Sashe 46
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
K'arfe d'aya da arba'in na ranar aka d'aura auren Jidda da Asad, d'aurin auren da ya tara manyan mutane sarakuna da y'ay'an su da jikokin su. Duk wani mai ji da kud'i da mulki yazo d'aurin auren domin kowa yasan mahaifin Asad haka mahaifin amaryar shima ba k'aramin mutum bane ba, bayan a gama aka fara watsewa kamar yadda aka tsara na jiki suka fara wucewa gidan gwamnati inda a nan ne Asad zai karb'o sarautar sa.
Gabad'aya bashi da walwala balle kwanciyar hankali fuskar nan tasa kadaran kadahan baza ka fassara yanayin sa kai tsaye ba a haka aka je dubban jama'a da kowa na garin da wajan garin duniya ta shaida Asad matsayin sabon sarki Katagum. Masu hotuna da y'an jarida nan da nan aka fara yad'awa cikin lokaci kad'an magana ta fita daga Katagum ta zaga ko wanne sashi na duniya domin ko wacce gidan jarida sun saka haka gidan radio da masu d'aukar hoto.
Tunda aka tabbatar dashi matsayin sarki yaji kamar an d'ora masa wani abu a kansa mai nauyin gaske ga rawanin da yake kansa an canja masa ado zuwa na sarakai gabad'aya ya sake girma da kwarjini a cikin su ya sake yin kyau k'uruciyar sa ta b'uya mayyanta ta bayyana a a kan fuskar sa. Kid'a ake ana busa ana tambari aka nemi Asad yayi jawabi dogarai suka tawo a guje aka kare shi da zai mik'e ya tashi tsaye yana takawa a hankali da sandar girma a hannun sa ya k'arasa inda aka tanadar ya tsaya yayi shiru bai ce komai ba.
Harrrrr yake ganin mutanen duk da ya saba tsayawa gaban jama'a yayi magana amma ba kamar wannan da yake da wannan matsayin ba, ya lumshe idanun sa ya bud'e yayi gyaran murya a hankali kana yace, "A'uzubillahi minal shaidanir rajim bismillahir rahmanir Rahim. Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah ala kulli halin." Yayi shiru na wasu sacanni baka jin komai sai zallar kirarin da ake masa a wajan nan take yaji sabuwar izza na sake ratsa jijiyoyin jikin sa da gangar jikin sa, izzar da take banbance tsakanin d'an sarki da sarki ita yaji tana bin ko wanne b'angare na jikin sa ganin dukka mutanen da suke wajan a k'asan sa yake in aka cire gwamna.
"Mai girma gwamnan bauchi, kwamishinoni, sanatoci, da dukkan wanda suka samu damar zuwan wajan nan ina yiwa kowa barka da wannan lokaci, ina matuk'ar godiya da wannan damar dana samu aka zab"e ni a cikin dubban mutane aka d'ora min nauyin mutanen da suke cikin garin Katagum."
Ya sake yin shiru yana sauke numfashi tare da lumshe idanun sa yace, "In sha Allah a mulkin da zamu gabatar ko wanne mutum da yake zaune a cikin garin nan zaiyi alfahari da kasancewar sa a garin bazai yi dana sani ba, zai kuma yi farin ciki da zama a k'arkashin inuwar wannan mulkin." Dak'yar yake fizgo maganar ya sake yin shiru na wani lokaci kafin yace,
"In sha Allah zamuyi iya bakin k'okarin mu wajan ganin bamu cutar da kowa ba ba kuma mu saka kowa zubar da hawaye ba, zamu tafiyar da mulki fiye da wanda mahaifina ya tafiyar dashi badan mun fishi k'warewa ba sai dan zamanatar da namu da zamuyi cikin ilimin addini dana zamani. Ina yiwa kowa fatan alkhairi da fatan komawa gida lafiya, ina rok'on Allah ya k'arawa mahaifina lafiya ya tashi kafad'un sa nan kusa, ya bamu ikon farawa lafiya ya bamu ikon gamawa lafiya, ya bamu ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyan mu."
Addu'a yayi da larabci yana yi yana tsayawa sabida yanayin amma sai ka d'auka wani sabon style d'in ne hakan sai ya sake burge mutane musmaman yadda yake magana da ilimi a cikin ta.
Tambari aka buga sai da gaban kowa ya fad'i shamakin Katagum wanda ya kasance kowa yaushe yana gefe ya matso da sauri aka k'arasa aka gyara masa wajan zama ya zauna bayan an kare zaman nasa.
Jijiyoyin kansa ya rik'e domin harbawa suke sabida ciwo gabad'aya ya gaji ya galabaita jira yake kawai a tashi kowa ya watse ga sallar la'asar a kansa baiyi ba. Ba jimawa mai girma gwamna yayi jawabi kafin a watse a tafi raka mai martaba sarki Asad cikin gidan sa.
Gudu ake a kan titi ana jiniya mutane da yawa sun fito kallo ana d'aga masa hannu duk sai yake jin wani iri sabuwar k'asaita tana shiga ilahriin jikin sa, a haka aka isa gidan sarauta ya shiga ta k'ofar da mahaifin sa ya shiga yana tafiya ana kirari ana takawa a hankali cikin rashin kuzari.
Kida ake a gidan ana wasa da dawaki ana busa jama'a sun cika sosai na cikin gidan da wajan gidan. B'angaren Mamaa aka fara raka shi Mama tana zaune ita da y'an uwanta da k'awayen ta jakadiya ta shiga tana gud'a tana fad'in, "Ga farin wata nan ya tawo ya haske ilahirin duhun da ya mamaye gidan nan, ga bangon sikari nan ga fari ka zak'i, yadda yake fari fari haka zuciyar sa take fara tass, ga inuwar bishiya nan mai kud'i ya zauna talaka ya zauna. Allah yaja da zamanin Sarki jikin sarki, Allah ya k'arasawa sarki lafiya da nisan kwana. Shigo lafiya Angon Fulani Jidda....."
