Sashe 121
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rauda ta kalli gidan sai ta tuna tazo gidan a daren da Yaya Ummi ta rakota da daddare ta juyo ta kalle shi tayi murmushi tace, "Na gode." Murmushi yayi yace, "nine da godiya da aka amince min. In babu damuwa zan iya cewa wani abun matsayin abokin Mai martaba?." Rauda ta d'aga kai alamun eh yace, "Tsakani da Allah ranki ya dad'e yana tare da damuwa sosai yanzu maganar da nake yi akwai Dr Yasir ya saka masa drip a ciki sabida jikin sa babu k'arfi, da aka auna jinin sa bp d'in sa ya hau fiye da tunani shiyasa aka sama masa ruwa dan a samu ya sauka da wuri. Yana da damuwa ranki ya dad'e zuciyar sa a cushe take Hydar ne abokin shawarar sa yanzu babu shi ke kad'ai kika rage masa, dan Allah ki taimaki rayuwar sa kar ciwo ya kashe shi da k'arancin shekarun sa."
Yadda yayi maganar a nutse sai ta sauke nunfashi cikin tausayin sa mai yawa da dana sanin abinda ta aikata ta girgiza kai tace, "in sha Allah. Na gode." Ya fito ya buɗe mata motar yace, "in kika wuce falon farko akwai na biyu dana uku, a cikin na ukun akwai underground nan zaki bi yana ciki." Kai ta d'aga ta nufi cikin kai tsaye zuciyar ta na bugawa.
Babu kowa a falon farkon sai haske da hotunan sa da suke cikin glass gabad'aya falon adon farin glass akayi komai fari hatta kujera da carpet gasu karr kamar ba'a takawa. Ciki ta wuce kamar yadda yace ta sake ganin wani falon mai step d'in da zaka hau sama ta sake wucewa nan ta sake zuwa wani falon da yake da underground d'in. K'asa ta dinga yi tana bin steps d'in har ta k'araso wata doguwar hanya mai kyau da haske da mudubi ta ko ina da adon fulayoyi kafin ta iso falon.
A zaune ta hango shi ruwan da yake shiga jikin sa ya k'are an cire Dr Yasir yana zaune yana had'a masa magani, "Assalamu alaikum." Ta fad'a cikin muryar mai dad'i Dr Yasir ya amsa yana juyawa yana kallon ta. Ganin ta ya saka Dr Yasir yace, "Barka da zuwa ranki ya dad'e." Kai ta d'aga bata ce komai ba shi kuma ya cigaba da had'a masa maganin.
Maganin ya bashi yasha tana tsaye har lokacin kafin Dr ya tashi ya fita daga falon bayan yayi mata sallama cikin girmamawa. Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta k'araso inda yake jikin ta a sanyaye tana kallon sa ganin ya rame a fuska da wuyan sa da k'aramar riga ce a cikin sa dogon wando.
Kamar bai san da mutum a wajan ba ta zauna a gefen sa tana kallon sa shi kuma ba ita yake kallo ba wani wajan daban yake kallo fuskar sa a d'aure. "Sultan!." Ta furta a hankali tana kallon sa sai da ya rufe ido ya bud'e sunan da yadda ta fad'e shi sun shige shi sosai amma baya tunanin zai iya kallon ta.
"Ya jikin ka?" Ta sake fad'a tana kallon sa amma bai ma kalle ta ba balle ya amsa mata. Ganin hakan sai ta zago ta dawo kusa dashi ta jawo stool d'in tsakiyar d'akin ta dawo dashi daidai da fuskar sa tace, "I'm sorry." Sai a sannan ya d'ago ido ya kalle ta suka had'a ido ta sauke nata k'asa sai ya sake d'auke kansa baice komai ba.
Hannun sa ta rike duk da kirjin ta yana bugawa tana kallon hannun da babu agogo a jiki zanen bak'in shaidar sa ta fito ta kalle shi tace, "Kayi haƙuri Sultan." Hannun sa ya zame daga cikin nasa ya sake kawar da kansa gefe tare da dafe kanta baice komai ba. Sake komawa inda fuskar sa take tayi zatayi magana yace, "Please" ya furta a hankali yana dafe da kansa.
Shiru tayi ganin ya dafe kai ta d'auke kai daga kallon sa tayi shiru tana wasa da hannun ta, a fakaice ya kalle ta gabad'aya khamshin turaren ta ya dame shi ya d'auke kai tare da sauke numfashi yana sake jin zafi a ransa jin khamshi na tashi a jikinta kuma a haka ta fito daga gida.
Mik'ewa yayi sai kuma ya d'an tsaya jin kansa na ciwo kafin ya fara tafiya zuciya cikin d'akin da yake cikin falon, da kallo ta bishi sai ta d'auke kai sai take jin ina ma bata kawo kanta an wulaƙanta ba da tayi zaman ta ya neme ta da kansa duk da ba haka ba. Kiran sallah taji na azahar a wayar ta ta kalla taga sha biyu da y'an mintina ta ajjiye wayar tana sauke numfashi.
