← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 131

Sashe 91

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jidda tana kuka ta zube k'asa kusa da Mum tana fad'in, "Mum dan Allah a fara solving problem d'in then sai ki tambaye ni ni kuma zan fad'a miki, in aka tsaya tambaya a yanzu rayuwata tana cikin hatsari Aliyu zai iya aikata min komai, dan Allah Mum ki taimake ni kafin ya kashe ni" ta fad'a tana sake fashewa da kuka ta kifa kanta a cinyar Mum.

Eman da ta shigo taji abinda suke cewa ta zauna a kusa da Mum tace, "abinda Mum take tambaya shi ya kamata ki fara bata amsa, me kika yi masa har kike tsoron hukuncin sa haka?." Mum hankalin ta da yake a tashe tace, "Abinda ya kamata mu sani kenan in yaso sai musan ta inda zamu b'ullowa lamarin, ki duba yanayin da take ciki fa kalli yadda ta rame ta lalace ga ciki a jikinta duk ta koma bak'a kamar ba ita ba. Me kika yi masa haka?."

Jidda ta d'ago kanta daga cinyar Mum tace, "Mum kawar da Aliyu shine abinda ya kamata a fara yi ba wannan tambayar ba, in abinda nayi masa ya bayyana ba ni kad'ai ba hatta dangin ki da dangin Daddy sai abin ya tab'a su. Dan Allah ayi gaggawar kashe shi tun kafin shi ya kashe mu." Mum ta kalli Eman itama ta kalle ta kafin Mum ta kalli Jidda tace, "Ikon Allah! Bakin ki bazai iya fad'a laifin ba kenan kome?."

"Fad'ar bata da amfani! Jinta sai iya tarwarsa kunnuwan ku Mum, ku tabbatar an kashe Aliyu in ba haka ba dukkan ku sai zuciyar ku ta kusa bugawa nan gaba" ta fad'a da ihu tana cigaba da kuka kafin ta baje a kan carpet tana kuka sosai tama manta akwai ciki a jikin ta.

Eman tace, "ki sanar da mijin ki mana na tabbatar zaiyi maganin sa tunda sama yake da kowa a garin nan." Jidda da take kuka a kan carpet ta d'ago ta kalli Eman sai ta sake kwantawa tana cigaba da zubar da hawaye. Hankalin Mum ya kai k'arshe wajan tayi idanunta a waje take tunanin wanne irin laifi mai girma Jidda ta yiwa Aliyu haka da ta tsorata da hukuncin da zai mata...?

        Jin yadda take kuka sosai ya saka Mum tace, "Taso nan Jidda" ta fad'a tana bata hannu ta rik'e ta mik'ar da ita ta zaunar da ita kusa da ita ta dafa kafad'ar ta tace, "Aliyu ne bakya so ki gani a raye ko?." Kai ta d'aga da sauri hawaye na sauka daga idanun ta wani yana bin wani tace, "Eh Mum, rayuwar sa barazana ce ga tawa rayuwar, zai tarwatsa min dukkan plan d'ina Mum."

Mum ta girgiza kai tace, "Shikenan za'ayi maganin sa kar ki damu. Ko meye za'a yi akan a ga bayan sa indai hakan zai saka hankalin ki ya kwanta." Rungume Mum tayi tana kuka bata ce komai ba Mum tana shafa bayan ta zuciyar ta cike da zullumin ranar da laifin da ta yiwa Aliyun zai bayyana, yadda taga ta tsorata sosai abin ya bata tsoro tana da tabbacin akwai wani abun a k'asa, amma meye? Wanne irin laifi ne mai girma haka?.

*☆☆☆.*

         "Kai wallahi Fulani mai babban d'aki ce take tawowa, yanzu ya zamuyi gashi waziri yace kar mu bar kowa ya shiga b'angaren nan? Bamu isa mu hanata ba" mai tsaron k'ofar ya fad'a yana kallon d'an uwan sa wanda yaka tsaye a kusa dashi. Kafin suyi wani yunk'uri Mama ta iso wajan ita da jakadiyar ta a bayan ta dole suka zube a k'asa suna gaishe ta ta d'aga musu hannu ta nufi ciki jakadiyar ta ta tsaya a baya.

Mama tana shiga d'akin da mai martaban yake kwance taga kan gadon wayam babu kowa a kai gabanta ya yanke ya fad'i ta dafe k'irji tana kallon d'akin aka bud'e k'ofa aka shigo, Uncle ne ya shigo ganin ta a tsaye duk sai ya rude yace, "Ranki ya dad'e yaushe kika shigo?."

"Yanzu na shigo? Ina mai martaba?" Ta fad'a tana sake kallon gadon tana kallon sa. Kafin yayi magana mai martaba ya fito daga band'aki fuskar sa duk ruwa da alama alwala yayi suka had'a ido da Mama ta tsaya cak tana kallon sa shi kuma ya d'auke kansa ya zauna a gefen gadon ya d'auki wayar sa da take gefe yana dubawa.

Kallon Uncle tayi ta kalli mai martaba ta sake kallon uncle ta sake dawo da kallon ta ga mai martaba da yayi kamar bai ganta ba yana zaune ya gefen gadon yana amsa waya. Ta juya ta sake kallon Uncle sai taga ya bud'e k'ofa ya fita ya kulle k'ofar ta sake kallon mai martaba da mamaki mai d'auke da tsoro hadi da al'ajabi.

