← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 131

Sashe 67

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jidda fuskar ta har lokacin da tsoro tace, "Duk da haka Mum kisa fa?, kisa sai kace cinnaka ko kiyashi? Nidai a bar maganar kisa Mum."
"Mtsww sai kiyi ai, ke za'a taimakawa fa in aka barta da rai billahillazi sai kinzo kina kuka da idanun ki nan gaba domin ta wuce inda kike tunani, gwara mu yiwa tufkar hanci yadda zaki mulki gidan san ranki kiyi abinda kika ga dama in kuma ganin bakya son hakan fine Jidda daman ai ke za'a taimaka." Jidda ta rausayar da kai tace, "Yadda kika ce Mum, kawai ina jin tsoro ne." Mum tayi murmushi tace, "kar komai ya baki tsoro ni nasan yadda zanyi, ki bani nan da wasu kwanaki zanyi maganin ta."

Jidda ta juyar da kai zuciyar ta gabad'aya a cushe haka kawai take ji bata so a kashe Mama amma bazata nunawa Mum ba dan duk abinda take yi dan ita take yi in ta nuna mata bata so bazata ji dad'i ba amma bata son aje ga kisa. Ta jima suna hira a gida har Daddy ya dawo suka gaisa sannan drivern ta da jakadiyar ta suka kwashe ta aka koma gida.

*☆☆☆*

         Waziri ne a zaune malami a gaban sa su uku ne a zaune a falon shi da malamin sai Suhail malamin ya kalli Waziri yace, "Ranka ya dad'e in ba'a gaggawa ba komai zai iya canja salo ya zama dole ayi abinda ya kamata." Waziri ya girgiza kai ya sauke ajiyar zuciya yace, "Za'a yi cikin kwanakin nan kuwa in sha Allah." Sallama sukayi malamin ya tafi falon ya rage dashi sai Suhail ya kalli Suhail yace, "Meye shawarar ka?."

Suhail yace, "ta yadda za'a raba shi da mulkin shine aiki." Waziri ya sauke numfashi yace, "kawo shawara dai."  Ya gyara zama yace, "a ganina shi shugaba ne kuma wanda ake yiwa kallon mai addini da sanin ya kamata, me zai hana mu samu baiwa mace a had'a baki da ita a biya ta kud'ad'e masu yawa a kuma ja mata kunne matuk'ar nan gaba ta furta abinda ya faru sai an kashe ta."

Ya gyara zama yace, "Me za'ayi kenan?." Suhail yace, "Sharrin alfasha!." Waziri ya zubawa Suhail ido shima shi yake kallo kafin ya sauke kansa yace, "duk k'imar mutum alfasha tana zubar dashi, duk mulkin mutum alfasha tana sakawa a ganshi tamkar bawa, duk kud'in mutum alfasha tana sakawa a ganshi kamar talakan da bashi da cin yau bare na gobe. Duk yadda ka kai da ilimin ka da addinin ka indai alfasha ta shigo ciki ko kai kad'ai ne malamin da jama'a suke sauraron wa'azin su daga rana sun daina domin zasu ga abinda kake tsoratar dasu da kar su kusance shi kai kana kusantar sa. Sharrin Alfasha shine zai tarwatsa Asad ta k'arfi sai an sauke shi daga wannan karagar."

Waziri ya girgiza kai cike da gamsuwa da maganar sa zuciyar sa cike da tsantsar farin ciki yace, "Na jima banji maganar data kwantar min da hankali kamar wannan ba Suhail. Kana da hangen nesa da sanin ya kamata kayi tunani mai kyau Suhail shawarar ka tayi dari bisa dari babu kuskure a cikinta, tabbas wannan shine zai tarwatsa sarki da dangin sa." Suhail ya murmusa ya shafa kansa yace, "Godiya nake ranka ya dad'e."
"Tashi kaje zan neme ka anjima."
"A tashi lafiya" ya fad'a yana mik'ewa ya fita ya bar mahaifin nasa a zaune.

