← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 131

Sashe 64

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama cikin firgici tace, "Hasbunallahu wani'imal wakil! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" ta fad'a tana dafe kanta da yake juyawa ya kuma cewa, "A halin yanzu yayi sakaci da rok'on Allah kamar baya shiyasa abin yake tasiri a tare dashi, bazan miki k'arya ba karya wannan tsafin na jikin sa ba abu bane mai sauk'i dole sai an had'a k'arfi da k'arfe wajan rok'on Allah, ma'ana sai an samu manyan malaman addini da dama an had'u ana yina addu'a sannan za'a samu nasara."

Mama kamar zata zubar da hawaye tace, "Kafin wannan babu abinda za'a iya yi?."
"Akwai ranki ya dad'e, zan bada ruwan rubutun da zai dinga sha amma sai dai a jira a rubuta a wanke a yanzu tunda ban san da zuwan ki ba in sha Allah zai rage wani abun tunda ayar Allah ce."
"Wanne malamai kake ganin za'a samu akan wannan?."

Ya sauke numfashi kana yace, "akwai wani babban malami sai dai ya tsufa sosai a cikin garin nan yake zaune Allah ya yi masa ilihamar iya karya tsafi ko asiri da ayoyin Allah da kuma maganin hausa." Mama ta gyara zama tace, "Ina zan ganshi?."
"Zan bincika ranki ya dad'e in yana nan zan sanar dake sai aje wajan sa."
"Ina jiran ka dan Allah kar kayi wasa."
"In sha Allah ranki ya dad'e. Bara na saka ayi rubutun" ya fad'a yana mik'ewa ya fita.
Ta jima sosai a gidan ta fito da jarkar rubutun tana jiri ta shiga motar Suhaima taja suka koma gida.

*☆☆☆*

      Baba ne ya lek'a d'akin Umma ya ganta ita da Rauda yace, "kuzo munyi bak'o" yana fad'a ya juya ya fita Umma da Rauda suka fito ko wacce ta saka hijjabi zuwa k'aramin setroom d'in baban. Hydar suka gani a zaune shida Baba ganin su ya saka shi yin murmushi yace, "Mai ciwon k'afa jiki yayi kyau sosai."

D'aure fuska tayi ta zauna sai Umma ce tace, "Wallahi fa, jiki ya jima da warkewa ai." Ya kalli Umma yace, "barka da yamma." Umma tace, "ya mutanen gidan?."
"Alhamdulillah. Rauda ya gida?" Ya fad'a yana kallon ta. Fuska a d'aure tace, "Alhamdulillah."

Hydar ya numfasa yace, "kuyi hak'uri da abinda ya faru d'azu in sha Allah bazan bari hakan ta kasance ba, a tak'aice nayi maganin abun in sha Allah baza su sake zuwa gidan nan da niyar wani abun ba." Baba yace, "to ma sha Allah mun gode sosai. Amma dan Allah meye dalilin sa na sakawa ayi mana wannan wulaƙancin?."

Hydar yace, "kuyi hak'uri kawai Baba, gabad'aya ya canja dana je na same shi akan maganar sai yace shi na bar maganar ya tsane ku ne baya son ku baya son dangin ku gabad'aya. Amma......" Rauda ta katse shi da fad'in,  "Amma me? Ka sanar dashi yadda ya tsane mu wallahil azim muma haka muka tsane shi bama son sa bama qaunar wani nasa. Har yana da bakin da zai ce ya tsane mu duk abinda aka yi mana mu bamu ce haka ba sai shii?. To ina so kayi masa albishir muma mun tsane shi dashi da dangin sa gabad'aya, dashi da babu ko nace dashi da banza duka d'aya suke a wajan mu, ka kuma tabbatar ka fad'a masa wallahi bai isa ya wulaƙanta ahlina na k'yale shi ba sai inda k'arfina ya k'are!" Ta fad'a a fusace tana kallon Hydar shima ita yake kallo da mamakin ta..........
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*058.*

          Jin yadda tayi maganar a fusace Baba ya kalle ta yace, "Rauda meye haka ne wai?." Shiru tayi tana girgiza kai jin abinda Baba yace Hydar ya cize baki yace, "Babu wanda zaizo ya sake cewa zai rushe gidan nan mun gama magana dasu babu abinda zai faru" ya fad'a yana mik'ewa tsaye Baba ma ya mik'e suka fita tare suna cigaba da tattaunawa.
Da harara tabi bayan sa taja dogon tsaki tace, "Aikin banza aikin wofi." Umma tayi murmushi kawai bata ce komai ba ta tashi ta shiga ciki ta bar Rauda a wajan tana faman cika da batsewa.

         Baba ne ya dawo ya same ta har lokacin a wajan ya kalle ta yace, "ki dinga nutsuwa mana Rauda ko yaushe zuciyar ki a sama ki dinga sassautawa mana, nasan anyi miki ba daidai ba amma shi wannan meye laifin sa? Naga taimaka mana yayi ko?." Rauda tace, "Wallahi Baba gabad'ayan su na tsane su bana son su ko kad'an, mu da gidan mu ace sai alfarma akayi mana aka k'yale mu dan mu zauna? Wanne irin wulaƙanci ne wannan?."
"Ya dai isa komai ya wuce yanzu ai."
"To Baba" ta furta a sanyaye.

Ya kalle ta yace, "Maman ki ta sanar dani lokacin Iddar ki ya k'are ko?." Gabanta ya fad'i ta d'aga kai ba tare da ta d'ago ba yace, "To Allah ya kawo miki miji na gari da gaggawa." Bata amsa ba ta canja maganar tace, "Baba indai zaka amince min a wannan lokacin ina so zan koma makaranta na cika burina na zama y'ar jarida." Baba yace, "me zai hana Rauda? Sai ki koma ai ba wani abun bane ba, da zaman gidan ai gwara ki koma. K'anwar ki Rahma ma in tana so duk sai ku koma d'in."

