← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 131

Sashe 1

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*026.*

Gaban ta ya fad'i k'irjin ta ya fara duka da sauri-sauri ta cire wayar daga kunnen ta ta kalla taga number sabuwa special mai sauk'in haddacewa ta sake mayar da wayar kunne ko zata ji an kuma magana amma shiru ba'a ce komai ba kuma har lokacin ba'a katse kiran ba. Sake cire wayar tayi ta kalla taga dai har lokacin tana tafiya ta sake mayarwa amma still shiru ba'a cewa komai.

Ta bud'e baki zatayi magana aka riga ta ta hanyar fad'in, "Don't confuse yourself." Zak'in maganar sa take ji har sassan jikin ta hakan ya saka ta yin shiru ta kasa magana tana jin maganar sa na zaga ko ina na jikinta ta lumshe ido ta bud'e kafin ta daidaita kanta tace, "waye yake magana ban gane ba." Baice komai ba daman kuma bazai ce ba taji an yanke wayar ba tare da an sanar da ita ba tabi wayar da kallo har lokacin k'irjin ta bai daina bugawa ba.

_Ina sonki._ abinda akace ya fad'o mata a rai ta sake kallon number zuciyar ta cike da mamakin wanda ya kira ta kuma bai fad'a mata waye ba ya kashe, tsaki taja tana so ta kawar da tunanin ko waye a ranta amma abin yaci tura ta zubawa waje d'aya ido kalaman da aka fad'a mata suna yi mata yawo a cikin kanta ta kasa kawar dasu daga kwakwalwar ta.
Tana so ta tuna inda tasan muryar amma ta kasa tunawa dan kamar a waya ta banbanta da wacce ta sani a zahiri hakan ya saka ta kawar da tunanin daga kanta ta kwanta a hankali kalaman Anas nayi mata yawo a a zuciyar ta da gangar jikinta.



"Mum yanzu me hakan yake nufi? Ana nufin ina ji ina gani Asad zai auri wata bani ba ba?" Jidda ta fad'a tana kallon Mum hankali a tashe. Mum tace, "nace ki kwantar da hankalin ki nice fa mahaifiyar ki, Asad bashi da wata mata in ba ke ba a duniyar nan."
"Amma naji kina min wata magana daban."
"Eh ya furta yana sonta amma asiri suka masa dan in kika ga yarinyar mai gadin gidan nan ma bazai d'auka ba balle Asad."

Jidda tace, "Mama ban damu da kyanta ko munin ta ba kawai ki sanar dani ni an ajjiye a gefe kenan?." Mum ta fusata tace, "Na fad'a miki ki kwantar da hankalin ki kece matar Asad ba ita ba, yadda nake miki tanadin yadda zaki mallake shi ko uwar sa bata isa ba balle wata banza a gefe da ta shigo yanzu. Asad naki ne ke kad'ai daga ke sai dangin ki dan haka ki nutsu wannan auren ba mai yuwa bane ba."

"Ta ya za'a fasa bayan kince yana sonta?."
"Ita bata son sa ai."
"A ganin ki Mum zak'i amincewa da tayin Asad ne?. Yana da kud'i, yana da kyau ga sarauta taya zata ki amince masa?." Mum tayi shiru kafin tace, "ko ta amince ko kar ta amince bata isa ta mallake shi ba, naki ne ke kad'ai zan iya yin duk abinda zanyi wajan ganin kin zama mallakin Asad koda kowa baya son hakan. Sai na juya Rabi'atu kamar yadda take juya mutane tafin hannun ki nake so Asad yazo ana zuwa wannan b'angaren zance ya k'are."

Jidda tayi bata ce komai ba tana girgiza kanta dan ita maganar ba wata shigarta tayi sosai ba tunda taji ance yana son yarinyar take jin kishinta a zuciyar ta, k'wafa tayi kafin ta tashi ta bar falon ta hau sama. Da kallon Mum ta bita tana k'iyasata abinda zata aikata akan lamarin dan ko da tsiya koda tsiya-tsiya Asad bazai auri Rauda ba y'ar ta zai aura, ko yana so ko baya so.

*◇◇*

Hydar ne zaune a gaban mai martaba shi kuma yana duba littafi a hannun sa kafin ya ajjiye yace, "Ina jinka Hydar." Hydar yace, "Allah ya k'ara maka lafiya Mama tana neman hana Asad auren wacce yake so, tana k'okarin cusa masa ra'ayin k'inta duk da yana sonta ya sanar dani zai iya barin ta sabida Mama. Abba meyasa Mama take yiwa Asad haka dan ya kasance me yi mata biyayya a ko wanne lokaci?."

Mai martaba yayi murmushi ya kashingid'a yace, "Mahaifiyar ku tana da wani hali wanda sai kuna taya ta da addu'a Allah ya cire mata shi daga cikin halayen ta in ba haka ba zata sha wahala yanzu ko nan gaba. Tana amfani da biyayyar da yake mata tana hana shi abinda yake so a ko wanne lokaci dan cikar burinta kawai, amma wannan karon bazan zuba ido ya rasa abinda yake k'auna ba wanda na tabbatar da alkhairin da yake cikin abinda yake so d'in zan nuna mata gaba da gaban ta. Kai ka tabbatar da yana sonta?."

