Sashe 19
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Asad d'ana ne meyasa za'ayi min haka?" Ta fad'a cikin kuka tana kallon sa. Baice mata komai ba ta had'a kai da guiwa tana kuka tana hasashen irin matakin da zata d'auka domin babu abinda zai hana ta raba auren koda nata auren zai mutu sai dai ya mutu bata damu, babu abinda zai hana d'aukar mataki koda za'a d'auki mataki a kanta itama, koda zai zama silar mutuwar kowa sai ta raba Asad da Rauda domin ruwa ba sa'an kwando bane ba.
*☆☆☆*
_Asad Mama tasan komai a yanzu, kasan abinda zakayi kafin ta raba ku, ka cigaba da addu'a dan tabbas Mama bazata barku lafiya ba. Matsayina na d'an uwan ka ina baka shawarar ka amince da matar ka ka maida ta cikkakiyar matar ka kafin lokacin ya k'ure mana._ sake maimaita message d'in Asad yake yi kansa na sarawa ambatar Mama da yayi a cikin sakon da aka turo masa. Da sauri ya fita daga wajan message ya shiga call log da niyar kiran Mama amma sai ya tsaya cak ya dafe kansa a bayyane yace, "me ma zanyi?."
'Hydar.' Zuciyar sa ta bashi amsa ya danna number Hydar a maimakon ta Mama har lokacin hannun sa yana rik'e da kansa da yake ji yana yi masa ciwo. Hydar bai d'auka ba ya kalli Rauda a kan gado yaga tayi bacci ya tashi ya fita yana sake kiran wayar Hydar, a karo na biyu ya d'auka bai bari Asad d'in yayi magana ba yace, "Mama tasan komai Asad daga yau zuwa ko wanne lokaci komai zai iya faruwa, ban so taji labari da sauri haka ba amma kasan yanayin gidan namu ba ko wanne sirri ne yake b'oyuwa ba especially da ya kasance Aliyu ya san komai."
Asad ya dafe kansa kana yace, "Maamaaa!." Hydar jin sunan da ya ambata ya saka yace, "eh, lokacin da nayi maka message d'in nan ta kira ni kamar zata dake ni tana fad'a min bakin mu d'aya nasan inda kake nace ban sani. Asad ka rik'e matar ka i mean ku zama d'aya kai da ita kafin Mama ta raba ku da ita." Asad ya sake cize bakin sa kafin yace, "why nake jin wani iri in ka kira Mama? Why ban kira ta cikin kwanakin nan ba?, why in na d'auki waya zan kira ta nake forgetting Hydar?."
Hydar yace, "ban sani ba Asad, ka dai cigaba da addu'a kamar yadda ka saba amma akwai tarin qalubale a gaban ka, sai ka cire wannan rashin son maganar taka ka rik'e matar ka yadda koda za'a raba ku za'a sha wahala" Hydar yana gama fad'a masa haka ya yanke wayar bai jira mai zai kuma ce masa ba.
Asad ya tafi duniyar tunani yana so ya gano dalilin da ya saka in ba ambatar Mama akayi ba mantawa yake da ita bayan a baya ba haka yake ba, inda akwai wacce yake tunawa a ko wacce dak'ik'a Mama ce, meyasa yanzu baya jin hakan a kanta a wannan lokaci?.
"Hello handsome." Muhibba ta fad'a a gefen sa tana tsayawa kusa dashi tana kallon sa. Bai kalle ta ba domin baya cikin yanayi mai dad'i ko kad'an daman itama tasan bazai yi magana ba tace, "zan iya taya ka hira?." Asad bai kalle ta ba ta sake yin murmushi tace, "na fad'awa sister ka sak'o ta fad'a maka I hope ta sanar da kai?." Kai ya dafe da hannun sa guda d'aya yaja k'aramin tsaki baice mata komai ba ya d'aga k'afa da niyar tafiya.
Hannun sa ta rik'e hakan ya saka shi tsayawa cak ya juyo ya kalle ta sai ta saki hannun nasa tana kallon idanun sa tace, "I love you!." Bai ce komai ba ya bar mata wajan ita kuma ta bishi da kallo tana murmushin farin ciki, ita kallon sa ma kawai nishad'i yake bata balle kuma yayi mata magana.
Asad fita yayi daga asibitin yana niyar shiga mota yaga kiran mai martaba bai d'auka ba ya shiga motar ya zauna sannan ya d'auka ya saka a kunne yayi sallama muryar sa a sanyaye mai martaba ya amsa kana yace, "Babar ka tasan komai Zaki, kar hakan ya dame ka ka saka a zuciyar ka komai Allah ya rubuta sai ya faru, ko meye zai faru kar ka baro k'asar nan ba tare da umarnina ba kaji ko?." Asad ya d'aga kai kamar yana gaban sa dak'yar ya iya furta, "In sha Allah."
"Ka cigaba da addu'a komai zaizo da sauk'i cikin ruwan sanhk, Babar ka bata isa tayi abinda Allah bai nufa ba komai ya faru Allah shine ya tsara faruwar sa."
Baice komai ba Mai martaba yace, "a cigaba da addu'a" yana fad'a masa hakan ya yanke wayar Asad ya sake cire wayar da sauri da niyar kiran Mama amma sai ya samu kansa da nemo number Hafiz ya dafe kansa ya manta abinda zaiyi kawai ya kifa kan a kan sitiyarin motar yana furzar da iska mau zafi.
