Sashe 130
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin yayi shiru ya saka tace, "Sultan baka ce komai akan makarantar tawa ba." Bai sake ta ba kuma bai magana ba yayi shiru suna tsaye a haka kamar baiji me tace ba jin yayi shiru itama sai tayi shiru.
"Kin tab'a ganin mace irin ki tana karatu a wata makaranta?." A sama taji maganar da bata d'auka ma zai sake maganar ba ta d'ago ta kalle shi tace, "To ai neman ilimi ne Sultan, kuma ina so shine burina a rayuwa."
"Badai a Nigeria ba sai dai in zaki iya a outside country" ya furta yana kallon ta sai yaga tayi murmushi tace, "Zan iya mana Sultan." Yayi murmushi baice komai ba ta bar jikin sa ya kalle ta yaga doguwar rigar jikinta bata nuna jiki ba kwata-kwata domin mai fad'i ce sosai ya rik'o hannun ta zuwa falo daga ita sai wayar ta kamar yadda tazo dan kayan da tazo dasu a jikin ta ma an ajjiye su a gidan.
Yasan amsar sa take jira shiyasa ya share dan abinda zaice ba dad'i zai mata ba ganin tana ta kallon sa ya saka yace, "In kina so zakiyi, amma dole a samu wacce zata zauna dani a nan in yaso duk sanda na samu lokaci sai naje can wajan ki. Ba'a barin shugaba a wani waje babu mata sai dai su zama biyu, akwai a nan akwai a can" ya furta yana kallon ta.
Take annurin fuskar ta ya d'auke ta ta bishi da kallo tace, "Kana nufin sai dai matan ka su zama biyu, ni ina can ina karatu ita tana tare dakai a nan? Sai lokacin da ka samu dama zaka je inda nake?." Ya d'aga girar sa alamun haka yake nufi sai yaga ta sake d'aure fuska gabad'aya walwalar da take fuskar ta ta d'auke tace, "Dole ne karatun?."
Mamaki yake jin tambayar da tayi masa sai ya tab'e baki ya wara hannayen sa alamun oho. Ranta gabad'aya ya b'aci ko kallon inda yake ta daina shima kuma bai kalle ta ba dan haka maganar take dole sai dai hakan ta faru inda tana son karatu.
A haka Suhail ya k'araso Asad ya bashi umarnin ya fara mayar da ita gida suka tafi har lokacin ranta a b'ace sai bayan ta tafi yayi dariya kawai. Ba jimawa ya dawo aka d'auki Asad suka wuce gida kai tsaye.
Rauda taga dawowar sa tasan b'angaren sa zai wuce ranta gabad'aya a b'ace yake a haka ta yi sallar azahar ta fito dan taje ta gaida Mama. A zaune ta tarar dasu kamar gidan mutuwa tayi sallama duk suka d'ago suna kallon ta sai ta sunkuyar da kanta ta k'arasa ta zauna tace, "Barka da Rana Mama." Mama ta fad'ad'a murmushi tana kallon ta tace, "Barkan ki. Kun dawo lafiya?."
"Alhamdulillah. Ya karfin jiki?."
"Jiki yayi sauk'i, ya naki jikin kema?." Rauda tace, "Alhamdulillah. Mun samu labarin anyi rasuwa Allah ya jikan wanda suka rasu ya gafarta musu."
Mama ta amsa da amin kafin Rauda taji muryar Mum tace, "Barka da shigowa Fulani." D'ago ido tayi ta kalli Mum tace, "Ya karin hak'uri?." Mum tace, "mun gode Allah." Rauda tace, "Allah ya gafarta mata, abinda ta haifa kuma ya saka ya kasance mai ceto."
"Amin" ta fad'a sai ta fashe da kuka tace, "Ki yafe min ranki ya dad'e dukkan abubuwan da aka yi miki nice nake kawo shawara ko nake bada goyan baya, dan Allah kiyi hak'uri da duk abinda ya faru wanda kika sani da wanda baki sani ba ina neman afuwar ki."
Rauda ta sauke numfashi tace, "Babu komai ya wuce, Allah ya yafe mana baki d'aya." Mum tace, "Amin ya Allah. Na gode ranki ya dad'e Allah ya saka da alkhairi." Rauda jikin ta duk yayi sanyi ta amsa da amin kafin Eman tace, "Yaya Jidda ta bani wasiya akan in nema mata yafiya a wajan ki, dan Allah ki yafe mata ranki ya dad'e ko zata samu sassauci a wajan wanda ya halicce ta." Rauda taji idanun ta ya ciko da kwalla tace, "Na yafe mata ina yi mata addu'a samun rahama a wajan Allah."
Mama tace, "Allah ya saka miki da alkhair. Kin haifu kin nuna mana dukkan mu baki d'auki sharrin da akayi miki a bakin komai ba domin dukkan mu da muke nufin ki da sharri gabad'aya kan mu ya dawo." Rauda tace, "Dan Allah Mama ta daina fad'ar wannan kalaman bana son sake maimaita su sun riga sun wuce."
Mama tace, "Haka ne. In da dama suna son iso wajan Asad." Rauda ta d'anyi jimm sai taji nauyi abinda Mama tace matsayinta na mahaifiyar sa ace itace zata nemawa babbar aminiyar mama iso a wajan Asad sai ta kasa magana jin abun wani iri lallai dan hakin daka raina shine yake tsone maka ido wata rana.
Suhaima ce tace, "Yanzu ya dawo sai dai ko su jira zuwa yamma ko dare." Mum tace, "Ko gobe ne zamu jira har sai mun ganshi in sha Allah." Ita dai Rauda tana nan zaune ta kasa magana sai daga baya ta mik'e tayi musu sallama ta fita duk suka bita da kallo zuciyar su na tariyo musu dukkan abinda suka aikata.