Rauda taji dad'i sosai cikin mamakin Baba jin fad'a d'aya har ya amince kafin tayi magana yace, "Ba kuna da takardun sakandiri ba?." Tace, "muna dashi Baba, Jamb kawai zamuyi wannan shekarar in mun ci sai mu nemi makarantar." Baba yace, "Ba laifi, Allah ya taimaka" ya fad'a yana fita Rauda ta amsa da amin ta buga tsalle ta nufi d'akin Umman ta.

"Ummana!, Baba ya barni na cigaba da karatu" ta fad'a cikin farin ciki tana kallon ta. Umma ta tab'e baki tace, "Na taya ki murna."
"Umma wai me ya canja Baba ne lokaci guda haka? Ya daina yi min fad'a sosai, zancen makarantar nan fa ina fad'a masa baiyi musu ba ya amince."
"Jeki ki tambaye shi ya baki amsa. Ni ba karatu nake so kiyi ba Rauda aure nake so kiyi Allah ya sani."

Jikin Rauda sai yayi sanyi ta kalli Umman tace, "Umma meyasa bakya son karatun?." Umma tace, "Haka kawai, nafi so kiyi auren ki in yaso kyayi karatun a gidan mijin ki. Lokacin karatu a yanzu ya wuce tun a baya da ya amince kunyi da yanzu ba wannan zancen ake yi ba amma ya hana. Gobe in Allah ya kaimu gidan Baba Malam zan koma na karb'o maganin farin jinin da yake baki Allah ya fito miki da miji kiyi aure ko zaki wuce takaicin abinda aka yi miki. Zaman gida ba naki bane yanzu Rauda."

Rauda jikin ta sai ya mutu murnar da take yi ta koma ciki ta kalle ta tace, "Ummana ai aure lokaci ne, ki duba wancan lokacin da yazo bamu shirya ba gabad'ayan mu sai da akayi haka wannan ma ko bamu shirya ba sai anyi. In na fara karantun in Allah ya kawo mijin ba shikenan ba?." Umma ta rausayar da kai tace, "To Allah ya bada sa'a."
"Amin Umma, na gode."

Fitowa tayi daga d'akin ta shiga d'akin ta taji wayar ta tana ihu tana dubawa taga sabuwar number da bata sani ba ta d'auka da sallama daga can b'angaren tace, "Sis Rauda kin manta dani gabad'aya ko?." Rauda tayi y'ar dariya da ta gane muryar tace, "Ni na isa? Wallahi kina raina Allah ne bai bani ikon kiran naki ba Anty Ramla. Ya na ganki da number Nigeria kuma?."
"Ai mun shigo gari yanzu ma kiran ki nayi in kina gida mu shigo mu gaisa."
"Dan girman Allah da gaske kike zaku zo?."
"Wallahi da gaske nake, Dear yasan address d'in ki ai yanzu zaki ganmu yau in sha Allah zamu sauke alƙawarin da muka d'auka."

Cikin farin cikin Rauda tace, "Lallai kam, ko yaushe ace min za'a zo sai yau Allah yayi. Ina gida sai kunzo." Dariya Ramla tayi ta kashe wayar Rauda ta ajjiye wayar ta fita da sauri zuwa d'akin Umma tace, "Umma!." Ta kalle ta tace, "Ke lafiya kuwa?."
"Ina wanda na baki labarin sun taimaka min a Egypt lokacin da abin nan ya faru...? Ita tayi min waya gasu nan zasu zo mu gaisa."

Umma tayi murmushi tace, "Lallai manyan bak'i ne, to ki samu ki dafa musu wani abun kafin su k'araso." Rauda tace, "Wallahi ban san me zan dafa bane ba Umma." Umma tayi hanyar fita tare tana fad'in, "ki musu abu mai sauki na hausawa tunda daga k'asar waje suke zasu fi sha'awar abincin mu." Da Baba suka had'u yace, "Su wa za'a yiwa abincin hausawa?."

Umma tace, "Bak'i ne Rauda zatayi kuma a can k'asar da aka yi mata aiki suke zaune sai yanzu suka zo nan shine tace zata zo su gaisa." Baba ya kalli Rauda yace, "Ke a ina kika santa?." Rauda tayi shiru tana kallon Umma itama ita take kallo kafin tace, "Itace wacce nake fad'a maka mijin ta ya taimaki Rauda a lokacin akayi sakin nan a can misira, kaga ai manyan bak'i ne ayi musu abinci ko?."

Baba ya girgiza kai yace, "Inda abinda yafi abinci ma ai a basu, tsayuwar me kike yi to kije ki samar musu abinda zasu ci. In sun zo kuma ki shigo da mijin nata har nan sai kiyi min magana mu gaisa" ya fad'a yana ficewa Umma ta shiga wajan Inna ita kuma ta nufi kitchen.

Ba jimawa tayi musu lafiyayyen d'anwake kasancewar suna da kayan sa a hannu umma bata rasa yaji dakakke nan da nan ta gama ta zuba musu a flake sabo cikin wanda aka fara siya mata na tafiya gidan miji ta koma d'aki tayi wanka tana cikin saka kaya taji ana kiran ta alamun sun zo.

Da sauri ta gama shiryawa ta fito taga Ramla a zaune da murmushi a fuskar ta ta k'arasa kusa da ita ta rugume ta tace, "Oyoyo Anty Ramla sannu da zuwa."
Itama murmushin take yi tace, "Tunda kika gudu Nigeria sai aka daina jin ki sosai." Rauda tayi dariya tace, "Ina Dr yake?."
Chapter 64 · 0% Book details