← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 131

Sashe 66

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Tana shiga falon ta hadimai suka zube ta kalle su tace, "Asad ya zauna a fada?." Hadima d'aya tace, "Eh ranki ya dad'e, amma ya shiga ciki yanzu." Bata ce komai ba ta shige ciki tana shiga d'aki tayi wanka ta shirya cikin shigar alfarma duk da bata jin dad'i sosai amma hakan bai hanata yin kwaliyya ba.

Tana zama a k'aramin falon ta Hydar da Suhaima suka falon suka zauna kusa da ita Hydar yace, "Barka da dawowa Mama, da fatan an sauka lafiya?." Numfashi ta sauke kana tace, "Alhamdulillah. Ku taya d'an uwan ku addu'a." Hydar yace, "Muna yi masa Mama" ya fad'a yana dafe kansa ta kalle shi cikin tsoro tace, "Ya dai? Ko ciwon ne?." Girgiza kai yayi kawai ta koma ta zauna tace, "yana ina yanzu?."
"Yana ganawa da bak'in da suka zo daga Cairo." Shiru Maman tayi bata ce komai ba.

"Ina so na ganshi nasan bazai zo nan ba." Jin yadda tayi maganar cikin sanyi duk sai ta basu tausayi Hydar yace, "Allah wuci zuciyar mahaifiyar mu. Kiyi haƙuri komai tsanani yana tare da sauk'i." Tayi murmushin takaici kana tace, "Zanje da kaina" ta fad'a tana mik'ewa dole suma suka mik'e suka rufa mata baya zuwa b'angaren sa zuciyar su cike da tunanin abinda zai biyo baya a can.

         Lokacin da suka je ya gama ganawa da bak'in ba hadimai gabad'aya yana niyar hawa saman sa kenan Mama suka shigo ya juyo yana kallon su, ya bada umarnin kar wanda ya shigo masa b'angaren amma babu wanda ya isa ya hana Mama shigowa yasan shiyasa aka barta ta shigo ya lumshe ido ya bud'e ya dawo da baya ya k'araso inda take ya duk'a har k'asa kamar ko yaushe yace, "Barka da Rana."

Ajiyar zuciya tayi tana jin ruwa yana taruwa a idanunta ta dafa kansa da yake cikin rawani yellow wanda ya amshi fuskar sa tace, "Asad" ta fad'a tana d'ago k'afadun sa ya mik'e tsaye tana kallon fuskar sa sai taga ya sunkuyar da kai kamar yadda ya saba a wancan lokacin tace, "Asad kana lafiya?."

Zaiyi magana kenan aka shigo b'angaren ko basu juya ba sun san wacece dan babu wanda zai shigo wajan daga su sai ita sai maganar ta maqale ya fasa Mama ta kalle ta ta ga ta d'aure fuska ta kalli Asad tace, "Wacece ni a wajan ka?." Yayi shiru na d'an lokaci kafin yace, "Mahaifiyata" yadda ya furta sai da suka kalle shi duka domin a sanyaye yayi maganar sosai.

Mama ta sauke numfashi tace, "Na isa dakai kamar lokacin baya Asad?." Ya girgiza kai yace, "Matsayin mahaifiyata baya tab'a canjawa." Ta kalle shi ta kalli Jidda tace, "Nasan kai shugaba ne koyi ya kamata mutanen cikin gidan nan dana waje suyi dakai akan komai, amma dole ce ta saka zan saka ka aikata abinda zan fad'a domin zama da ita ba alkhairi bane a rayuwar ka, ban damu da maganar mutane ba indai zaka zamu lafiya shine burina. Dan haka Ina baka umarnin ka saki wannan yanzun nan!" Ta fad'a yana nuna masa Jidda da yatsan sa.

Juyawa yayi ya kalli Jidda suka had'a ido yaga tana murmushi ya dawo da kallon sa ga Mama ya sake kallon Jidda sai ya kasa cewa komai ya sauke kansa k'asa zuciyar sa tana bashi umarnin aikata abinda Mama tace amma harshen sa da gangar jikin sa sun k'i bayar da wannan damar. Mama ta kuma cewa, "mahaifiyar ka nake shiyasa nace ka sake ta nasan baka tab'a tsallake umarni na a ko yaushe. Ina so ka sake tabbatar mata da na isa da kai yanzun nan ba anjima ba ka sake ta Asad."

Kai ya saukar k'asa sosai ya sauke numfashi zuciyar sa naso ta furta amma maganar tak'i zuwa harshen sa, dak'yar ya iya tattaro abinda yake bakin sa yace, "Allah ya wuci zuciyar Mama na, bazan iya sakin ta ba!."
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*059.*

           Yadda Mama ta k'ame 'kam tana kallon sa da alamun mamaki a tare da ita mai had'e da tsoro da firgitarwa da tashin hankali had'i da rud'ani take kallon sa, tashin hankalin da ya shiga jikinta har a kan fuskar ta ya bayyana k'arara ta kasa furta komai sai kallo da take binsa dashi shi kuma kansa yana k'asa baice komai ba. Bakin ta har rawa yake yi tace, "Asad....!."
"I'm sorry Mama ina so na aikata abinda kika ce amma bazan iya ba, ina neman izinin tafiya" ya furta a sanyaye bai jira ta bashi umarnin ba ya juya ya hau sama ta bishi da kallo jiri yana d'aukar ta.

