Sashe 15
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A b'angaren Rauda sun bata ruwa tayi alwala a inda take sun nuna mata yadda zatayi sallah tayi duka wanda ake binta ta idar suka kawo mata tea tasha, yadda suke kula da ita baza kace mara lafiya bace abin ya burge ta duk da ta d'auka matsayin Asad shine ya saka suke mata haka dan taga duk sun sanshi bata san haka tsarin asibiti yake hatta na Nigeria kula da mara lafiya a wuyan nurses yake.
Bata jima sosai ba akayi sallar asuba tayi sallah a zaune kamar d'azu bayan ta idar ta kalli gefen ta taga wayar ta ta d'auka ta shiga Islamic app ta fara karatu kamar ko yaushe. Bayan ta gama ta shiga wajan hotunan wayar tana kallon haukan su Khalil a wayar ta tana murmushi tana jin kewar su a zuciyar ta sosai. Tana cikin farin cikin kallon y'an uwanta ya shigo ya canja kaya cikin suit fara tas tayi masa kyau sosai ya k'araso ya zauna a gefen ta yana kallon fuskar ta da take ta murmushi har lokacin ta kalle shi tace, "Ina kwana."
Kafin yayi magana tace, "Da sauk'i. " Da mamaki yake kallon ta ta kalle shi tace, "nasan zaka ce ya jikina ne shiyasa na hutar da kai nace da sauk'i." Kyakykyawan murmushi yayi wanda ta jiyo sautin sa a inda take ta sake kallon sa da mamakin abinda ya bashi dariya haka shi kuma yadda tayi saurin amsa abinda bai tambaya ba shine ya bashi dariya wato tasan abinda zai tambaya kenan, sai ta sake burge shi sosai da alama dai tambayar bata mata dad'i shiyasa tayi saurin tare shi.
"Ya kika tashi?" Ya furta in slow voice yana binta da fararen idanun sa masu d'auke da boyayyiyar k'aunar ta wacce shi kad'ai yasan da ita a zuciyar sa. D'ago kai tayi ta kalle shi cikin mamaki suka had'a ido har lokacin fuskar sa da murmushi a kai sai ta sauke kai k'asa tace, "lafiya lau." Murza yatsun hannun sa yayi suka bada sauti ta d'ago ta kalle shi ya nuna mata k'afar ta alamun ya take ji, "babu ciwo" ta fad'a a nutse tana kafe shi da nata idanun a son ranta sai dai ya d'auke nasa ita baza ta d'auke ba amma suna had'a ido sai ta sauke nata k'asa jin wani abu yana shigar ta.
Waya ya d'auko daga aljihun sa yana dannawa ba jimawa ya mik'o mata ta karb'a a hankali dan tsoro take kar wayar ta sub'uce a hannun ta tayi masa asara gata da santsi, fuskar Baba taga ya bayyana akan screen d'in tace, "Lah Baba kaine?." Daga can b'angaren yace, "Nine Rauda, ya jikin naki ance anyi miki aikin?."
Farin ciki ya bayyana a kan fuskar ta tace, "Babu ciwo Baba kamar ba'a yi min komai ba. Ina kwana."
"Lafiya lau Rauda ya zaman misra?."
"Lafiya lau, Ina Ummana?."
"Gata ku gaisa."
Fuskar Umma ta bayyana sanye da hijjabi ta sake fad'ad'a fara'ar ta tace, "Umma na ina kwana." Daga can b'angaren itama da fara'a a tare da ita tace, "lafiya lau Rauda, ya jikin naki?ance har anyi aikin k'afar taki."
"Umma babu ciwo kamar ba'a yi min komai ba. Umma kinga yadda suke kula dani kamar ba mara lafiya ba kamar wata matar shugaban k'asa?, ga asibitin mai kyau Umma kamar ba'a duniya kake ba."
Umma tayi dariya tace, "kedai shirman ki yawa gare shi Rauda, ya mijin naki?."
"Mijina kuma? Au ashe fa ina da miji wallah8 mantawa nake Umma. Yana nan yadda yake Umma ko magana fa baya yi sai yaga dama daga ya jiki sai sannu shikenan, wani lokacin kamar na shak'o wuyan sa haka nake ji, yana da kayan haushi ni mantawa nake miji nane badan kin fad'a ba."
"Lallai baki da hankali Rauda; duk fad'an da nayi miki bai shiga kunnen ki ba." Rauda ta share zancen tace, "Umma ina Ummulkhairi ina Khalil dasu Rahma? Wai Umma yaushe ma Baba yayi babar waya nidai nasan ba'a video call da k'aramar waya sai babba kuma dai nasan Baba bazai fitar da kud'i ya siya ba." Umma tayi dariya tace, "Mijin kine ya bashi kafin ku tafi sabida mu dinga ganin ki kema kina ganin mu."
Rauda tace, "Allah sarki angode Allah ya saka masa da alkhairi."
"Amin. Shiyasa nace ki dinga masa biyayya banda rashin kunya Rauda."
Sai kuma tayi dariya sosai tace, "Daman dai nasan wallahi duk wahala Baba bazai siyi waya ba, da ya siya ai gwara ya ajjiye kud'in yana kallon su." Umma tayi tsaki kad'an tace, "In ya siya sai ki kwace." Rauda tace, "Ina k'annena suke Umma?."
"Yanzu basa nan da sun dawo anjima sai ku gaisa."
"Toh shikenan Ummana, nayi kewar ku wallahi sosai."
"Muma munyi Rauda, Allah ya baki lafiya. A cigaba da biyayya banda rashin kunya Rauda banda tsiwa nasan halin ki."
