← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 131

Sashe 116

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta bashi dariya ma amma baiyi ba ya danne ganin yadda ta wani basar ta d'aure fuska itama ya jinjina kai yana girmama k'arfin hali irin na mace, in ba ita ba waye yana zaune a kan kujera zai zauna? Waye zai wani d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa a gaban sa?, lallai ba'a yiwa mace mulki in taso nata mulkin sai yafi na ko wanne shugaba.

D'auke kai yayi daga kallon ta ganin yayi mata banza ya skaa ta kalle shi taga bama ita yake kallo ba waya yake dannawa suna chart da son MD d'in sa na company akan sabon aikin da suka samu. "Ina da abin yi fa" ta fad'a ba tare da ta kalle shi ba. Sarai ya jita sai yayi kamar ma baiji ba ta sake cewa, "Ina da bak'i ni zan tafi."

Kallon ta yayi sai ya d'auke kansa daga kallon ta ya sake yi mata banza. Ganin hakan kawai sai ta mik'e zata bar wajan taji yace, "Dawo." Sai ta fara yi mata dara tana buga k'afa a k'asa kamar zatayi kuka tana cewa, "Nace maka ina da bak'i kana ji kuma ina magana kayi banza dani."

Nan ma banza yayi mata kafin ya d'ago ya kalle ta ya hard'e hannu a k'irji ya juya kansa yana k'are mata kallo kafin ya mata alama da hannu taje. K'aramar harara ta sakar masa yana kallon ta ta juya ta sauka shi kuma yayi dariya kad'an dan ta bashi dariyar sosai.
Tunda ta bar wajan sa basu sake had'uwa ba tana wajanta tana ta amsar bak'i daga waje daban-daban na gidan har Habiba da Walida kawayen ta yadda suke mata sai ta dinga jin nauyin su.

Waya sukayi da Umma take ce mata taje ta duba Mama kar abinda ya faru a baya yayi tasiri a zuciyar ta duk abinda zatayi ta dinga tuna Asad d'in. ta gamsu da abinda Umma tace bayan sun gama waya ta kira number Asad, bai d'auka ba har ta katse bata sake kira ba ta ajjiye wayar.

Kusan mintina ashirin da kiran ya kirata ta d'auka ta saka a kunne tayi sallama bata jira ya amsa bama tace, "Ammmmm daman ina so naje duba Mama ne." Shiru yayi kamar bai ji ba itama tayi shiru dan tasan yana jinta sai da aka d'auki lokaci sannan yace, "Suhail zai kaiki" yana fad'a ya datse kiran tabi wayar da kallo tana harara kamar shi take harara.

Ba jimawa hadimar ta ta shigo ta sanar da ita zuwan Suhail ta bada umarnin ya shigo ya shigo yana fad'in, "Allah yaja da ran Fulani." Dariya kawai tayi dan bawai ta iya wad'annan abubuwan bane tace, "na taso ne?." Suhail yace, "zamu iya tafiya."
Ita da Jakadiyar ta suka tafi Suhail yaja motar suka je asibitin har lokacin Mama bata farka ba taga jikinta suka gaisa da Suhaima da kannen Maman kafin ta dawo gida dan da fitar da dawowar ba'a yi mintina talatin ba.

Da daddare Hydar ya kaiwa Mama ziyara a lokacin babu kowa a wajanta sai security ya shiga har gaban gadon da take kwance ya zauna yana kallon ta kafin yace, "Mama nasan wataƙila kina jin abinda zance; nazo dan naga lafiyar ki na kuma shaida miki abubuwan da suke raina."

"Wato Mama nasan kaf cikin y'ay'an ki kinfi sona tabbas nasan da wannan amma kinfi nuna k'aunar Asad a kaina tunda shi kike yiwa burin zama shugaba bamu ba, baki tab'a tunanin hakan zai k'ona mana rai zai kuma iya sakawa mu dauki mataki ba, kawai abinda yake zuciyar ki kike fito dashi bakya duba da yanayin da hakan zai jefa mu tunda muma jinin sarauta ne. Kullum zancen ki Asad ya mulki garin nan ko kara baki tab'a yi mana ba shin mu babu jinin sarautar a jikin mu ne? Ko kuma Asad ne kawai ya gaji sarauta banda mu?."

"Mama a duk sanda kika fad'i haka ina jin kamar na bawa Asad guba yasha ya mutu sabida banbancin da kike nunawa k'arara a kanmu, bakya tunanin komai sai shi kawai bayan muma y'ay'an kine muna da hakki a kanki ko sau d'aya ki ambace mu dukkan mu babu wanda baya son sarautar amma maganar d'aya ce kullum Asad!" Ya fad'a cikin fusata yana dafa gadon da take kai kafin ya cigaba da fad'in, "Na shirya abubuwa da yawa akan ganin bayan duk wanda zai hanani mulkar garin nan koda kece Mama, ina nan akan baka ta duk abubuwan dana shirya a baya baza su zama a banza ba sai na aiwatar da kudurina. Jiya na bawa matar Asad maganin zubar da ciki amma na fahimci tayi min wayo ne bata sha maganain ba to ai in tasan wata bata san wata ba zanyi maganin ta cikin k'aramin lokaci."

"Mama ban hak'ura da mulkin nan ba ina nan ina shirin yadda zan ga bayan Asad da mijin ki, koda kece zan iya ganin bayan ki a duk sanda naso indai burina zai cika. Kiyi haƙuri Mama amma bazan iya hakura ba sai na tabbatar da burina ya cika hankalin kowa zai kwanta. Ina baki hak'uri in kika farka kika samu bak'in labari ba laifina bane laifin kine."