Yana fita wayar sa tayi k'ara kamar jira ake ya fita ya duba ganin number da yake jira ya saka shi ya d'auka yace, "Kamar kin san jiran kiran ki nake yi master." Tace, "akwai update ne?."
"Sosai ma kuwa."
"Ina jin ka."
"Maganar raba Mai martaba da kujerar sa ce an samo mafitar da zai barta koda baya so."
"Meye ita?."

Waziri yace, "Sharrin alfasha za'ayi masa, abinda nake nufi a kama shi da mace a d'aki macen ma baiwa." Tayi k'aramar dariya tace, "Sarkin za'a kama da baiwa a d'aki? Kana mantawa da sarki ne fa bafa hakimi ba?." Ta sake yin dariya kafin tace, "sam wannan shawarar batayi ba, babu ta yadda za'ayi sarki guda ace an kama shi da wata yarinya kuma baiwa a d'aki d'aya hankali ma bazai d'auki a wannan ba."

Waziri yace, "Zaiyu mana, ba Zuciya ce fa."
"To ta yaya ta shiga? Meya kaita d'akin sa? Me zata kai masa har d'aki?, daga kanta ya fara?, meyasa a baya ba'a tab'a jin makanancin labarin ba?. Bafa Aliyu bane Asad ne ya kamata ka gane."

Waziri yayi shiru jin yayi shiru ya saka tace, "in zaki yanke hukunci kuyi wanda hankalin mutane bazai kai shiri bane kuyi abu kamar gaske, inda ace Aliyu ne dan munyi masa sharrin nan ba wani abu bane mai wahala kowa kuma zai amince da zai iya aikatawa tunda daman an san dabi'ar sace, amma Asad fa?. Kai koma Aliyun ne sarki ne fa taya zai nemi baiwar sa? In ma neman matan zaiyi ba'a gidan ba sai dai wani wajan daban."

Waziri cikin gamsuwa yace, "Tabbas maganar ki gaskiya ce." Tayi murmushi tace, "tunda lokacin da muke jira yazo zan san abinda za'ayi amma wannan shawarar a ajjiye ta a gefe d'aya ba za'ayi aiki da ita ba kwata-kwata."
"Me za'ayi?."
"Zan sanar dakai in na gama shirya komai."
"Batun yin cikin matar sa fa? Bana so ya ajjiye d'a a duniya domin zai iya zamar mana barazana nan gaba."
"Shida haihuwa har abada, na gama da wannan aikin tun ba yau ba."

Waziri ya sauke numfashi yace, "Zan so ki bayyana min fuskar ki ko sunan ki ni kaina ban sanki ba har gobe." Dariya tayi tace, "nan kusa" tana fad'a ta yanke kiran yabi wayar da kallo zuciyar sa na hasaso masa wacece master planer......?

*☆☆☆*

         Washe gari

        Da wuri Rauda ta shirya tana jiran su Ramla dan ranar Baba malam ya basu suje su ganshi, k'arfe goma na safe suka bayyana a k'ofar gidan har gida Ramla ta shiga suka fito tare suka shiga mota suka tafi. A mota Rauda tace, "Ina kwana Dr."
"Lafiya lau Rauda, mun fito dake da sassafe." Murmushi tayi kawai bata ce komai tana nuna musu hanya har suka je k'ofar gidan.

K'arewa k'ofar gidan kallo suke yi ganin sa a cike da manyan motoci ga babura Dr ya kalli Rauda yace, "kalli jama'a kamar ana sadaka?." Ramla tace, "abin mamaki ba." Rauda tayi murmushi tace, "Dan ma yau asabar da jiya ne wallahi wajan nan babu waje." Kai ya girgiza suka fito Rauda tace, "shiga ciki zamuyi ai." Cikin gidan suka shiga suna wuce mata a zaune da maza wasu da hijjabi wasu kuma da mayafi wasu kuma da niqab.