"Umma wai wa zan yiwa rashin kunyar?, Tabd'ijam wannan mutumin ba sai naga fuskar yi masa bama, kofa magana baya min sai yaga dama shima sau d'aya kawai in yace ya jikin ki basai sake cewa komai ba" ta fad'a bayan ta gwada muryar sa tana yamutsa fuska zuciyar ta na karyewa kamar zatayi kuka.
Umma tace, "kina addu'ar dana fad'a miki? Duk da nasan ki bakya wasa da addu'a amma dai ki dage."
"Ina yi sosai Umma" ta fad'a murya na rawa."
"To meye kuma na kukan bayan alqwarin da kika yi min kin daina? Haba kodai daman alqawarin bai kai zuciya ba?." Ido Rauda ta goge bata ce komai umma tace,
"Kuma kina jin komai na barin zuciyar ki?."
"Eh Umma."
Umma tace, "to ki dage nan gaba sai dai ki bada labari. Baki ga abinda ya aiko mana dasu ba ga ginin gidan mu an kusa gamawa baki ga ginin da akayi ba kamar ba'a unguwar ba, bamu da bakin gode masa ai sai addu'a ko iya haka aka tsaya, balle shi da yaga jinin mu yace yana so duk da tazarar da take tsakanin mu dashi, dan Allah Rauda ki cigaba da hak'uri."
Rauda tayi murmushi bata ce komai ba kafin Umma tace, "ke ni na gaji sai anjima" ta Fad'a tana k'okarin yanke wayar da sauri Rauda tace, "Ina kewar ki Ummana, a gaida min dasu Khalil ace ina kewar su sosai, in Yaya Ummi tazo suyi min magana ta Whatsapp mu gaisa dasu."
Da to Umma ta amsa ganin Raudan ta fara hawaye sai ta kashe wayar itama ta ajjiye wayar a k'irjin ta ta jingina da bango ta lumshe idanun ta cikin kewar y'an gidan su da k'aunar iyayen ta.
Asad da yake jin ta duk abinda take yi yana kallon ta jin yadda take ta magana a kansa ta bashi dariya, wai baya magana daga ya jiki shikenan lallai da gaske ya jikin nan tana bata haushi. Murmushi yayi ya shafa kansa sosai ta bashi nishad'i da farin ciki sosai a zuciyar sa musamman in ya tuna yadda take kwaiwayon muryar sa sai ya sake yin dariya yana kallon ta dan yaga alama ta manta dashi a wajan shiyasa ta saki baki.
"Waya ta" ya furta a hankali yana mik'a mata hannu. Da sauri yaga ta firgita tana kallon sa ta wara idanun ta alamun ta tuna da b'aranb'aramar da tayi kunya ta kamata ta kasa koda motsi ta d'auke kai daga kansa ba kuma ta bashi wayar ba, godiya take yiwa Allah da yasa bata furta bata son sa gaban idanun sa. Ganin hakan sai ya matsa daf da ita sosai har tana jin numfashi sa da khamshin turaren sa ya kai hannu k'irjin ta inda wayar take yana kallon ta yana sake matsar da hannun sa zuwa jikin ta.
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*034.*
Hannu ya saka ya d'auki wayar sa a k'irjin ta yaja baya kamar bashi ba ya koma danna wayar sa hankali a kwance kamar ma bashi ne ya kalle ta ba, kunya ta da lullub'e Rauda tunawa da sakin bakin da tayi ta manta shaf yana zaune gefen ta sai ta kasa d'ago kai balle ta iya kallon sa. Bai kalle ta ba ya mik'e tsaye yace, "Byeee" abinda ya furta kenan ya d'aga k'afa da niyar fita sai kuma ya dawo da baya ya dawo kanta ya tsaya yana kallon fuskar ta da take a duk'e ya matso kusa da ita ya sunkuya a goshin ta ya sakar mata lafiyayyen kiss kafin ya kai ga d'agowa aka shigo d'akin.
Muhibba da ta shigo taga abinda akayi amma bata kawo komai ba dan tasan Sister d'insa ce da yayi mata kiss a goshi ba komai bane ya d'ago ya sake tamke fuskar sa ta kalle shi da murmushi tace, "Morning Prince." In ya kalle ta ma ta gode Allah ya kalli Rauda suka had'a ido tayi saurin d'auke kanta ya fita ba tare da ya sake cewa komai ba. Muhibba ta bishi da kallo tana lumshe idanun ta Allah ya sani yana burge ta sosai jan ajin sa yana d'aya daga cikin abinda yaja hankalin ta gare shi.
Rauda ta kalla tayi mata murmushi tace, "ya jikin ki?." Rauda ta kalle ta tace, "Da sauk'i." Daga haka bata ce komai ba ta juya ta fita Rauda ta bita da kallon mamaki kafin ta tab'e baki ta saka hannu ta shafa saman goshin ta har lokacin tana jin sanyin lips d'in ta a kai sai abin ya bata dariya.
*Nigeria*
*3:00pm.*
A wannan lokacin jirgin Asad ya sauka a Nigeria yana fitowa ya samu Hydar yana jiran sa ya k'araso ya shiga motar yana duba wayar sa, Hydar ya kafa masa ido yana kallon sa har ya tsargu ya kalle shi yayi masa alama da lafiya sai Hydar yace, "gani nayi kayi kyau kwana biyu kawai ga wani annuri akan fuskar ka."
"Mtswww!" Shine abinda Asad ya furta kawai Hydar yayi dariya yaja motar bai tsaya a ko ina ba sai a mtn office.