← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 131

Sashe 100

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A firgice ya kalli Rauda yana nuna ta da yatsa yace, "Eh tabbas ni yazo gidan ku ba shine nan nazo, rubutun sa da kika gani a takarda computer ve ta d'ora a k'asar Dubai ina sane da duka abinda yake faruwa tsakanin ku a Cairo hatta magana in yayi miki ina jin me yake cewa domin kuwa na canja azurfar hannun sa na saka masa wacce take d'auke da na'ura a jikin ta a Kano lokacin da muka je jana'izar Abie, duk abinda yake fad'a ina ji a haka nasan dukkan abubuwan da suke faruwa tsakanin ku. an tabbatar min akwai yuwar dawowar ki masarauta kuma zaki iya zama barazana a gareni shiyasa nayi maganin ki tun kafin ki shigo dan bana son ganin wani abu da zai dakatar dani daga burina" ya fad'a yana zaro mata ido kamar zai dake ta.

Mama da take gefe ta mik'e hankali a tashe tazo inda Aliyu yake ta rik'e shi tana kuka tace, "Aliyu me kake fad'a haka?." Ya kalle ta ya wara idanun sa waje yace, "Eh Mama nine na sake ta, sannan kuma nine na zauna da Jidda matsayin Asad cikin jikinta kuma nawa ne! Domin kuwa babu abinda ya tab'a had'a su da Asad na bata maganin da zata lalata masa mazantarka sa kuma ta bashi yasha ya kuma yi aiki, kamar yadda kikayi aiki aka lalata a lokacin da yake Cairo tare da matar sa!. Ni ne na shirya komai nine nan na tsara kuma nake tafiyar dashi yadda nake so!" Ya fad'a da ihu yana kallon Mama da take rik'e da wuyan sa ruwa har sakkowa yake daga cikin idanun sa.

"Nayi k'ok'arin iya komai na Asad duk da wani lokacin ina yin ba daidai ba" ya kalli Mama ya nuna ta yace, "Kin tuna lokacin da kika ce min na canja kamar bani ba? Eh tabbas ba Asad d'in bane nine ina yin iya yadda zan iya ne wajan ganin nayi tamkar Asad amma ban iya yi ba wani lokacin. Dalilin sakaci da addu'a ta k'awar ki ta samu galaba a kaina a tunanin ta Asad ne. Dalilin ni ba Asad bane shiyasa kika kasa samun abinda kike so a wajena, Asad mai biyayya ne kina juya shi yadda kike so ni kuma bazan lamunci wannan biyayyar ba shiyasa kike ganin canji da yawa cikin lamari na. Ni na shirya, na tsara nake kuma aiwatar dashi yadda nake so."

"Ba kai bane Aliyu, d'auka kake kaine ka shirya kake kuma aiwatarwa amma baka d'auki kashi d'aya a cikin kaso d'ari na cikin abinda suka aikata ba. Kai kanka a k'asan su kake baka san komai ba kana yin komai bisa umarnin su" Mai martaba ya fad'a yana kallon sa shi Kuma yana kallon Mama.

Mama tace, "A'a k'arya kake Aliyu ba gaskiya kake fad'a ba, ka daina cutar kanka kana fad'ar abinda ba gaskiya ba."

*Wai! To su waye wad'annan?🏃🏼‍♀️*
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*079*

Mai martaba ya murmusa jin abinda Mama tace yace, "Koma ki zauna zaki ji komai." Jikin ta a salub'e ta zame hannunta daga jikin Aliyu ta koma ta zauna tayi tagumi zuciyar ta na bugawa sosai.  Mai martaba yace, "Cigaba da bayani Aliyu."

Aliyu yace, "Daga wannan lokacin ni kaina bazan ce ga abubuwan da suke faruwa ba, na rasa tunanina bana gane komai sai Jidda kawai. Daman akwai plan d'in daina kirana da Aliyu sai dai Asad da yake tana so sunan ya shiga bakin ta ko sau d'aya bata tab'a kuskuren nunawa ba Asad bane ba ni" ya fad'a yana dafe kansa tare da runtse ido. Mai martaba yayi murmushi mai kyau ya girgiza kansa yana kallon kowa da yake zaune a falon.

Zaiyi magana kenan aka turo k'ofa aka shigo ganin wacce ta shigo ya saka gaban Waziri fad'uwa ya kasa d'auke ido daga kanta ganin ta garau da ita babu alamun ma tayi hatsari sai yaji tsoro gaban sa ya fad'i. "Munafukin Allah dole ai kaita kallona ka so kashe ni Allah baiyi ba" Hajiya ta fad'a tana kallon sa itama.

Dawo da kallon ta tayi ga Mai marataba tace, "Allah yaja da ranka zan fad'i dukkan abubuwan da muka k'ulla nida Waziri da wata boyayyiyar abokiyar shirin sa, ya saka a kashe ni a daren jiya dan kar wannan ranar tazo bai san ina sane na saka likitan yace ace muku naji mummunan ciwo ba dan kawai ya sakankace bani da lafiyar da zan halarci wannan zaman ba."

Kowa ya kalli waziri da yake zare ido aka kalle ta Mai martaba yace, "An baki fad'i duk abinda yake bakin ki." Ta nemi waje ta zauna tace, "Duk wani abin da yake faruwa a cikin masarautar nan nida shi mune muke k'ullawa dan cikar burin mu kawai, burina kar jinin Rabi'atu ya mulki garin nan shi kuma burin sa ya mulki garin nan. Burin mu iri d'aya ne shiyasa muka had'a kai wajan ganin bayan y'ay'an Rabi kodan cikar burin mu."

