Sashe 60
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba ta Jidda take ba dalilin da ya saka batayi mata magana ba tace, "Ina tambayar ka kayi min shiru ka bani amsa." Asad yace, "Mamaaaa...." shiru yayi ya kasa k'arasawa Jidda da take zaune ta fashe da kukan munafurci.
Gabad'aya hankalin sa ya koma kanta ya juyo yana kallon ta tace, "Kamar ni Hydar zai ce zai daka, ina matsayin matar ka dan yana k'anin ka sai yace zai dake ni..?. Kenan nan gaba ma bawan gidan nan sai ya d'aga hannu ya dake ni tunda ka nuna musu bani da mahimmaci a wajan ka." Kallon Hydar yayi suka had'a ido ya kalle ta ya sake kallon sa da ido yake masa magana ya fahimta amma sai ya basar kamar bai gani ba domin haushin Asad d'in yake ji ba kad'an ba.
"Ni zaka kalla Asad ba Hydar ba." Kallon Maman yayi kamar yadda tace zaiyi magana Jidda ta sake katse shi tace, "shikenan ni an wulaƙanta ni kenan a banza? Ina matsayin matar sarki uwar gidan sa uwar y'ay'an sa wani yayi yunk'urin dukana a zuba masa ido daidai kenan...?." Mama ta fusata tace, "Kee Jidda! Bana son shirmen banza kin san halina, ko Sadiya bata magana in ina magana balle ke."
Jidda tace, "Sai ita tak'i yi amma ni zanyi. My king ko a d'auki mataki akan Hydar ko kuma na bar gidan nan." Asad ya runtse ido ya kalli Hydar yayi shiru baiyi magana ba Mama tace, "Asad wai me yake damun ka? Kayi magana me ta baka kaci ka koma haka..?."
"Abinda kika bawa mai martaba yaci ya koma yadda yake shi na bashi yaci, yadda kika mayar dashi haka nima zan mayar dashi wannan ba damuwar ki bace ba. ku tashi ku fitar min daga b'angaren miji lokaci shiga turaka......" babu zato taji saukar mari a kuncin ta.
Suhaima ce a gabanta ta manta ma a falon wa take da kuma su waye a gabanta jikin tane kawai yake rawa jin yadda take fad'awa Mama maganar da tunda tazo duniya bata tab'a ji an fad'a mata irin ta ba.
Mik'ewa tsaye Asad yayi idanun sa a waje yana kallon Suhaima da take kallon Jidda sai kuma ta kalle shi ta duk'a tace, "ka gafarce ni bazan iya zuba ido ana zagin Mama ba dole na d'auki mataki, nasan kuma mai martaba yana girmama mahaifiyar sa dan na d'auki hukunci akan wacce taci zarafin ta bazai bani laifi ba."
Jidda da take dafe da kunci cikin mamaki dan bata d'auka hakan zai faru ba tace, "Ni kika mara Suhaima? Ina matsayin matar yayan ki, matar sarki, matar shugaban ki sama nake da kowa a gidan nan zaki d'auki hannu ki mare ni. My king kana gani kk?" Ta fad'a tana kallon Asad da yake kallon Suhaima baice komai ba.
"K'asa kike da Mama shiyasa na hukunta ki."
"Ko ita Maman sama nake da ita domin ita ta tako tazo inda nake ba nice nazo inda take ba, babu wanda ya fini a gidan nan koda kuwa itace!."
Shiru falon yayi ana jiran aga hukuncin da zai yanke dukkan su basuyi tsammani ba suka ga ya tsinkawa Suhaima mari abinda bai tab'a faruwa ba kenan tsahon rayuwar su. Mik'ewa Mama da Hydar sukayi ba shiri Mama ta kallli Hydar shima ya kalle ta suka kalli Suhaima da hawaye yake sakkowa daga idanun ta cikin bak'in ciki da k'unar rai. Hydar ya k'arasa inda yake yace, "Asad kana cikin halin ka? Mama ta zaga fa dan tayi mata hukunci sai ka dake ta?, kenan ka fifita ta akan Mama kenan?" Ya fad'a da alama ya manta matsayin da Asad yake dashi kallon Asad d'in da yake masa.