Buɗe k'ofa akayi aka shigo ya kalli wanda ya shigo yaga Suhaima ce kawai sai ya mik'e ya fita bai mata magana ba a daidai lokacin da Mama ta fara wani irin numfashi k'irjin ta yana sama da k'asa.
Hankalin Suhaima ya tashi ta fita a guje suka dawo da likita aka yiwa Mama allura  amma har lokacin numfashin baiyi daidai ba dak'yar aka samu numfashin ya tsaya tana kuka ta kira number Asad ta sanar dashi halin da ake ciki.

A daren suka fito shida Suhail suka tawo hankalin sa a tashe, lokacin da suka zo ta koma bacci likita yake sanar dasu an fad'a mata maganar da ta tayar mata da hankali ne shiyasa hakan ta kasance in aka cigaba da hakan kuma zuciyar ta zata iya bugawa. Nan take Asad ya saka dokar ko waye kar a sake barin sa ya shiga sai Suhaima kawai da kannen Mama in basu ba kar a sake barin wani yazo inda take.

Ransa a b'ace ya koma gida yaga Rauda a saman sa ko ta kanta baibi ba ya wuce itama bai isheta kallo ba balle ta kalle shi ta tab'e baki ta cigaba da hira da Yaya Ummi a wayar ta domin tayi alwashin nuna masa itama fa bazata d'auki wulak'anci ba sai dai duk abinda zai faru ya faru.

Bayan kwana biyu.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*088*

        Cikin ikon Allah a cikin kwanakin duk wani abu da Aliyu ya b'ata da ya shafi masarauta Asad ya gyara shi da taimakon Abba, duk wata sadaqa da aka daina yanzu an dawo da ita komai yana tafiya bisa tsari Asad yna k'okari ganin komai ya tafi bisa tsarin addinin musulunci. Ma'aikatan gidan su kansu sun san an samu canji sosai kowa farin ciki yake yi don sakaqa da taimako ya dawo.

A cikin kwanakin Rauda da Asad babu abinda yake had'a su magana ba sai anga dama tun tana zuwa ma b'angaren sa har ta share ta daina daman sabida mutane take yin wani abun to ta gaji da wulaƙancin itama ta watsar dashi sai a kwana a wuni ma a sake tashi basu had'u dashi ba balle magana.

Jikin Mama yayi sauk'i sosai duk da batayi magana ba tunda ta farka amma jikinta ya warware sosai sai dai an kafa mata sharud'a akan ahiga damuwa da yawan tunani. A ranar da ta kasance ranar laraba da safe aka sallamo Mama ta dawo b'angaren ta bayan an gyara mata b'angaren nata. Tun safe ake karb'ar bak'i amma har lokacin batayi magana ba Asad kawai take son gani amma shiru bai shigo ba duk ta damu.

Shi kam bayan an tashi daga zaman fada kai tsaye wajan ta yayo tunda aka hango shi aka fara bada hanya ana kirari sosai saman sa da lema har ya k'araso k'ofar falon Mama. Sauke Lemar akayi ya shiga ciki su kuma duk suka tsaya a waje ya shiga ya same ta zaune ita da k'annen ta mata biyu wanda suke wajan ta.

Tunda yayi sallama ta mik'e har ya k'araso ya tsuguna a k'asa yace, "Barka da dawowa Mama." Sai a sannan bakin ta ya buɗe bakin ta yana rawa tace, "Asad!." Kowa yayi mamakin jin maganar ta farin ciki ya cika zuciyar su har lokacin bai tashi ba. Zama tayi akan kujera shi kuma ya zauna a k'asa kusa da ita tana ta kallon sa kafin ta fashe da kuka.

Hankalin Asad ya tashi ya kalle ta yana kallon fuskar ta yace, "Zubar da hawaye bai kamaci mahaifiyata ba, dan Allah Mama ta daina kuka nima hakan yana cutar dani." Mama ta dinga kuka kafin ta share hawayen ta ta kalle shi tace, "Asad kayi haƙuri."

Kai ya dafe yana kallon ta kamar zaiyi kukan shima yace, "Subahanallah! Dan Allah mamana ta daina furta wannan kalmar dan Allah" ya fad'a yana dafe kansa da yake sarawa. Mama tace, "Dole na baka haƙuri Asad na cutar dakai akan abubuwa da yawa dan ka kasance me yi min biyayya na dinga tauye maka hakki, kayi haƙuri ka yafe ni" ta sake fad'a cikin kuka sosai.

Ya kasa magana sabida shi kansa sarawa yake yi Mama Jamila tace, "Haba Maman Suhaima, dan Allah ki daina wannan kukan kinga kin saka Asad din cikin wani yanayi mara dad'i. Ga abinda likita yace" Ta kalle su tace, "Dole nayi kuka Jamila, na cutar da Asad iya cuta duk abinda ya nuna yana so sai na raba shi dashi bana duba halin da zai shiga kawai cikar burina nake so. Ban tab'a addu'ar in mulkin nasa ba alkhairi bane Allah ya hana shi kullum alkhairi nake hangowa ban tab'a fad'awa Allah yayi min zab'i ba. Na raba Asad da aikin sa, na raba shi da burin sa, na raba shi da duk wani abinda yake so hatta matar da yake matuƙar qauna na raba shi da ita kawai dan na samu cikar burina."
Chapter 116 · 0% Book details