Baya tayi zata fad'i Suhaima tayi hanzarin rik'e ta shi kansa Hydar ya daskare a wajan kallon inda Asad yabi kawai yake yi hankalin sa a tashe tsoro ya mamaye masa zuciyar sa, murmushi Jidda take yi daga gefe kafin ta k'araso inda Mama take tace, "Har abada bazai tab'a iya sakina ba, zai iya rabuwa da dukkan ku amma bazai iya rabuwa dani ba, In ma tunanin da kike kenan is better ki ajjiye shi sabida bazai tab'a faruwa ba ko yanzu ko nan gaba. Zaku iya tafiya zanje wajan mijina na taimaka masa yayi wanka ya huta."

Mama idanun ta a lumshe yake bata iya magana ba Suhaima zatayi magana Hydar ya hanata dan baiga amfanin maganar ba suka rik'e Mama suka fita sabida mutane ma ta k'ofar baya suka bi zuwa b'angaren Mama dan har lokacin suna rik'e da ita jiri take yi.Kafin su isa zazzaɓi ya lullub'e Mama suna ajjiye ta falo Hydar ya kira Dr ya sanar dashi emergency yake son zuwan sa.

Duk suna zaune kusa da ita ba jimawa yazo Hydar ya bada damar shigowar sa ya shigo ya fara auna BP Mama, sai da ya kammala ya bata magani ya kalli Hydar yace, "Ranka ya dad'e jinin Fulani ya hau sosai fiye da tunanin ka, inda akwai abinda yake damunta ayi gaggawar ganin ta rage damuwar ta in ba haka ba akwai matsala gaskiya."

Sallama sukayi da Hydar bayan ya bata magani ya tafi ya dawo kusa da ita yace, "Mamana muje d'aki ki huta." Taimaka mata sukayi ta tashi zuwa d'aki ta kwanta a gefen gado idanun ta rufe sai a lokacin suka lura kuka ma Maman take yi. Basu iya cewa komai ba ta kwanta suka kullo mata d'akin ko wanne jikin sa a sanyaye.

Hydar ya kalli Suhaima yace, "Wanne mataki kike ganin zamu d'auka akan Jidda?." Suhaima tace, "wanne mataki kenan Yaya Hydar? Mama fa ita take son Jidda ita ta saka ya aure ta ta raba shi da wacce yake so, ni daman wallahi sau da yawa na kanyi tunanin kamar akwai wata manufar da Mum take zaune da Mama a lokacin dana fad'a mata bazata amince ba sai dai ma raina ya b'aci. Yanzu kuma sun fito da asalin kalar su, waccen matar tasa yana sonta haka Mama ta raba su yanzu kuma gashi tana so ya rabu da wacce baya so yace bazai ba."

"Kinga Suhaima wannan ya wuce, meye mafita yanzu da zamu taimaka masa?."
"Addu'a mana, asiri suka yi masa wallahi dan in ba asiri ba banga abinda zai raba Mama dashi ba. Sai dai mu taya ta fad'awa Allah ya kawo sanadin raba su dan in ka lura yanzu ibadar sa ta ragu."

Hydar yayi shiru yana saukar da numfashi yace, "Zan sanar da abokan sa na Madina su taya shi Addu'a nima zan nemo maganin da za'a dinga bashi ba ko Allah zai taimake mu ya warke, matsalar kuma in an nemo ma basha zaiyi ba." Suhaima tace, "in muna Addu'a zai sha wata rana ai. Kawai dai mu dage da addu'a in ba haka ba wallahi sai gidan nan ya gagari Mama zama wata rana, ka duba har jinin ta ya hau in aka cigaba ban san me zai faru da Mama ba." Hydar ya girgiza kai ya fita ya bar Suhaima a wajan.

*☆☆☆*

         "Mum kin san bata jima da fita ba na fito nazo nan wai ya sake ni." Mum tace, "What! Ya sake ki?."
"Wallahi Mum, kuma yau yadda yayi mata magana cikin biyayya yayi mata ni na fara jin tsoro wallahi kar wata rana tayi galaba a kansa fa."

Mum tace, "kice sai an sake nemo mafita kenan, in aka cigaba da haka wata rana zatayi nasara. Ta bazama nema masa magani yau ma daga Kano ta dawo wajan malaman su nacan akan matsalar in muka bari ana haka tabbas wata rana namu zai karye. Dole a samo mafita."
Jidda tace, "abinda ya kamata ayi kenan Mum dan ni na tsorata wallahi, yadda yayi mata magana a sanyaye ya bani tsoro. wacce mafita za'a samu?."
Mum tayi shiru tana kallon wani wajan daban zuciyar ta na kawo mata wani abun kafin tace, "Kashe ta za'ayi Jidda!."

A firgice Jidda ta mik'e tsaye idanun ta a waje tace, "Mum kisa?." Mum ta kalle ta tace, "dallah malama zauna kar ki tara min jama'a" ta fad'a tana jan hannun Jiddan ta zauna har lokacin idanun ta a waje Mum tace, "Nutsu."  Jidda ta had'd'iye yawu cikin tsoro tana kallon ta Mum tace, "Dan nace a kashe ta kika wani firgita kamar nace ke za'a kashe?, in tana duniya wallahi wata rana sai ta raba ku dashi. Kar kiga shi shugaba ne a tsarin gidan sarauta sarki baya saki ke bama sarki ba ko wanda suke a k'asan sarki basa saki to wallahi sai ta nemo hanyar da zata raba ku, shu'uma ce duk yadda kike tunanin ta ta wuce haka."
Chapter 66 · 0% Book details