*☆☆☆*
Mama kwanan zaune tayi ko kad'an bacci yak'i zuwar mata ido da ta kulle idon ta sai ta hango Asad da Rauda a kwance a waje d'aya sai ta bud'e ido a zabure tana cize bakin ta. Mai martaba yana lura da ita bai kuma ce mata komai ba.
Asuba nayi yana fita masallacin cikin gida Mama ta zabura ta fito daga b'angaren sa ko sallar bata yi ba ta burin ta kawai ta ganta a b'angaren ta tana shiga a haukace hadiman ta na gaishe ta amma bata bi ta kansu ba ta shiga cikin d'akin ta ta kulle kanta.
Hannun ta na rawa ta d'auki waya ta kira Asad amma wayar bata shiga ta canja akalar kiran ta kira Mum hankali a tashe, Mum bata d'auka ba ta cillar da wayar tana zagaye d'akin cikin neman mafita, tayar da sallah da taji anyi shine ya saka ta yin alwala sallar ma ba'a nutse tayi ta ba tana idarwa ta mik'e ta fita zuwa d'akin Suhaima. A bakin k'ofa suka had'u da alama zata je gaishe tane tace, "Barka da asuba Mama." Mama bata amsa ba tace, "sako hijjabin ki zamu fita yanzu." Suhaima da mamaki tace, "Mama Ina zamu je da asuba?."
Kallon da tayi mata ya saka ta yin shiru tana bin maman nata da kallo ganin ta firgice kamar ba ita ba tace, "Mama lafiya naga kin koma wani iri?." Cikin tsawa tace, "Kiyi abinda nace kawai Suhaima, kije ki sako hijjabi zamu fita!." Da sauri Suhaima ta koma ciki ta sako dogon hijjabi akan kayan baccin jikin ta tana fitowa Mama ta bata key na mota tace, "ki fita da motar zan fito ta baya na same ki."
"Mama amma Abba ya hana ni yin driving" ta fad'a tana karb'ar key d'in.
Hannu takai da niyar marin ta Suhaima tayi baya da sauri ta fita tana mamakin abinda ya samu Mama haka.
Duk a tsorace Suhaima take kar Takawa ya ganta dan ya hana ta jan mota balle kuma da asuba haka, a haka ta fita da motar zuwa can bayan gidan dan tasan ta nan Mamaa zata b'ullo tana zuwa kuwa ta ganta tsaye Suhaima na tsayawa ta bud'e gaban motar ta shiga Suhaima taja motar ba tare da tasan inda suka nufa ba.
Tsoron yi mata magana take yi gashi bata san inda zasu je ba haka take mik'ewa kawai tana tafiya Mama kuma na gwada wayar Mum har lokacin bata d'auka ba, tsaki tayi ta kalli Suhaima tace, "kiyi kwana" ta fad'a tana nuna mata inda zata bi Suhaima ta bi wajan suka cigaba da tafiya.
Sunyi tafiya mai nisa sosai domin Suhaima ta d'auka ko Mama ta manta hanyar ne amma babu damar tambaya tayi shiru har suka k'araso wata ruga ta fulani da babu mutane sai gidajen k'asa suma sai ka irga su ta bata umarnin tsayawa, bud'ewa tayi ta fita Suhaima zata fito tace, "kiyi zaman ki ina zuwa." Ta fad'a tana shiga cikin gidan da tazo da Sauri Suhaima ta bita da kallo.
A zaune ta same malamin da yana jan carbi sallamar ta ya saka ya mik'e yana fad'in, "Ranki ya dad'e, Allah yaja zamanin ki, ya raya mana y'an uku yasa su mulke mu. Kece da kanki da sassafiya haka?." Mama bata iya amsawa ba ta zauna tace, "Ina cikin tashin hankali ne da dole na fito yanzu." Malamin ya zauna yace, "to ranki ya dad'e meya faru?."
"Mahaifin Asad ne ya d'aura masa aure da yarinyar da muka zo wajan ka kwanaki ba tare da sanina ba."
Malamin yayi murmushi yace, "Daman na fad'a miki auren su da wahala in bai yu ba, datse shi abu ne mai matuk'ar wahala." Tace, "Yanzu haka suna Egypt tare da yarinyar." Farantin gaban sa ya jawo ya fara duba k'asar gaban sa na wani lokaci kafin yace, "Tabbas suna can, yanzu haka gasu nan tare suna tafiya shi da ita amma kamar bata da lafiya na gani."
Hankalin Mama ya sake tashi tace, "babu ta yadda za'a raba su ya dawo gida? Bana k'aunar ta ko kad'an." Ya sake bincikawa yace, "akwai kuma babu, hanyar da za'a bi wajan raba su dole sai an jira lokaci domin kuwa akwai d'an katanga a yanzu da kafin a rusa ta dole sai an jira."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanzu ko kashe tane baza'a iya yi ba?."
"Za'a iya ranki ya dad'e, amma a ganina abi wata hanyar domin kafin a samu wannan nasarar ma za'a jima dan na fad'a miki tana da rik'o da addini ba komai ne zaiyi saurin tasiri a kanta ba."