Asad ya kalle shi yace, "Matata take, kuma sama take da kowa a gidan nan, sau d'aya tak baka tab'a ganin k'annen Abba sun daki Mama ba dan bazan lamunci gani anyi a gaban idanuna na k'yale ba." Hydar da ya zuba masa ido shima shi yake kallo cikin mamaki da tsoro Hydar yake girgiza kai Jidda tace, "wannan hukuncin yayi mata kad'an ina so ka saka ayi hukunci kamar yadda za'a yiwa baiwa in ta aikata kuskure da tayi."
Mama ta matso kusa dashi cikin sanyin jiki ta juyo dashi da hannunta tana kallon sa shima kirr yana kallon idanun ta tace, "Asad anya kaine?" Ta fad'a tana d'ago kansa tana sake kallon idon sa ta tabbatar shine da gaske ba wani ba tace, "Meya same ka Asad? Wannan canjin daga ina yake haka?" Ta fad'a a tausashe tana kallon sa.
"Mama a gaban ki ta mari Jidda baki hanata ba bayan hakan ba daidai bane" sake kallon sa take jin abinda yace tana girgiza kai.
"Nifa my king kawai su sauka su bar wajan nan bana son ganin su, sannan ka saka a yiwa Suhaima hukunci indai kana sona kana qaunar zama dani!" Jidda ta fad'a tana kuka tana kallon sa suka had'a ido ya kalli Mama ya nuna musu hanya yace, "Mama ko zaku iya sauka?."
"What!" Hydar ya furta yana kallon sa da mamaki jin abinda yacewa Mama idanun sa k'asa kuma kamar koda yaushe. Kafin su gama mamaki suka ji ya kalli Suhaima yace, "Ki tabbatar da sai an miki bulala goma nan gaba in kika sake....." Sai ya dafe kansa kana ya cigaba yace, "zan miki hukuncin da bakiyi tunani ba."
Mama baki bud'e take kallon sa idanun ta sunyi ja sabida tashin hankali da tsoro hadi da al'ajabi da bugawar zuciya tace, "Asad kasan da wanda kake magana kuwa?." Ya runtse idanun sa ya dafe kai yace, "Na sani, na sani Mama! Don Allah ku barni kafin ku haukata ni bana son magana." Hydar ya sake kallon sa yace, "Asad kaine?." Cikin b'acin rai da fusata Asad yace, "Hydar i said out!" Ya fad'a da d'an k'arfi yana nuna musu hanya idanun sa a waje yana dafe kansa jin kamar zai fashe.
Ba shiri Hydar ya kama k'afadun Mama suka wuce Mama na kallon Asad shi kuma idanun sa a kulle hannun sa dafe da kansa suka fara sauka daga steps d'in, "Suhaima ki tabbatar sai kin karb'i hukuncin ki domin bazan yafe miki laifin da kika aikata ba." muryar Jidda ta katse su suka juyo dukkan su suka kalle ta suka cigaba da sauka ko wanne zuciyar sa cike da tashin hankali.
*Boom*💥😂😂
FitattuBiyar
Nana haleema
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*056.*
Mama bata san sun isa b'angaren ta ba sai gani tayi Hydar ya zaunar da ita a gefen gado ya kawo mata ruwa mai sanyi a kofi ya mik'a mata ba musu ta karb'a ta shanye ko zata daina jin zafin da yake tasowa daga zuciyar ta amma babu canji, cillar da kofin tayi ya tarwatse a wajan ta dafe kanta da hannunta jikin ta yana rawa sosai dan tunda take bata tab'a shiga tashin hankali makamancin wannan ba.
