← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 131

Sashe 129

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suhail na ganin sa ya mik'e tsaye har ya k'araso ya zauna Suhail yace, "Barka da fitowa ranka ya dad'e. " zama Asad yayi ya nuna masa kujera shima ya zauna kafin Suhail yace, "Ina fatan mai martaba ya samu lafiya." Asad yace, "Alhamdulillah." Suhail yace, "Sai aka tashi da rasuwa, Allah ya jikan wanda suka rasu." Nan ma ya amsa da amin kafin Suhail yace, "Ranka ya dad'e ga abincin, ga kuma list d'in matan da aka kawo wanda za'a aurar babu kayan d'aki. Ga kuma yawan takardun masu neman aikin da muka samu. Na bibiyi gidajen y'an matan da za'a aurar kuma na tabbatar da gaske auren zasuyi wasu abincin gidan ma yana gagarar su balle kayan d'aki."

"Su kuma samari masu neman aikin na tabbatar dukkan su babu aiki babu kuma Sana'a, a cikin su wasu babu mahaifi sai mahaifiya da y'an uwa nauyi ya hau kansu amma babu halin saukewa."

Karb'ar takadar Asad yayi yaga sunayen mata sama da hamshin ya girgiza kai yace, "A siyi kayan ko a basu kud'in?." Suhail yace, "A siyi kayan ranka ya dad'e." Asad ya girgiza kai ya mik'a masa yace, "Duk abinda ya kamata ayi, a had'a da kayan abinci ga kowa a d'ora kud'i."
"Kamar nawa kenan ranka ya dad'e? Abincin kuma kamar ya za'a saka?."

Asad yayi masa alama da yayi komai Suhail yace, "In sha Allah. Allah ya k'ara arzuk'i yasa a d'auki alkhairin da ake a duniya a gidan Aljanna.

A zuciya ya amsa da amin kafin Suhail yace, "Su kuma masu neman aikin zan rarraba wasu a company mai martaba wasu kuma za'a basu jari." Asad ya girgiza kai alamun gamsuwa kafin Suhail ya kuma cewa, "akwai bak'i da suka zo suna son ganin mai martaba na sanar dasu mai martaba yayi tafiya sun kafe akan zasu jira shi ya dawo." Yayi k'aramin tsaki yace, "bazan koma yanzu ba." Suhail yayi murmushi Asad ya kalle shi ya d'aga gira sama yace, "Fad'i abinda yake ranka."

Suhail ya shafa kai yana murmushi yace, "ni na iya ranka ya dad'e? Babu abinda yake raina sai alkhairi."  Asad yayi murmushi shima dan yadda yaji dad'in kwana d'ayan nan bazai koma ba sai sun kwana biyar cif. Asad yace, "Hydar bai shigo ba?." Suhail yace, "tun kwanaki ban sake ganin gilmawar sa a gidan ba."

Ya girgiza kai kawai baice komai ba dan ya tabbatar akwai abinda yake shiryawa shiyasa yayi shiru kamar babu shi. Wayar Suhail tayi k'ara bai d'auka ba Asad yace, "pick it, akwai abinda za'a baka ka kawo min." Jin hakan sai Suhail ya d'auka ai kuwa masu delivery ne ya fita yaje ya karb'o kayan a leda babba ya shigo dasu ya ajjiye.

Suhail yace, "Ranka ya dad'e in anyi min izini zan iya tafiya?." Asad ya d'aga masa kai ya mik'e sai Asad ya kalle shi yace, "Wai yaushe zakayi aure ne?." Suhail bai sam dariya ta sub'uce masa ba shima Asad d'in dariyar yayi Suhail yace, "Ranka ya dad'e an kusa in sha Allah." Maimakon yayi magana sai ya sake yin dariya yana cize bakin sa kafin yace, "yafi dai."

Suhail yana dariya suka had'a ido sai yaga Asad d'in ya d'aga masa gira ya sake yin dariya yace, "Zan zo wajan mai martaba a nema min mata dan naga giyar auren har saurin warkar da marasa lafiya su warke." Asad yayi dariya mai sauti amma baice komai ba.

Suhail yace, "Na barka lafiya, a gaida Fulani." Kai ya d'aga masa yana murmushi har lokacin Suhail yana jin farin ciki a ransa dan yaga shugaban nasa yana farin ciki shi kuma yana so yaga yana farin ciki domin yana da ciwo a zuciyar sa sosai farin ciki shine kawai maganin ciwon.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*094.*

        Yadda ta rame ta lalace kallo d'aya in kayi mata sai ka sake kai duba a gare ta sannan zaka tabbatar itace, tayi bak'i babu gayu a tare da ita balle ado da kwalliya. Fuskar ta ta jeme kamar an saka sirinji an kwashe albarkar fuskar ta ta koma y'ar k'arama kamar wacce ta shekara tana jinya. Tana zaune kusa da Mama tana kuka wanda ya zamar mata abokin hira tun bayan rasuwar Jidda har ta hawaye basa tsayawa a fuskar ta ko yaushe cikin zuba suke.

Itama Maman kuka take amma bai kai na Mum dukkan su sun kasa magana ga Eman a gefe itama ta rame sosai idanun ta yayi bala'in ja. Dak'yar Mum ta iya had'a kalmomin a kan harshen ta ta kalli Mama tace, "Na rasa ta wacce kalma zanyi amfani na nemi afuwar ki Rabi'a, na rasa wacce irin kalma zan furta wacce zata nuna miki nayi nadamar cin amanar ki."