Takowa take yi zuwa kusa dashi shi kuma ya d'auke kansa tamkar ma bai san da wata hallita a wajan ba har ya gama wayar ya ajjiye wayar ta k'araso kusa dashi ta zauna kusa dashi tace, "Mijina kai nake gani ko kuma idona ne yake min gizo?." Idanun sa ya d'ago suka had'a ido ya d'aure fuska matuk'a sai ya sake d'auke kansa daga kanta. Idanun ta suka ciko da kwallah ta kwantar da kanta a kafad'ar sa tana hawaye tace, "Mijina kayi min magana dan Allah, kai nake gani ko mafarki nake yi."

Hannayen sa ya saka ya d'agota daga jikin sa suka had'a ido yayi kamar bazai magana ba kafin yace, "ba mafarki kike ba nine dai da kaina." Sai ta rud'e ta rike hannun sa tana fad'in, "Tun yaushe mijina ya farka ban sani ba? Ka san adadin damuwar dana shiga akan rashin lafiyar nan taka amma shine har zaka tashi kana tafiya ba'a sanar dani ba?."

Hannun sa ya kwace daga rik'on da tayi masa ya hard'e hannun a k'irji yana kallon ta yace, "Kina so na farka ne daman?." Yadda ya kafe ta da ido sai ta kasa magana ta diririce ta rasa me zatace ta sunkuyar da kai ta d'ago ta rasa me zata ce, ganin hakan sai yayi murmushi yace, "tashi ki koma inda kika fito, sannan umarni nake baki kar wani ko wata yasan da wannan labarin koda wasa, in kuma akasin hakan ya faru ranki ne zai b'aci dan nasan ke kad'ai kika sani."

"Mijina ina zanje?." Ya kalle ta yace, "Inda kika fito nan zaki koma, bana son sake ganin ki a wajan nan har sai lokacin da kowa zai san na farka zaiyi. Asad, Aliyu, Hydar ban amince dukkan su su san da wannan maganar ba, in kuma naji a bakin su na tabbatar ke kika fad'a." Sai ta fashe da kuka tana kallon sa murya na rawa tace, "Mijina dan Allah ka yafe min nasan nayi abubuwa da yawa a bayan idanun ka, nayi ne sabida...."
"Son zuciyar ki ko?" Ya katse ta da fad'ar hakan yana kafe ta da idanun sa masu kwarjini.

Shiru tayi ta sunkuyar da kanta tana kifta idanu yaja dogon tsaki yace, "baki fara ganin komai ba Rabi'a, baki ga komai ba a cikin abubuwan da kika shuka yanzu kika fara girbar su. Tashi ki bani waje bana son ganin ki gabad'aya." Jiki a sanyaye ta mik'e tana tafiya kamar mara laka ta juyo ta kalle shi taga bama ita yake kallon ba tace, "Dukkan abinda na aikata nayi nadama bazan sake aikata makamancin su ba."

Bai amsa ba dole ya saka ta fita yaja tsaki ya lumshe idanun sa dukkan abinda ta aikata suna dawo masa cikin kansa ya cize baki shi kam bai tab'a ganin mace makira kamar ta ba. Uncle ne ya shigo d'akin ya kalle shi yace, "Mubarak taya aka bar Rabi'a ta shigo a wannan lokacin?." Uncle yace, "Ranka ya dad'e na fita ta shigo su kuma masu tsaron k'ofa baza su tab'a iya hanata shigowa ba, da ace ina nan ne zan san yadda zanyi na dakatar da ita to bana wajan."

Mai martaba yace, "Bana tunanin zata iya shiru da bakin ta ba tare da ta fad'awa y'ay'anta ba, fad'a musu daidai yake da lalacewar komai." Uncle yace, "Babu abinda zai faru in sha Allah mai martaba, Allah ya wuci zuciyar ka." D'auke kai yayi kana yace, "Ina Asad yaje?." Uncle yace, "Babu wanda yasan inda ya tafi." Abba ya sauke numfashi yana girgiza kai yace, "komai yazo k'arshe."
Uncle ya amsa da fad'in, "Da izinin Allah."

        B'angaren Mama kuka take sosai a kan gadon ta, bata tab'a jin dana sani akan abubuwan da ta aikata ba sai a wannan lokacin da ta tabbaatar mijin ta yasan duk wani target d'inta nasan ganin bayan kowa akan burinta.  Tunawa da wani abun sai ta zabura ta fara zagaye d'akin tana girgiza kai tana fad'in, "A'a bazai san ni na aikata wannan laifin ba, bazai sani ba, in ya sani na shiga uku na lalace" ta fad'a tana d'ora hannun ta a kanta tana cigaba da zaga d'akin hankalin ta a tashe tsoro ya bayyana a tare da ita.

Sai ta koma kan gadon ta zauna tana kuka tayi tagumi, "shin ina y'ay'a mazan da nake alfahari dasu?" Ta tambayi kanta dan dukka su uku bata san inda suka suke ba balle ta neme su. Kai ta dafe zuciyar ta na farbawa da sauri-sauri zazzaɓi yana neman rufe ta tunda mai martaba ya farka bata da kwanciyar hankali dan tasan daidai yake da tonuwar dukkan asirin ta wanda ta jima tana b'oyewa.

K'wankwasa k'ofar da akayi ya saka ta kalli k'ofar bata bada umarni ba aka shigo ganin Hydar ne ya saka ta mik'e ya k'araso inda take da sauri ta rik'e shi tana fad'in, "Mahaifin ku ya farka Hydar, naje na same shi a zaune yana magana har yana tafiya. Meyasa zai farka yanzu? Meyasa sai da komai ya lalace min zai tashi?" Ta fad'a tana rik'e Hydar shima ya rik'e ta dan yaga kamar bata hankalin ta.
Chapter 91 · 0% Book details