hankalin ka yake kai kololuwa wajan tashi ina ga wacce mahaliccin kane zai baka sakamakon da kansa?. Kayi hak'uri!" Baba ya sake fad'a a tausashe yana kallon sa.
Shiru yayi yana murmushin k'arfin hali kafin yace, "Babu komai Baba na d'auki k'addara." Baba yace, "Haka ake son dukkan mu'umi ya kasance Anas. Yanzu ya za'ayi da iyayen ka? A sanar dasu?." Anas yace, "A'a Baba, bazan so ace an sake fasa aurena ba a karo na biyu hakan bazai wa mahaifiyata dad'i ba, in na jure ita babu lallai ta iya jurewa. Na amince da tarbiyyar y'ay'an ka da kuma ilimin su Baba, tunda na rasa Rauda ina so a bani k'anwar ta guda d'aya."
Baba ya washe baki farin ciki ya bayyana a tare dashi ya gyara zaman sa yace, "Banda abinka Anas wannan ai abu ne mai sauk'i, na kuma ji dad'in wannan kalami naka har sosai ba kad'an ba. Rahma k'anwar Rauda ce jinin tace sai ta maye gurbin y'ar uwarta a gare ka, wataƙila daman can Allah ya riga ya rubuta itace matar ka ba Rauda ba tunda dukkan lalube muke a cikin duhu."