Ta jima a nan a zaune har ta tashi taga wata k'ofa a falon ta buɗe taga band'aki ne ta shiga tayi alwala ta fito ta sake d'aukar wayar ta ta nemi alqibla a falon ta nuna mata ta tayar da sallah. Bayan ta idar ta kalli k'ofar da ya shiga bazata iya sake zuwa inda yake ba gwara ta tattara ta koma inda ta fito zaifi mata alkhairi akan ta zauna yana share ta.
_Amma kuma bashi da lafiya_ zuciyar ta ta fad'a mata sai ta tashi ta nufi d'akin a sanyaye. A kwance ta same shi alamun har yayi sallah ya kwanta ya kashe hasken d'akin gabad'aya sai sanyin a.c da da yake tashi a hankali, d'akin ba sanyi sosai kuma babu zafi. K'arasawa tayi kusa dashi ta kalli fuskar sa sai taga idon sa a kulle ta juya ta fita ta k'yale shi.
Yunwa take ji tana damun ta taga ragowar yogurt da ya rage ta d'auka tasha sai taji dad'i a cikin nata ta jingina da kujera tana kallon robar drip d'in da aka cire a haka itama bacci ya d'auke ta.
Yunwa ce ta sake tashin ta daga bacci ta tashi tana juya wuyanta ta sabida ya sage ta kalli tangamemen agogon bangon mai d'auke da hoton sa taga k'arfe uku daidai ta kalli falon tana neman abinda zata ci, tashi tayi duk k'ofar da ta gani sai da ta buɗe amma babu kitchen gashi tsoron komawa baya take dan girman gidan tsoro yake bata ga zurfi tsaf za'a yi mata wani abun ma bai ji ba.
Yunwa ta dame ta sosai ji take kamar ana nad e mata hancin ciki ta zauna duk ta jigata sabida yunwa tana runtse idanunta, hannu ta saka ta kulle fuskarta kawai ta fara kuka, kukan yunwa da kukan k'in kulata da yayi. Duk abinda take yi yana tsaye a bakin taga yana kallon ta ya rigata tashi ya fito yaga tana bacci ya koma, fitowa yayi bata ji ba ya wuceta bai jima ba ya dawo da pack na abinci yazo kusa da ita ya mik'a mata tare da cewa, "Me kukan yunwa."
D'ago fuska tayi ta kalle shi ta kalli hannun sa sai ta turo baki ta goge idanunta ta karb'a ta buɗe ta fara ci ko wanke bakin ta ma batayi ba sabida yunwa. Sai da ta cinye tass har lokacin yana tsaye a kanta ya hard'e hannun sa a k'irji yana kallon ta, kwarewa tayi ta fara tari ya bata ruwa ta karb'a tasha ta ajjiye pack d'in tana sauke ajiyar zuciya dan sai lokacin taji ta dawo daidai.
Kallon kanta tayi sai a sannan taga babu roiling din mayafin da tayi sai hular kanta kawai tasan shine ya zare da tana bacci hakan ya saka bata damu ba ta sunkuyar da kai k'asa bai magana ba ya juya ya tafi. Da kallo ta bishi ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi ganin ya d'an samu lafiya ba kamar d'azu ba ya kuma ya d'an sarki rai fuskar sa bata kai d'azu d'aurewa ba.
La'asar akayi ta sake tashi tayi alwala tayi sallah a falon tana zaune akan carpet d'in ya fito yayi wanka ya saka k'aramar riga fara da farin wando wanda ya wuce guiwa kad'an rigar mai k'aramin hannu gabad'aya hannun sa a waje yake. Mik'ewa tayi tana kallon sa shima ita yake kallo da idanun sa har sai da ta sauke nata k'asa ganin kallon yak'i k'arewa sai kuma taga ya juya ya nufi barin falon.
Da hanzari ta bi bayan sa dan bazata iya zama ba taga ya koma wancan falon ya shiga wani d'aki ta zauna tana jiran sa. Ya jima sosai har ta gaji da zama ta tashi ta lek'a taga karatu yake yi ya tara uban littafai a gaban sa sai ta sake komawa ta kulle masa k'ofa.
Sai da akayi magariba ya fito yana kallon ta ta tashi tana rik'e da bayanta ya sake komawa ta sake bin bayan sa. Tare sukayi sallah bayan an idar tana nan zaune a kan sallar ta sake jin yunwa tana damunta, kamar ya fahimta ya sake kawo mata abincin da Suhail ya tulo masa taci sosai ta sauke numfashi.
Babu wanda yake magana a cikin su har akayi i'sha suka sake yin sallah bayan an idar ne tayi shafa'i da wutur shima haka kafin ta tashi ta fara nad'a mayafin ta ta gama tsaf ta kalle shi tace, "Kayi haƙuri nazo inda baka gayyace ni ba, na jure wulaƙancin naka na wani lokaci amma na kasa jurewa zan koma inda na fito" ta fad'a tana kallon sa tare da soka filled d'in jikin mayafin ta.
Tashi yayi yazo gab da ita yana kallon ta sai ta tsaya daga abinda take yi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya sauke numfashi amma bai daina kallon ta ba, a hankali ta kalle shi murya na rawa a tausahe tace, "Na baka haƙuri kak'i ka hak'ura" ta fad'a hawaye na sakko mata ta goge.