"Na tabbatar da wannan takawa, yana k'aunar ta sosai zan iya cewa itace mace ta farko da Allah ya d'ora masa k'aunar ta. A idanun sa in ana maganar ta mai martaba zai tabbatar da abinda nake fad'a, yana sonta so mai tsanani."
"Ikon Allah kenan. Babu damuwa zan yiwa tufkar hanci kafin ta farga, sai dai ta farka daga dogon bacci ta tarar aikin gama ya riga da ya gama. Gobe kaje kazo min da mahaifin yarinyar zan sanar dakai inda zaka kai shi." Hydar yace, "Allah ya kaimu goben. A huta lafiya" ya fad'a yana tashi ya fita mai martaba ya bishi da kallo.

Ajiyar zuciya mai martaba ya sauke ya kalli gefe guda abubuwa da dama sun cushe masa a kansa da kuma zuciyar sa, shi kansa zai so ayi auren Asad da gaggawa kodan ya cika mutum bashi mulkin ya huta gabad'aya, zai kuma tsaya wajan ganin Asad ya samu abinda yake so a karon farko in sha Allah.

A b'angaren Mama lokaci d'aya ta fize ta rame sabida tashin hankalin da take ciki wanda ta d'orawa kanta, hankalin ta gabad'aya baya tare da ita tana zaune ta zubawa tv ido a zahiri sai ka d'auka kallo take amma ba kallon take ba ta tafi duniyar tunani.
"Mama!." Suhaima ta fad'a daga bayan ta tana k'arasowa kusa da ita ta ta zauna a k'asa kusa da k'afar tana kallon ta. Bata amsa ba hakan ya saka Suhaima tace, "Dan Allah Mamana ta daina saka damuwa a cikin zuciyar ta dan Allah, in Allah ya rubuta yarinyar da ake magana a kai matar sace sai ya aure ta kenan babu amfanin damuwa akan lamarin. kuma....." Kallon da Mama tayi mata ya hanata k'arasawa ta tashi daga kusa da ita cikin tsoro ganin irin kallon da take mata tsaf zata iya bugeta.

"Kar na sake jin wannan maganar a bakin ki matuk'ar kina buk'atar kwanciyar hankali na da naki kwanciyar hankalin, in kuma kina son b'acin raina ne sai ki fara daga yanzu. baza ta zama matar Asad ba da ganin wannan ranar gwara ganin ranar mutuwa ta!" Ta k'arasa fad'a tana kallon Suhaima. Suhaima tace, "Allah ya zuci zuciyar Mama, tuba nake" ta fad'a tana barin wajan tana waiwayon ta.

Da sauri Mama ta d'auki waya ta kira layin Mum ana d'auka bata jira anyi magana ba tace, "ya maganar mu?." Daga can b'angaren Mum tace, "Da nace a bari sai zuwa jibi sabida kar ayi saurin gano muna da hannu a ciki." Mama tace, "A gano mana sai me?! Me zasu iya yi mana?, kiyi gaggawar aiwatar da komai a yau bana so a samu matsala, a b'atar da yarinyar nan daga duniya gabad'aya hankali na zai fi kwanciya!" Bata jima mai Mum zata ce bama ta yanke wayar tana wuci.

Ta kwashe sama da awa biyu a zaune a wajan har dare yayi tana zaune ganin kiran Mum ya saka ta d'auka tace, "Good news please." Mum tace, "na tura wanda zasu shiga gidan, yanzu haka ma sun tabbatar min da suna cikin gidan sun samu mafaka jira suke dare yayi su aiwatar da komai." Mama tace, "kar ki kuma kirana sai an tabbatar an kashe ta" tana fad'a ta yanke wayar ta ajjiye a gefen ta.

Suhaima da take jin komai gaban ta ya fad'i ta zaro idanu waje tare da dafe k'irjin ta ta wuce Maman da sauri ba tare da ta kula da ita ba ta fita zuwa b'angaren su Asad. A haukace ta shiga falon taga Hydar a zaune yana kallon ball ta kalle shi tace, "Yaya Hydar ina Yaya Deaf?." Kallon ta yake ganin ta a firgice yace, "meye kike neman sa?, lafiya kike?."
"Mama ce ta tura a shiga gidan su yarinyar nan a kashe ta."
"What!" Hydar ya furta yana wara idanu tare da mik'ewa tsaye yana kallon ta yace, "Wacce yarinya?."
Suhaima tace, "Wacce Yaya Asad yake so."

"Ke kin tabbatar da abinda kike fad'a kuwa bana son hauka" ya fad'a yana kallon ta a firgice jin abinda baiyi tsammanin ji ba. Girgiza kai tayi tace, "Allah abinda naji tana fad'a a waya kenan, dan tace kar a kuma kiran ta sai an tabbatar an kashe yarinyar. Kayi wani abu bro bana son hakkin kisa ya rataya akan Mama." Asad da ya shigo falon yaji abinda ake fad'a ya kalli Hydar kafin yayi magana ya juya da sauri ya fita.

Da sauri Hydar yabi bayan sa amma kafin ya k'arasa ya shiga mota yaja har ya fita daga gate na biyu ya nufi na farko dole shima ya d'auki tasa motar ya shiga yabi bayan sa da gudu. yayi mamakin gudun da Asad yake yi domin bai ganshi ba alamun yayi nisa sosai dole shima ya ware motar yana binsa a guje.
Chapter 1 · 0% Book details