Sashe 84
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suhaima tace, "tsohuwar matar mai martaba kike nufi?." Dummm gaban mutane hud'u ya buga a wajan, Asad, Aliyu, Mama, da kuma Hydar. Babu wanda gaban sa bai fad'i ba har ita Maman nan take annurin fuskar ta ya canja ta kalle ta tace, "Lallai sai kin danganta ta dashi kenan? Ko kin fini sanin tsohuwar matar sace?."
Suhaima tace, "Allah ya wuci zuciyar ki. Gani nayi ta taimake mu badan ita ba da Mamana ta kwana biyu da rasuwa ta sadaukar da tata rayuwar sabida ta Mamana."
Mama ta kalli Suhaima tace, "tashi ki bani waje tunda kin gama basu labarin abinda ya faru." Suhaima da take mamakin Maman nata tace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ki tashi lafiya" ta fad'a tana shiga d'akin ta ta barsu a zaune kowa yayi shiru a wajan.
Mama ta kawar da zancen tace, "Asad akwai abubuwan da nake so a aiwatar a cikin kwanakin nan." Asad yace, "Umarnin ki nake jira."
"Batun canja min wajan zama da muka fara mgana tun lokacin baya aka fara ginin wajan aka tsaya ina so a cigaba nan da sati zan koma can. Sannan duk ma'aikatan gidan nan a tabbatar an biya su albashin su domin bana tunanin ana biya a watannin baya, abu na gaba kuma matar ka Jidda."
Zirrrrr zirrrr zirrrr wayar Asad ta fara vibration ya kalli kiran yaga gwamna ne ya d'ago ya kalle ta sai tace, "Pick it."
"Godiya nake" ya fad'a yana d'aukar wayar ya saka a kunne. Ya jima yana amsa wayar kafin ya sauke ya kalle ta yace, "Taro na gaggawa na majalisar d'inkin duniya ya taso a England yanzu zan bar k'asar nan."
Mama tace, "Kai da wa zaku tafi?." Yace, "Nida shamaki da zagi sai Uncle."
"Jeka" ta fad'a jin babu Jidda a lissafinta yayi godiya yace, "Mama a dinga taya ni addu'a ina manta wasu abubuwan dana aikataa baya, koda an fad'a min bana sani nayi." Kai ta girgiza ya tashi ya fita yana fita zuciyar sa cike da jin dad'in maganar Jidda da ta katse aka rufa masa baya da kirari zuwa b'angaren sa.
Yana fita bai jima ba Aliyu ma ya fita Mama ta kalli Hydar tace, "halin Aliyu ya canja kamar bashi ba ka lura da hakan?." Hydar ya murmusa yace, "Na lura mama, abin farin ciki ne ganin hakan ko babu komai an daina mana gori da halayyar sa." Ta girgiza kai alamun gamsuwa kafin tace, "Allah yasa ba wani shirin yake yi mana ba." Hydar ya amsa da amin daga nan shima yy mata sallama ya fita.
*Bayan wasu kwanaki.*
Sati d'aya Asad yayi a London ya dawo aka cigaba da gudanar da mulki a satin ya ziyarci wata saukar alkur'ani ya yiwa daliban kyautar kud'i da kuma na alkur'ani mai girma. Yana k'ok'arin canjawa sosai amma bai canja d'in ba sai ya d'auko hanya sai ya karkace dan tuni jidda ta sake kamo lagon sa tsawa ko hantara ya daina ya koma mata kamar da sai abinda tace ake yi amma yana zuwa wajan Mama duk d ba sosai ba.
Aliyu kuwa kowa yasan ya canja bama kasafai yake zaman gidan ba wata rana bama a nan yake kwana ba yayi shiru har lokacin babu abinda ya aiwatar bincike yake a sirrance yana kama duk wani wanda yasan hana da hannu abinda aka masa, su Waziri tun suna jiran sakamakon ganin Asad ya haukace har sun hak'ura in suka yiwa Aliyu maganar sai yace yana sane kuma yana sane d'in akwai abinda yake shiryawa wanda yafi nasu.
Hajiya Mama an fara farfad'owa ginin da take so ayi mata an gama cikin sati d'aya har ta tare a cewar ta ba matsayin ta d'aya da ragowar matan gidan ba duk da girman kan ba kamar baya ba. Jikin mai martaba ana ta samun cigaba sosai duk da akwai wanda basa son farfad'owar sa.
*☆☆☆*
Bikin Rauda ya rage saura sati biyu an kawo lefe akwati goma sha hud'u ko wacce cike taf da kaya komai akwatin sa akayi masa y'an uwa da abokan arzuk'i sai murna kawai ake yi. An ta jeren gidan amarya a unguwar Tatari Ali quarters gida d'ankarere mai kyau da tsari kowa yaje sai ya dawo yana santin gidan.
Suna zaune ana ta shara yadda shagalin kamu zai gudana duka matan gidan ana zaune ana hira ita tana gefe tayi shiru domin mugun zazzaɓi take ji a jikinta, Yaya Fariha ta kalle ta tace, "Wai amarya lafiya kike ana hira kin yi shiru?."
Rauda tace, "wallahi zazzaɓi nake ji sosai ga ciwon kai." Yaya Shamsiyya tace, "Muda muke da Fariha kun manta ta kusa magana karatun ta? Duba mana ita ki bata magani bana son wannan zaman nata shiru wallahi."
Yaya fariha ta k'arasa kusa da Rauda tace, "Kodai malaria ko typhoid shine yake damun ta, abinda zai faru ina jin ina da sabon sring a aljihun jakata dana siya a makaranta muka gwada wani abu bara na d'auki jinin ki aje a gwada dan mu san meye" ta fad'a tana d'aukowa daga Jakarta.