Duka mutanen Falon sun tashi banda Mama da take jin kanta a sama kamar zai fashe Asad ya shigo falon yana kallonta ta saki Murmushi ya k'arasa kusa da ita ya tsuguna a k'asa ta d'ora hannunta a kansa tace, "Allah ya yiwa rayuwa albarka, Yadda ka fara lafiya yau Allah yasa ka gama mulkin ka lafiya."
"Amin, Allah yaja da ranki ya baki tsahon kwanan ganin mulkin jinin ki" dogarai suka fad'a cikin d'aga murya. Mama tace, "ka gaji kaje ka huta." Kai ya girgiza domin bazai iya magana ba ya mik'e sai a lokacin ya kalli matan falon yaga dukkan su sun zube a k'asa kowa da farin ciki a kan fuskar sa.
Fita sukayi daga b'angaren ana ta kid'a ana busa ana ta tambari an saka masa lema a sama yana takawa mata suna gud'a da addu'a ana ta d'aukar sa hoto shi kuma yana dogara doguwar sanda mai cike da ado yana takawa a hankali yana kallon kowa d'aya bayan d'aya, aka raka shi har inda ya kasance b'angaren sa kafin kowa ya watse ya barshi shi kad'ai domin ya huta dan bazai iya zaman fada ba.
*The beginning.......*
FitattuBiyar
Nana haleema
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*049.*
"Rauda! Rauda!! Rauda!!." Daga can cikin d'aki tace, "Na'am! Baba gani nan." Jim kad'an ta fito daga d'akin hannun ta rik'e da d'ankwali ta fito inda Baba yake tsaye tace, "Baba gani" ta fad'a tana d'aura d'ankwalin. Ya nuna mata waje yace, "Zauna" ya fad'a yana zama shima ta zauna a kan carpet tana kallon sa yace, "Ashe yau aka nad'a mijin ki ya koma sarkin katagum amma shine koda wasa baki fad'a min ba?."
Gabanta ya fad'i har sai da ta dafe k'irjin ta ta d'ago ta kalle shi zatayi magana yace, "Wannan ai wulaƙanci ne kin san da abu baki sanar damu ba ai ko Allah ya sanya alkhairi maje muyi masa ko bamu muje wajan nad'in ayi damu." Yadda yake magana da fad'a ya saka ta had'd'iye abinda yazo harshen ta Umma da take zaune tace, "Ke kin san za'ayi sarautar ne?." Kai ta girgiza alamun a'a ta mayar da kanta k'asa bata ce komai ba.
"K'arya kike, ta yaya za'ayi masa sarauta matsayin ki na matar sa baki sani ba?, nafa san take-taken ki tun farkon auren nan ba so kike ba keda uwar ki da take goya miki baya shiyasa tunda kika dawo kike neman hanyar da zaki bi ki datse igiyar auren tunda kin samu abinda kike so k'afa ta warke ko?. Rauda tayi shiru bata ce komai ba Baba ya kuma fad'in, "Ta yaya zaki ce baki sani ba banda rainin hankali...? ko kuma kishin ya k'ara aure kike yi shine ya mayar dake haka?."
Lumshe idanun ta tayi ta bud'e su bata da abinda zata ce Baba ya fahimce ta gwara taja bakin ta tayi shiru a ganinta hakan yafi mata kwanciyar hankali, "ba magana nake miki ba? Kishi kike ko me?" Baba ya sake katse ta a fusace.
"Kayi hak'uri Baba, duka abinda ka fad'a ban san anyi ba, tunda muka dawo yace min a kawo ni gida zaizo nayi hak'uri daga nan ban kuma ganin sa ba."
"Ba kince kuna waya ba?."
"Eh muna waya Baba amma ba sosai ba" ta fad'a a sanyaye tana mayar da idanun ta k'asa. Baba yaja tsaki yace, "Zamu je muyi masa Allah ya sanya alkhairi matsayin sa na wanda yake auren y'ata." Rauda ta kalli Baba hawaye ya ciko idanun ta tace, "Baba basai kunje ba, da ace yana so kuje da zai sanar dakai." Umma da take gefe tace, "Abinda na gani kenan nima dai. Bai sanar damu ba kawai sai a d'auki k'afa a bishi ayi masa Allah ya sanya alkhairi?."
"Daman ai ke ba son auren kike ba tun farko dole kice haka da yake dukkan ku baku san ya kamata ba, ai ko babu komai tsakanin su ko dan aikin da akayi mata ta samu lafiya aje ayi masa balle matar sace. Dole naje nayi masa fatan alkhairi matsayin sa na sirikina." Rauda ta runtse ido jin kalaman Baba na k'arshe zuciyar ta nayi mata d'aci da mugun ciwo tana bugawa tunawa da abinda ya faru.
Umma taja bakin ta tayi shiru Rauda ta sunkuyar da kai tana wasa da hannun ta Baba yace, "In ma akwai wani abun a ranki kiyi gaggawar kawar dashi, auren ku babu rabuwa in sha Allah dan ya auri wata ba wani abun bane ba itace daman wacce babar sa take so ya aura tun farko, ki kwantar da hankalin ki ki kawar da ko maye a ranki tunda shi yana son ki zance ya k'are. Yauwa dan aure kam babu rabuwa da izinin Allah" yana fad'a ya tashi ya fita Rauda ta bishi da kallo ta sauke ajiyar zuciya.