Mama da take jin me take cewa ta runtse ido tace, "Daman ku biyun nan na jima da sanin shirin ku na kashe min y'ay'a tun suna k'ananu, na jima da sanin kuna bak'in ciki da kyautar su da Allah ya bani. Shiyasa lokacin da kika so kashe shi ta hanyar bashi guba a zogale......" Hajiya ta katse ta tace, "Bani na bashi guba ba a wannan lokacin yana da kyau ki amince da nayi tabbas zan fad'a a yanzu dan yau lokacin fad'ar komai ne" ta dawo da kallon ta ga Mai martaba tace, "Ban san wanda ya bashi guba ba, abinda na sani munyi shirin hakan yafi sau babu adadi Allah bai bamu sa'a ba. Tabbas da tace tun suna yara nake so na kashe su haka ne domin ranar da aka haife su sai da naje wajan malaman tsibbu suka bani tabbacin dukkan su zasu tashi basu da amfani a masarautar sannan hankalina ya kwanta."

Fulani Hajiya ta kuma cewa, "Nida shi da wata wacce ake kira master planer wacce ni ban santa ba shima kuma bai santa ba, sai kuma d'ansa Suhail wanda yake bamu gudunmawa sosai wajan ganin bayan Asad. Mun bawa Suhail laya ya sakawa Asad a k'asan katifa ba sau d'aya ba ba kuma sau biyu ba, mun bashi ya bashi a ruwa yasha ya kuma ci a abinci duka burin mu na ganin bayan sa amma babu nasara. Akwai wani lokaci da daddare da Asad ya jini ina waya ina zancen a kashe shi da naga yaji a take na saka a busa masa yaji a idanun sa yadda bazai ga wacece ba. Asad ya amince dani amma munci amanar sa koda yake Aliyu ma yana cikin tafiyar mu" ta fad'a tana kallon mai martaba.

"Ban sani ba ko shirin sane kwanciya rashin lafiyar ka domin kuwa yana aikata abubuwa wanda ban san dashi ba amma ni bani da hannu a ciki wallahi, abinda na sani kawai mun saka Suhail ya shiga jikin sa ta k'arfi yana saka shi duk abinda muke so a kuma lokacin da muka so. Shirina gabad'aya akan Asad ne da y'an uwan sa amma banda Mai martaba da mahaifiyar sa" ta fad'a kanta a k'asa idanun ta na cikowa da kwalla.

Ta kuma cewa, "Tunda naji da kunne na yana niyar kashe ni naji komai ya fitar daga cikin raina, a lokacin da ya saka a daki motar da nake ciki daga nan na sake tabbatar da cewa ramin mugunta kurarrare ne kuma rana d'aya ta b'arawo rana d'aya tak ta mai kaya. Naso ganin bayan Asad sai ban ga bayan sa ba wanda muke k'okarin ganin bayan wani tare dashi ashe nima yana k'ok'arin ganin nawa bayan. Na sanar da mai martaba komai abinda yake faruwa ko wanne hukunci da ya cancanci ayi min a shirye nake dana karb'e shi."

Falon yayi shiru babu wanda yake magana a cikin su sai mai martaba da yayi murmushi yana kallon su kafin yace, "Dukka shirin ku na sani Sa'adatu, keda Yazuha da wacce baku sani ba hatta Suhail d'in na sani. Ko Suhail?" Ya fad'a yana kallon Suhail da yake zaune a gefe ya tankwashe k'afar sa kansa a k'asa.

Murmushi Suhail yayi kawai baice komai ba kafin mai martaba ya kuma cewa, "Yazuha wacece master planer?." Waziri da ya dabarbarce ya fara zare idanun sa gumi yana keto masa kana kallon sa kasan yana cikin tashin hankali sosai ba kad'an ba, ganin ya kasa magana sai ya d'auke kansa ya kalli Asad da yake zaune yace, "Asad akwai magana a bakin ka, ka k'arasa warware abubuwan da suke faruwa dan mu sani."

Asad ya sauke numfashi ya kalli mutanen falon gabad'aya ya lumshe ido ya buɗe cikin muryar sa mai taushi da kwantar da hankali yace, "Kamar yadda kuke d'auka Suhail yana cutar dani ba haka abun yake ba, duk wani shiri da kuke dan ganin bayana Suhail yana sanar dani ne yana kuma taimaka min dan ganin na tsira daga dukkan shirin ku shiyasa baku tab'a nasara ba domin kuwa kafin ku aiwatar na sani ni kuma na d'auki mataki. Yana amfani da kune yana jin sirrin ku da abinda kuke k'ullawa a kaina amma bai tab'a cutar dani ba" ya furta cikin muryar sa ta ko yaushe a tausashe yana kallon Waziri da Hajiya.

Hajiya tace, "kar ka amince da dad'in bakin Suhail wallahi dashi ake k'okarin ganin an kashe ka." Asad yayi murmushi yace, "a zahiri kenan, amma a bad'ini baya tare daku yana tare dani. Na amince da Suhail fiye da yadda ba amince da y'an uwana na jini."

Mai martaba yace, "kuna so kusan wacece master d'in da ku kanku baku Santa ba? Kuna so kusan wanda ya jefa ni a cikin rashin lafiya sabida son zuciyar sa?." Kowa ya zuba masa ido masu sunkuyar da kai duk suka sunkuyar da kai ganin hakan sai mai martaba yace, "ban san me zance bane, ban kuma san me zanyi ba. Rabi'atu ta cutar da y'ay'an ta dukkan su sabida son zuciyar ta da kuma burin da ta d'auka ta d'orawa zuciyar ta."
Chapter 100 · 0% Book details