Jinin Raudan aka d'iba ta yago takarda daga Jakarta tace, "Maza Rahma jeki nan baya ayi wannan test d'in" ta fad'a tana rubutu ta bawa Rahma da kud'i wacce take zaune. Rahma ta karb'a ta mik'e ta fita tace, "kifa yi sauri kar jinin ya daskare."
Rahma na fita Baba ya shigo yace, "Ah lallai yau an zo za'a cinye min abincin gida, ko wacce ta kwaso yara an tawo zaman hira kawai." Da yake sun saba da halin mahaifin nasu dukkan su dariya sukayi kawai aka gaisa ganin su tare shima sai ya zauna ana hirar dashi.
"Ke kuma lafiya?" Ya fad'a yana kallon Rauda. Yaya fariha tace, "Zazzaɓin nan dai, na bayar dai yanzu ayi mata test na malaria da typhoid yadda zamu gane wanne ne yafi yawa sai ayi maganin sa kai tsaye."
Baba yace, "Yau dai naga amfanin karatun ki." Ummulkhairi da take gefe tace, "Baba nima in mukayi waec wannan shekarar shi nake so nayi."
"Sai kiyi ai" ya bata amsa yana tab'e bakin sa kafin yace, "Itama mijin tane yake biya ki jira kiyi aure kema mijin naki ya biya miki."
Yaya Shamsiyya tace, "Ai ko mijin ta bai biya ba Baba mu zamu biya mata, Allah yana rufa mana asiri dukkan mu yanzu Alhamdulillah." Baba yace, "Masalaha mai kyau." Umma da Inna dai kanzil basu ce ba suna dai zaune suna jin me ake yi.
Rahma ce ta shigo da sallama ta mik'awa Yaya Fariha takardar tace, "Ashe gwajin ba wahala, nan da nan akayi ashe ma uku yayi wai ya manta ya had'a da gwajin ciki." Yaya Fariha tayi dariya tace, "Yo ina ruwan mu da gwajin wani ciki ana zaune lafiya" ta fad'a tana warware takardar tana dubawa.
Dummmmm gabanta yayi mugun fad'uwa a gigice tace, "Ke anya jinin dana baki ya gwada kuwa? Kodai anyi had'e dana wani?." Rahma tace, "A'a Yaya, babu kowa ma fa a lab d'in ni kawai aka yiwa gwajin." Yayar mu tace, "Lafiya?."
Shiru tayi ta sake kallon takardar hannun ta yana rawa tace, "Ba lafiya ba, bara na sake d'aukar sample d'in naje da kaina a sake yi na gani." Baba yace, "Fad'a mana abinda kika gani har ya tayar miki da hankali haka." Tace, "bara dai a sake yi Baba wannan bai nuna daidai ba."
Yayar mu tace, "Dalla Malama ki fad'a. Wani ciwon ne Raudan!?" Ta fad'a cikin tsawa tana kallon ta. Umma da take gefe tace, "K'anjamau ce ko me Fariha?." Duk sai suka rud'a ta tace, "Gwajin da akayi mata ne ya tabbatar akwai ciki a jikin ta na sati biyu......!"
[17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*068.*
A tare dukkan su k'irjin sa ya bada sauti mai k'arfi da hakan ya saka wasu daga cikin su dafe k'irji tare da runtse ido firgici ya mamaye fuskar su da zuciyoyin su nan take suka ji abinda basu tab'a ji ba. "Kee Fariha wanne irin ciki ana zaune qalau? Gwajin jinin Rauda nefa ba naki kona Ummi ba" Yayar mu ta fad'a tana kallon ta itama da alaamun tashin hankalin a tare da ita.
Yaya fariha idanunta ya fito waje sabida tashin hankali ta sake kallon takardar ta kalle su tace, "Abinda sakamakon ya nuna kenan shiyasa nace anyi kuskure wajan yin gwajin, gwara a sake daukar sample d'in a sake yi sai a tabbatar." Baba da ya kasa cewa komai sai baki da ya buɗe zuciyar sa kamar ana doka ganga yace, "Ya dai kamata a sake yi amma har na cikin a sake gwadawa."
Umma da taji hawaye masu d'umi suna sakko mata daga idanunta ta girgiza kai tace, "Basai an sake yin gwajin nan ba abinda aka gani tabbas hakan ne, na fukanci hakan a yanayin ta daga jiya zuwa yau gudun kar zagi ya shiga zuciya ta sai na watsar da abin na barshi a rashin lafiyar da take fama da ita ne kawai. Amma sakamakon ku gaskiya ne Rauda nada ciki!."
"Wannan wacce irin maganar banza ce Binta? Da bakin ki kike cewa Rauda nada ciki?" Baba ya fad'a a fusace yana kallon ta kafin yaja tsaki yace, "Fariha sake d'aukar jinin muje tare a sake yin gwajin mu gani." Rauda da take zaune kamar an dasa bishiya sai idanu da take binsu dashi amma ko kad'an ta kasa fahimtar ma abinda suke cewa, tunda aka furta kalmar ciki shikenan sai kwakwalwarta ta tsaya cak ta daina aiki gabad'aya, tana ji dai suna ambatar ciki amma bata san me suke cewa ba.
Har aka huda fatar ta aka saka k'arfe cikin jijiyar ta aka d'auki jini bata sani ba wani wajan kawai take kallo zuciyar ta kamar ana kid'an kwarya sabida duka. Baba da Fariha suka fita falon yayi shiru baka jin motsin kowa sai sautin kukan Umma kawai da ya cika falon dan ita zuciyarta ta tabbatar mata da gwajin da akayi gaskiya ne ba k'arya ba.