← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 131

Sashe 48

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jidda ta kalli steps a can gefen falon kai tsaye ta nufi wajan cikin takun isa ta k'arasa inda steps d'in take tana takawa har ta bayyana a saman ta sake karo da lafiyayyen falo wanda sai ka sauka k'asa zaka shiga cikin sa yayi round sai khamshi yake ga sanyin a.c.

falon har yafi na k'asan kyau da tsari girma na k'asan zai fishi ta da manyan kujeru na alfarma kasancewar sa na saukar bak'i. K'ofa guda d'aya rak ta gani a falon kai tsaye ta nufe ta ta bud'e sai gata a doguwar hanya wacce aka mata ado da fulawa na roba masu wuta da dogon carpet jah a jikin sa an rubuta sunan Asad.

       "Woww!" Ta furta a bayyane domin da gaske ya burge ta bada wasa ba. A nan taga k'ofofi sama da guda biyu ta rasa wanne zata shiga a ciki tana wannan tunanin taji an bud'e ta farkon yana fitowa suka had'a ido da ita tana kallon sa yana kallonta, waya ta gani a hannun sa sai taji yace, "Na ganta."

Daga can b'angaren Mama tace, "Yauwa nayi mamaki da kace bata k'araso ba, dan Allah Asad karka bani kunya kaga dai itace zab'ina abinda nake so kuma kana so kayi k'okarin ganin ka sauke hakkin ta da yake kanka, kar ka duba baka sonta ka duba ni ka kuma duba hakki ka tuna kai yanzu babban mutum ne lokacin da zaka fara tara y'ay'a yayi.

     Da hannu ya nuna mata hanya ta rab'a shi ta shiga tana kallon sa da murmushi, baima kula tana murmushi ba tunanin sa ya tafi ga ciwon da ya same shi a Egypt wanda tun lokacin har kawo yau bazai iya d'aukar nauyin ko wacce mace ba bai kuma mayar da hankali sosai akan neman magani ba tunda suka baro can gashi ba jimawa yayi ba aka yi wannan auren, jin bai baice komai ba Mama ta kuma cewa, "Ina fatan babu wata matsalar dai ko?."
"Babu" ya furta a kasalance domin bazai iya furta mata abinda yake damun sa ba gwara yayi shiru da bakin sa kawai tunda mai martaba baya nan ya yiwa kansa magani a hankali.

       "Ka tabbatar babu matsala Asad?." Ya sauke numfashi yace, "Babu Mama." Yana jin sautin murmushin ta tace, "Allah ya tashe mu lafiya, karka manta kasha maganin dana baka na tsari ne suna da mahimmaci sosai domin Abie kafin ya rasu duka su yake sha."
"In sha Allah. A huta lafiya" daga haka ta datse kiran ya sauke wayar daga kunnen sa yana kallon sa.

       Jimm yayi yana kallon k'aton mudubin da yake facing d'insa ya sauke numfashi ya juyo sai ya tsaya cak yana binta da kallon mamaki, ta cire alkyabbar ta ajjiye a gefe daga ita sai rigar bacci bak'a wacce iyakarta guiwa tabi jikinta sosai kana ganin komai na jikinta. D'auke idanun sa yayi daga kanta yaja k'aramin tsaki Allah ya sani ya tsani mace mara kamun kai irin ta in ya tuno yadda suke cafkewa da Aliyu sai yaji takaici ya cika masa zuciyar sa.

Wajan madubi ya nufa ya ajjiye wayar sa ya k'araso inda take ya wuce ta ya shiga band'aki khamshin turaren ta gabad'aya ta dagula masa lissafi, tsigar jikin sa tana tashi kansa na sarawa zuciyar sa na bugawa sabida d'akin da yake ji a cikin ta. Bai jima ba ya fito fuskar sa da ruwa da alama alwala yayi ya kalle ta sai yaga tana murmushi tana kallon sa ya sake kallon ta shi abinda yake nufi taje tayi alwala ita kuma ta d'auka burge shi tayi.

"Barka da dare" ta fad'a cikin murya mai sanyi. Wuce ta yayi jin tama raina masa hankali tun d'azu bata gaishe shi ba sai yanzu zata wani ce barka da dare, a dak'ile yace, "Barka" daga nan yaja bakin sa yayi shiru bai kuma ce mata komai ba. Ganin zata b'ata masa lokaci baiyi sallar i'sha ba ya saka shi tsayawa a kan sallaya yana niyar tayar da iqama sai yaji tace, "Bara nayi alwala nazo muyi banyi sallar i'sha ba."

Tana fad'a ta shiga band'akin ya tsaya ba tare da ya kalle ta ba badan mahimmacin Jam'i ba babu abinda zai saka ya tsaya ta, jim kad'an ta fito ta saka alkyabbar da ta cire mayafin da ta yafa ta kuma yafawa suka tayar da sallah. Sun jima a tsaye yana karatu a bayyane tun tana daurewa har ta k'osa ta fara yamutsa fuska, dak'yar ta kai i'sha d'in nan kafin ya sake mik'ewa dan ta burge shi ta tashi itama taga sunyi raka'a biyu amma ita ba'a jima sosai ba yayi sallama.

Shiru babu mai magana ita binsa take da kallo kawai dan Allah ya sani tana sonsa yana kuma burge ta sosai musamman bakin sa tana ji kamar ta kamo shi ta tsotse bakin sa. kallon yaji yayi yawa a jikin sa ya d'ago ya kalle ta sai ya nuna mata leda da hannun sa kafin ya mik'e tsam ya fita ya bar mata d'akin. Jawo ledar tayi ta bud'e sai taja tsaki ganin abinda yake cikita ture ita ba kaza take son ci ba shi take buk'ata kawai ba wani abun ba.

