← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 131

Sashe 33

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar ta kurma ihu haka take ji amma ya zatayi ita take nema dole tayi shiru tana kallon sa ta kuma cewa, "Allah ya taimake ka magana nake yi." Sai a sannan ya kalle ta yace, "Ina jinki." Ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido ta sauke kai k'asa tace, "yaushe akayi masa umarnin dawowa?."
"Ba yanzu ba."
"Amma meyasa ranka ya dad'e?."
"Haka nayi niya."

Ta taune bakin ta tace, "Amma Takawa bai kamata ayi hakan ba tunda har ka bayar da kujerar nan me za'a jira kuma?." Ya sake kallon ta yace, "to Rabi'a fad'a min abinda ya kamata sai nayi."
"Allah ya wuci zuciyar ka."
"Mtswww." Sake kallon sa tayi zatayi magana yace, "Ina da iko da Asad kamar ke, ina da ikon na saka shi yayi abinda nake so kamar ke, dan haka ki k'yale ni sai sanda naga dama zai dawo."

Hawaye ya taru a idanun ta tace, "Yanzu fa Asad ko nema na bayayi matar da ka aura masa ta juyar masa da hankali daga kaina gabad'aya, rabon da naji muryar Asad har na manta, wallahi ina so na ganshi kayi min izinin zuwa naje can koda bazan dawo bashi" ta fad'a hawaye yana sakko mata.

"Ban bada dama ba Rabi'a, indai nine wanda yake auren ki ban baki umarnin barin k'asar nan ba, in kuma kina ganin kin isa bismillah." Mama tace, "nidai gaskiya bazan zuba ido ina ji ina gani a raba ni da d'ana ba, dole naje inda yake."
"Indai ina da rai da lafiya baki isa fita daga Nigeria ba Rabi'a, ke ko garin nan baza ki bari ba sai na bada damar hakan."

Cikin kuka tace, "Shikenan yanzu ka sallamawa wata banza shi ta raba ni dashi ta raba shi da k'asar sa?." Bai amsa mata ba ta mik'e tsaye tana goge idanun ta ta gyara zaman alk'yabbar  tace, "Kayi hak'uri ranka ya dad'e amma sai na dawo da d'ana garin nan, sai ya dawo ya karb'i mulkin sa."
"Kayi duk abinda kika ga dama Rabi'a" abinda ya furta mata kenan ta fita zuciyar ta na sak'a mata hanyar da zata bi wajan ganin tayi abinda take so domin matuk'ar yana raye tabbas bazai bata damar yin abinda take so kamar yadda yace, dole ta d'auki mataki bazata zuba ido wata bak'a mai mummnar fuska ta kwace mata shi ba dole ya dawo ya cika mata burin ta na zama sarki ya kuma auri Jidda........
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*042.*

         Da ciwon kai ya tashi zaune idanun sa har lokacin a kulle ya jingina da fuskar gadon yana sauke numfashi a hankali, ya jima a haka kafin ya bud'e idanun yaga d'akin babu haske ko kad'an ya zura hannu gefen sa ya kunna switch d'in wutar nan take haske ya bayyana a wani sashe na d'akin. Agogo ya fara kalla yaga k'arfe uku da arba'in na dare ya kalli d'akin gabad'aya abinda ya faru yana dawo masa a hankali.

Lokacin da ya gama tuna abinda ya faru sai ya kalli kansa yaga babu riga a jikin sa amma akwai short niker, tunawa yayi da lokacin da abin ya faru ai babu komai a jikin sa ya akayi yaga boxer a jikin sa?. Kansa ya dafe jin yadda ya kuma sarawa har lokacin marar sa a d'aure take ya daure ya tashi tsaye yayi saurin komawa ya zauna jin jiri na neman kayar dashi sai da ya d'an huta sannan ya tashi yana takawa a hankali ya fito zuwa falon, duhu shima falon bai kula da ita a akan kujera ba burinsa yaje ya fara tsarkake kansa ya wuce zuwa d'aki ya shiga tare da kullo k'ofa.

Band'aki ya shiga kai tsaye yana dafe da kansa har lokacin yayi abinda zaiyi a ciki ya fito d'aure da towel a jikin sa yana goge kansa da guda d'aya, shiryawa yayi ya saka doguwar riga mai santsi ya shinfid'a sallaya ya kalli gabas ya tayar da sallah. Ya jima yana sallah har akayi kiran farko na asuba sannan ya zauna yana lazumi yana cin sassuci akan abinda yake ji a jikin sa. Bayan an idar da asuba ya cigaba da lazumin sa yayi azkar kamar yadda ya saba ya d'auki littafan sa yana dubawa duk da baya jin dad'in jikinsa.