Sai ta sake fashewa da sabon kuka zuciyar ta nayi mata kuna da ciwo tace, "Kin amince dani na ha'ince ki, babban burina naga bayan ki na mallake dukkan abubuwan da kike taqama dasu ke na raba ki dasu badan komai ba sai don son zuciyata da rashin k'aunar Allah da kuma zallar cin amana. Gashi yanzu dalilin mugun halina na kashe y'ata da kaina domin badan na d'ora ta akan turba mara kyau ba da duk hakan bai faru ba."

Mama ta girgiza kanta tace, "Sadiya laifina ne, da ban nuna miki burina akan sarautar ba da kema baki saka ranki a kai ba, dan nuna miki tsantsar son kai ba da kema baki yi wannan tunanin ba, da ban nuna miki in y'ar ki ta shigo gidan nan zan mayar da ita tamkar baiwa ba da kema baki tunanin d'aukar mataki ba, da ban nakasa Asad akan banzan burina ba da bata kai kanta ga Aliyu ba, da ban nuna nice nake so nayi iko da komai ba da baku mallake Aliyu ba. Duka wad'annan abubuwan nice naja nice na bada k'ofar da aka shigo aka aikata su, nice na bada dama nice na bada lasisin aikita dukkan abinda aka aikata shiyasa kike k'okarin kashe ni. Ni ya kamata na nemi yafiyar Jidda domin badan abinda na saka aka yiwa Asad ba da yanzu tana matsayin matar sa."

Mum ta girgiza kai tace, "Duk da haka ban zauna dake da zuciya d'aya ba, tabbas nasan yawan cewa a kashe wane da wance da kike cewa shine ya d'arsa min son kashe ki shiyasa na  saka aka kwance burkin motar Suhaima ta yadda zaku mutu gabad'aya amma Allah ya tseratar dake. Na sake bada guba aka saka miki a shayi shima Allah ya kubtar dake. Dan girman Allah kiyi hak'uri Fulani naga sakamakon aikata sharri tun kafin naje lahira, naga sakamakon mugun nufi tabbas naga amfanin karin maganar da hauwasa suke cewa in zaka hak'a Ramin mugunta ka yishi daidai kai."

Kuka suke dukka su biyun kafin Eman tace, "Mama kafin Yaya Jidda ta rasu ta bani sak'o na sanar dake ki yafe mata abubuwan data aikata miki, dan Allah ki yafe mata ko zata samu salama a cikin kabarin ta." Mama ta kalki Eman da take hawaye tace, "Na yafewa Jidda, nima naso tana raye ta yafe min dan ina da hannu a halin da ta shiga." Eman tace, "Mai martaba da matar sa tace na nema mata afuwar su Mama, a ina zan gansu?."

Mama ta share hawaye tace, "Asad da matar sa basa nan sunyi tafiya amma na tabbatar sun kusa dawowa. Allah ka yafe mana abubuwan da muka aikata dan tabbas duk cikin mu babu wanda baiga sakayyar Allah ba tun a duniya, shi waziri da ya tashi y'ay'a biyu ya rasa lokaci d'aya.....Allah ka yafe mana."

Mum tace, "Baki ce kin yafe min ba Fulani." Mama tace, "Na yafe miki, kema ki yafe ni."
"Na yafe miki nima. Allah ya saka da alkhairi" ta fad'a tana sake fashewa da kuka dukka su ukun kuka suke har Suhaima ta had'u da take gefen su.

*☆☆☆☆*

Cikin kwana hud'u da Asad da Rauda sakayi sun yishi cikin soyayya da nuna tsantsar kulawa ga junan su, ko gate basa fita ko yaushe suna cikin gida duk abinda suke so Suhail zai kawo musu ko yaushe suna tare da juna. Sunyi haske Asad har kib'a yayi dan ya samu mai kwantar masa da hankali bata barin sa cikin tunani da taga ya zauna shi kad'ai zata dawo kusa dashi tana bashi labari.

         Tsaf ya shirya cikin manyan kaya shadda kalar ash colour babbar rigar har k'asa take tasha aiki kai da ka kalla kasan aikin bana k'ananun sarakuna bane, aka kawo alkyabba kalar shaddar aka d'ora akai aka saka rawani kalar aikin shaddar takalmi kalar shaddar da aikin da yake jikin ta. Ba sai ance yayi kyau ba kana kallon Asad kasan yayi kyau sosai yana tsaye a jikin madubi yana sake gyara rawanin kansa.

Rauda da take tsaye a bayan sa tana kallon sa tace, "Sulatan." Ta madubin ya kalle ta tace, "In ka saka kayan nan sai ka koma tamkar babba, kuruciyar ka sai ta b'uya sai manyanta ya bayyana akan fuskar ka. Kana kyau da kayan nan kamar daman dan kai aka yi su."

Yayi murmushi ya juyo yana kallon ta ta tako zuwa inda yake tana kallon sa itama kamar zai mata magana sai ya fasa ya juya yana cigaba da abinda yake yi amma har lokacin fuskar sa a sake take. Sai daga baya sannan yace, "Muwaddaty banso tafiya yau ba, amma ya zanyi dole na amsa kiran Abba in ba haka ba sai mun kwana bakwai a nan" ya juyo yama kallon ta yace, "Na jima ban samu farin ciki kamar na kwanakin nan ba."

Hannunta ta zaga dashi a jikin sa ta rik'e bayan sa tace, "Ai a can d'in ma muna tare ko yaushe." Yayi k'aramin tsaki ya girgiza kai yace, "ba kamar nan ba, can hayaniya tayi yawa."
"Abba yayi kira dole mu amsa, amma nima bana so mu tafi zaman nan yafi na can dad'i. Kasan ni ban saba da wannan kirari ga abubuwan da ake min ba sai naji wani iri" ta Fad'a tana kwanciya a jikin sa ya rik'e ta shima idanun sa a lumshe.
Chapter 129 · 0% Book details