Rauda sai yamma tayi abinci kamar kullum aka tafi kaiwa mai martaba ta canja kaya zuwa atampa doguwar riga ta d'ora mayafi babba kamar ko yaushe dan ita ba son saka alkyabbar nan take ba zafi isar ta yake yi. A saman sa ta ajjiye tray d'in yana zaune ya canja kaya shima yana kad'a k'afar sa waya na kunne sa yana amsawa.
Zama tayi jin da larabci yake wayar bayan ya kammals tace, "Akwai Maman Jidda tana son ganin ka tana nan tun d'azu." Abinda tace kenan ya kalle ta yaga fuskar a d'aure sai ya tuna yadda suka rabu. Had'a ido sukayi yayi mata nuni da ta bashi abincin ta tashi ta zuba masa ta mik'a masa ya karb'a ya rik'e hannun ta ta zauna ya cika cokali ya kai bakin ta.
Bata da zab'i dole ta buɗe bakin ya bata sannan shima yaci baice mata komai ba, a haka suka ci abincin ya d'auko ruwa da kansa ya bata tasha shima yasha ya sake share ta kamar ma baiji me tace a d'azu ba.
"Fushin duk na meye Sultana?." Jin sunan da ya kira ta ya saka ta kalle shi tace, "Muwaddaty sunana ba Sultana ba." Yayi murmushi yace, "Ohh sorry Muwaddaty, fushin na meye?." Ta girgiza kanta tace, "Ba kai bane daga yin maganar makaranta sai ka kawo min zancen da zai b'ata min rai, in baka so nayi ai sai ka fad'a min ba sai ka fad'a min maganar da zatayi barazara ga zuciyata ba" ta kalle shi tace, "Wallahi Sultan zuciyata bugawa take yi ji nake kamar zata fashe" ta fad'a tana kallon sa kamar zatayi kuka.
Yayi murmushi ya rik'e hannunta amma baiyi magana ba sai daga baya yace, "Na fad'a miki gaskiya ne Muwadda, ba tsarin gidan sarauta bane tafiya karatu ka bar miji a wani garin" ya fad'a yana kallon idanun ta.
Shiru tayi dan tasan akwai k'arashen maganar raba maganar yayi sai ya gama hutawa yana ja mata aji zai fad'a. Shiru ya sake ratsawa kafin yace, "A wata masarautar zama da mace d'aya haramun ne a al'adar su, a nan ba lallai bane amma ki duba Abbana kiga matan sa nawa." Kallon sa tayi tace, "me kake nufi? Me kake so kace min?."
Yayi dariya mai sauti ya girgiza mata kai ya jingina da bangon kujera yana kallon ta amma baice komai ba, sai da suka d'auki mintina goma a haka sannan yace, "Babu abinda nake nufi, ina fad'a miki ne in kina son karatu har matakin PHD zakiyi Muwaddaty, ki zab'i duk inda kike so zan kaiki amma ki sani zaki bar wata a nan ke kina can duk sanda na samu lokaci zanzo wajan ki." Sai kawai ta fashe da kuka ya runtse ido yasan daman sai anyi haka tace, "Kawai kace min kana so ka k'ara aure basai kana yi min magana cikin magana ba, wayyo Allah na shiga uku" ta fad'a tana sake fashewa da kuka.
Bai kulata ba sai da ta gaji da kuka tayi shiru ta mik'e zata tafi taji yace, "In ina da ra'ayin a baya a yanzu na sauke, ki duba abubuwan da suka faru a gidan nan bazan so su faru da abinda zaki haifar min Muwaddaty." Ta juyo ta kalle shi yace, "Beside bana da wannan ra'ayin ke kawai kin ishe ni rayuwar zaman duniya, bazan iya had'a ki da kowa ba ke kawai kece." Dawowa da baya tayi ta zauna ta rungume shi tana dariya yayi dariyar shima amma baice komai ba.
"Har naji dad'i da ka saka naji tsoro, indai haka ne na fasa karatun bazan sake maka maganar sa ba na hak'ura." Baice komai ba ta d'ago ta kalle shi taga yana kallon ta yayi murmushi ya dungure mata kai a zuciyar sa yana aiyana tabbas zatayi karatun tunda tana so.
Basu fito ba sai magariba suka wuce wajan Abba tare suka gaishe shi kafin su rabu ta koma ta barshi tare dashi. Abba ya kalle shi yace, "Naji dad'i da naga kana farin ciki Asad, hak'ik'a naji dad'in da ka samu mace mai tarbiyya wacce zata d'ebe maka kewa a koda yaushe."
Asad ya kalli Abba nasa yace, "Abba yanayin jikin ka ya canja." Mai martaba yace, "Jiki yak'i dad'i cikin kwanakin nan Asad, shiyasa na ce ka gaggauta dawowa duk da daman kana cikin garin nan na sani na kyale kane ka huta kamar yadda kake buk'atar sa. Jikina yak'i dad'i gabad'aya daman jikin tsufa sai a hankali kullum mutuwa sake gabato mu take."
Jikin Asad yayi sanyi ya kalle shi sai gaban sa ya fad'i Abba yace, "Ka yiwa iyayen Jidda gaisuwa kuwa?." Asad yace, "Munyi da mahaifinta a waya mahaifiyar ta kuma tana wajan Mama daga nan wajan ta zanje."
"Duniya kenan, wacce suka so su kashe sai gata itace take rayuwa dakai wacce suka so ta rayun itace ta bar duniya, in baka ji tsoron Allah a a duniya babu inda imanin ka zaije."