       A cikin wani d'aki Rauda suka sauka suka zauna sannan ta tashi ta shiga cikin gidan suka gaisa da mutanen ciki ta dawo ta zauna tace musu, "Yanzu zai shigo in sha Allah." Suna zaune kowa yana danna wayar sa babu mai magana a cikin su kusan mintina arba'in a haka kafin suji gyaran murya a bakin k'ofa.

Da sauri suka mik'e dukkan su yana murmushi ya shigo yana fad'in, "Ku zauna mana, Babata zauna." Zama yayi akan wata kujera a d'akin suma suka zauna kafin su gaisa dukkan su ya amsa da murmushi ya kalli Rauda yace, "Babata kinyi min yaji ba'a ganin ki ko kad'an sai kinga dama." Murmushi tayi tace, "Muna gaisawa a waya ai Baba."
"Ni ganin Babata nake so nayi ai ba waya ba, koda yake baki jima da fita daga idda ba ai." Murmushi kawai tayi tace, "Baba ga bak'in da Umma ta fad'a maka zasu zo munzo tare."

Yace, "To ma sha Allah." Rauda ta mik'e tace, "bara na shiga ciki" ta fad'a tana shiga cikin gidan ta barsu dan su sake su fad'a masa matsalar su. Ta jima a ciki suna hira da y'an matan gidan har aka turo kiran ta sannan ta dawo ta shiga da sallama ya kalle ta yace, "Rauda." Ta zauna tare da fad'in, "Na'am Baba."
"Gobe da yamma ko da daddare kizo ki karb'ar musu magani bani dashi a yanzu zuwa da asuba zan samo shi in sha Allah."
"To Baba Allah ya kaimu."
"Amin ya Allah. Kema akwai naki sai ki tafi dashi a goben gabad'aya."
"To Baba."

Baba ya kalle su yace, "Khalifa in sha Allah gobe za'a karb'ar muku maganin da izinin Allah kuma za'a dace, sannan kuma ku bi shawarwarin da na baku in sha Allah za'a dace, a kuma dage da rok'on Allah." A tare suka ce, "Mun gode Allah ya k'ara girma." Baba malam yace, "babu komai, zaku iya tafiya yanzu ina da bak'i."

Dr ya d'auko kud'i masu yawa ya ajjiye masa Baba Malam ya girgiza kai yace, "Bana buk'atar kud'in sadaka daga wajan ku, mahaifiyar Rauda ta sanar dani taimakon da kuka yiwa mata kun cancanci fiye da haka daga wajan iyalan mu. Mu rama alkhairi da alkhairi" ya fad'a yana mik'ewa cikin murmushi fuskar sa sak ta Umma sukayi godiya sosai ya fita.

Cikin gidan Rauda ta shiga tayi musu sallama suka fito suka fita, a k'ofar gidan suka ga dogarai maza guda biyu a bakin wata mota kana ganin motar kasan daga gidan sarauta ta fito yanayin number motar ya nuna hakan suka wuce abin su ba tare da sun kalli wanda yake ciki ba.

A mota suna cikin tafiya Rauda na baya a zaune Ramla tace, "Gaskiya naji dad'i wallahi Rauda, badan ke ba wannan layin ai bamu san lokacin da zamu bar nan ba wataƙila ma layin bazai zo kan mu ba. Allah ya bar zumunci wallahi dan ji nake a jikina kamar har mun samu waraka." Dr yace, "Nima haka, ban tab'a jin wani yak'ini na samun magani kamar wannan ba, kuma ta inda ya burge ni da alkur'ani da hadisi yake amfani baya duba baya tsafi ko wani abun. Gaskiya Rauda kun dace samun babban mutum a dangi kamar sa ma rahama ne."

Murmushi tayi kafin taji yace, "naji yana ce miki Babata sunan maman sane dake?." Rauda tayi dariya tace, "A'a kawai yana fad'a min ne sabida ina kama sosai da babar su Umman shiyasa. Umma tace kamar itace ta haife ni shiyasa yake ce min haka."
Chapter 67 · 0% Book details