Zabura tayi ta kalli Suhaima tace, "Mik'o min wayata da sauri." Suhaima jikinta duk a mace har lokacin inda Asad ya mare ta zafi yake mata ta mik'a mata wayar hannun Mama na rawa ta kir number Mum bata d'auka ba ta sake kira ba'a d'auka ba ta cillar da wayar a kan gado tana ji kamar tayi hauka sabida tashin hankalin da take ciki.
Hydar yace, "Dan Allah Mama ki kwantar da hankalin ki kin sani ba halin Asad bane abinda ya aikata akwai abinda yake faruwa a cikin lamarin nan."
"Abinda yake faruwa ya wuce ta mallake shi?" Suhaima ta bashi amsa daga gefe idanun ta yana cikowa da hawaye.
Da hannu Mama tayi musu alama da su bar mata d'akin Hydar ya fita Suhaima ta kwashe glass d'in da ya fashe sannan ta fita kowa zuciyar sa babu dad'i akan abinda ya faru. Kamar mahaukaciya haka Mama ta koma so take ta samu mafita amma ta rasa inda zata samu ta d'auki waya ta kira babar yayar su amma wayar a kashe ta ajjiye wayar ta dafe kanta da duka hannayen ta.
"Ni Rabi'a Jidda zata yiwa wannan wulaƙancin? Inaaaa bata isa ba wallahi ba kuma zata isa ba har abada" ta fad'a tana sake naushin iska cikin tashin hankalin da bata san iyakar adadin sa ba.
Bata san ina adadin lokacin da ta d'auka tana a haka ba ita dai tasan bata jin bacci ko kad'an ga abinda ya kuma tsaya mata a rai rashin kiran ta da Mum bata yi hakan ya sake tauar mata da hankali matuk'a. Bacci b'arawo ne ya sace Mama shima tana yi tana mafarkai tana farkawa.
Washe gari.
*☆☆*
"Rauda!" Umma ta fad'a tana tab'a ta tayi firgigit ta kalli Umma tare da sauke tagumin fuskar ta tace, "Na'am Umma, yaushe kika shigo?." Umma tace, "ta ya zaki san na shigo bayan kin shiga duniyar tunani?. Anya Rauda kina son samawa zuciyar ki salama kuwa? Kin mayar da tunani abokin ki koda yaushe kuna tare dan k'addara ta fad'o rayuwar ki?, meyasa baza kiyi tawakkali bane?."
Ta sunkuyar da kai Umma ta kuma cewa, "da k'aracin shekarun ki zaki jawowa kan ki ciwo sabida d'a namiji, son sa kike har haka ne?." Ta kalli Umma ta sake sunkuyar da kai Umma ta kuma cewa, "kinyi gangancin bari soyayyar sa ta shiga zuciyar ki, kin sani ba tsarar ki bane daman akwai dalilin da ya saka shi auren ki ya samu abinda yake so kuma ya barki, kina saka damuwa a ranki shi yana can yana walwala yama manta da shafin ki a rayuwar sa ke kuma kina nan zaki kashe kanki da tunani. Ina rok'on Allah da na sanki da shi Rauda? Ina karatun alkur'anin da na san ki dashi duk ina suka tafi?."
Rauda ta share idanun ta tace, "Umma bawai ina sonsa bane kawai in na tuna ni a yanzu bazawara ce sai naji zuciyata ta karye."
"Rashin karb'ar k'addarar kenan Rauda, dole ki damu amma bana tunanin zaki kaini damuwa domin nice mahaifiyar ki, addu'ar da nake yi babu dare babu rana shine ya sa kike ganin kamar ni abun bai dame ni ba amma na fiki damuwa. Ki cigaba da addu'a da rok'on Allah komai zai wuce ya zama tamkar ba'a yi ba, duk kin bi kin rame kin sake yin bak'i kamar ba ke ba."