       Gajiya tayi da zaman ta tashi ta zare alkyabbar ta zauna a gefen gado tana jiran ya shigo amma shiru babu alamun sa ta kasa daurewa ta tashi ta fita ta bud'e d'aya k'ofar ta ganshi a zaune yana duba littafi, k'arasawa tayi kusa dashi ta zura hannayen ta a kafad'ar sa cikin shagwab'a tace, "kazo mu kwanta." Rutse ido yayi ya cize bakin sa ya sauke ajiyar zuciya yana jin wani iri a jikin sa.

Dumin lips d'inta yaji a cheek d'insa a daidai kunnen sa tace, "Come on my king." Bai bari ta fahimci ya shiga yanayi mara dad'i ba ya d'auke hannun ta daga kafad'ar ta ta matso kusa dashi tace, "My king pls." Shiru yayi ya kalle ta kamar zaiyi magana sai ya fasa ya cigaba da duba littafin hannun sa turaren jikin ta gabad'aya ya hautsina masa lissafi.
"I'm coming" ya furta cikin muryar sa mai sanyi ba tare da ya kalle ta ba, bubbuga k'afa ta fara tana turo baki gaba tace, "Please ka tashi muje tare tsoro nake ji na kwanta ni kad'ai."

       Shiru yayi ya cigaba da abinda yake yi ganin yayi mata banza ya saka tace, "zanje ka tawo yanzu dan Allah." Bai bata amsa ba ta fita ya kifa kansa a kan littafin yana jan numfashi dak'yar yana k'ok'arin daidaita kansa.

Bai jima a haka ba ya d'ago kansa ya sauke ajiyar zuciya ya tashi ya fita daga d'akin. Kallon d'akin da take yake yi yana tunani a zuciyar sa domin bai san me zai mata ba in ya shiga, ya fahimci abinda take nema gashi shi kuma bashi da abinda take so d'in babu amfanin shiga hakan ya saka shi sauka k'asa ba tare da ya shiga ba.
   Jidda tunda taji sa shiru kawai taja tsaki ranta a b'ace ta kwanta zuciyar ta na rawa sabida b'acin rai a haka bacci ya d'auke ta.

*☆☆☆*
         Aliyu yana tsaye yana kurb'ar lemo a glass cup yana kallon taga wayar  sa tayi k'ara ya duba ganin mai kiran ya saka shi ya d'auka daga can b'angaren akace, "Ranka ya dad'e an aiwatar da komai kamar yadda kace, na zuba maganin kuma tabbas ya tsallaka a d'azu."
Aliyu yace, "zaka ga alert yanzu, ka tuna in naji maganar a bakin wani....." bai k'arasa ba mutumin yace, "baza ka barni ba."
"Good" yana fad'ar ya yanke wayar yana murmushi.

      "Asad lokaci yazo, lokacin ka ya fara nawa kuma ya kusa fara aiki, nan bada jimawa ba labari zai sha banban da wanda aka saba ji a ko yaushe. Lokaci Asad" ya fad'a yana murmushi ya kurb'i lemon nasa. Wayar sace tayi k'ara ya duba ganin mai kiran ya saka shi ya saka a kunne daga can b'angaren yace, "Allah yaja da ran yarima akwai matsala a binciken mu na d'azu na kira ka ban samu ba sai yanzu."

       "Meye matsalar?."
"Yarinyar da Asad ya saki akwai yuwar dawowar ta masarauta kuma matuk'ar ta dawo komai ya lalace."
"Ta yaya zata dawo?."
"Shine abinda ban sani ba, amma binciken mu ya tabbatar min da akwai yuwar dawowar ta, cikin kashi d'ari akwai tabbacin kashi saba'in na dawowar ta dole a d'auki mataki."

Aliyu yace, "Me kayi game da hakan?."
Yace, "na fara aikin da zan saka ya manta da ita da dangin ta baki d'aya na sanar dakai ne sabida gudun matsala in akwai abinda zakayi a naka b'angaren sai a had'a k'arfi da k'arfe." Aliyu yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "ayi abinda ya dace nima zan san abinda zanyi" ya fad'a yana datse kiran wayar yana kallon tagar d'akin cikin sabon tunani.

Murmushi yayi samo mafitar da yayi a zuciyar sa ya cize baki yana girgiza kai cikin gamsuwa da shawarar da zuciyar sa ta bashi yace, "Asaddddd!" Sai ya yi y'ar k'aramar dariya yana sake taune lab'b'an sa zuciyar sa cike da mugayen abubuwa wanda ya tsara domin kuwa kashe Rauda shine abinda ya fara zuwa zuciyar sa.

*Akwai kura.*

FitattuBiyar
Nana Haleema.
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*050.*

           A zaune take a gefen gado ta shirya cikin doguwar riga ta lace tayi mata kyau sosai fuskar ta a cushe babu walwala hannun ta rik'e da waya a kunne tana magana, yadda take maganar zaka gane da wacce take yi daga can b'angaren akace, "Ke Jidda bana son k'arya fa." Jidda tace, "Wallahi Mum da gaske nake; ni tunani nake ma anya za'ayi abin arzuk'i da mutumin nan?."

Mum tace, "To meya faru haka? Nifa bana so a d'auki lokaci mai tsaho bai mayar dake cikakkiyar matar sa ba dan in hakan ta kasance akwai matsala wallahi."
"Hmmmm ban san meye ba."
"Amma mu bashi lokaci dan jiya ta wuce ai akwai yau ki san yadda zakayi ki tabbatar wani abun ya shiga tsakanin ki dashi kafin kwanaki bakwai d'in nan su wuce, suna da matuk'ar mahimmaci a zaman auren ki dashi bana so a samu matsala Jidda."
Chapter 48 · 0% Book details