Rufe littafin yayi yana kallon wani waje daman yana sake tuno abinda ya faru har ya tsinci kansa a yanayin da bai tab'a shiga ba tunda yazo duniya, "kenan ita ta saka min shortniker?" Ya furta a bayyane yana d'an wara idanun sa yana jin wani iri a jikinsa. "Wanne irin yanayi ne wannan? Meya faru dani?" Ya fad'a yana dafe jijiyoyin kansa da suke sarawa masa ya ajiiye littafin ya tashi ya fito falon. A zaune ya same ta itama tana karatun alkur'ani da ka ba tare da alkur'ani a hannun ta ba tana bin ko wacce aya daki-daki tana lumshe idanun ta alamun karatun yayi mata dad'i.

A kan kujera ya zauna yana kallon ta kafin yaga ta kai k'arshe sura ta bud'e idanun ta ta kalli gefen da yake, had'a ido sukayi taga ya fad'a lokaci guda jijiyoyin kansa a mike har lokacin sai tace, "Ina kwana, ya jikin?" Ta fad'a a tare tana kallon sa.
Da hannu yayi mata alama da tazo inda yake ta mik'e a hankali tana takawa har taje gab dashi juwa ta kwashe ta ta fad'a kansa gabad'ayan ta dan ita ba k'arfi gare ta ba.

Zafi yaji a jikinta alamun zazzab'i ya cize baki yana kallon idanun ta kafin ta sauke nata k'asa, muguwar soyayyar ta yake ji tana sake shiga ko ina na jikinsa, son kasancewa da ita har abada yana sake ninkuwa sau babu adadi a zuciyar sa. Baya son rabuwa da ita domin yana sonta kuma ita kad'ai ce sirrin sa tunda gashi itace ta suturta masa jikin sa lokacin da yake kwance babu lafiya, ko mahaifiyar sa tun yana yaro rabon da ta saka mishi suttura to me zai saka rabu da ita bayan wannan babban matsayin da ta samu wanda babu wacce ta same shi?.

"Jikin ki akwai zafi" ya furta yana kallonta. Jikinta har rawa yake a hankali tace, "Nasha magani." Shiru yayi baiyi magana ba sai kallon ta da yake yi yana jin kamar ya mayar da ita jikin sa ya huta da kewar ta da yake ji a ko wanne lokaci a zuciyar sa. In akace zai so mace kamar yadda yake sonta zai karyata faruwar hakan amma da yake Allah shine mai tsara komai sai gashi yana jin sonta fiye da komai a duniya. A kan kujerar ya ajjiye ta ya mik'e ya k'arasa inda butar shayi take ya kunna nan da nan tayi zafi ya had'a tea a kofi ya dawo inda take ya zauna ya mik'a mata yace, "take it."

Kunyar sa take ji ba kad'an ba hakan ya saka ta mik'a hannu zata karb'a shi ya d'auka ta rik'e sai ya saki sai kuwa ya d'an zuba a yatsan ta ta yarfe hannu shayin ya zube a wajan, "wayyo Allah" ta fad'a tana yarfe hannun ta yayi saurin karb'ar hannun nata ya saka yatsan a bakin sa kamar alawa. Shiru tayi tana kallon sa shima ita yake kallo kafin ya zame shi daga bakin sa ya kalli yatsan nata sai kuma ya saki hannun nata ya tashi ya shiga d'aki.

Jim kad'an ya dawo da wani cream dogo a hannun sa ya bud'e ya shafa a yatsan nata ya kalle ta yace, "Sannu, ko muje asibiti?." Kai ta d'aga zai kuma tashi ta rik'o shi tace, "Bana jin zan iya shan tea ka barshi kaima baka da lafiya." Bai fasa tashin ba ya k'arasa fridge ya d'auko lafiyayyen yogurt mara sanyi sosai ya k'araso kusa da ita ya zauna ya bud'e ya nufi bakin ta dashi. Ba yadda ta iya haka ta bud'e baki ya zuba mata ta shanye ya sake bata ta sake shanyewa a haka sai da yaga ta sha da d'an yawa sannan ya k'yale ta ya d'auko magani ya bata tasha ya sake tab'a wuyan ta yaji har lokacin da zafi.

"Jikin ki akwai zafi still, meyasa bakya son ganin Dr?."
"Ai naji sauk'i bana son fita ne yanzu."

Da kafad'ar sa ta tayar da kai shi kuma ya rik'e hannunta, babu mai magana a cikin su kowa yayi shiru tana kwance a jikin sa yaji saukar numfashin ta alamun tayi bacci ya kalle ta yayi mata kiss a goshi ya tashi ya d'auke ta ya kaita d'akin sa ya kwantar a kan gado ya zauna gefen ta yana shafa goshin ta a hankali cikin k'auna da soyayyar ta mai tarin yawa.

*☆☆☆*

           "Mai martaba sarki mai murabus ne babu lafiya, yanzu haka ance jikin sa ko motsi bayayi yana kwance kamar gawa" hadimai suke suna tafiya suna tattauna maganar cikin jimami. A wannan lokacin Hankalin Hydar a tashe yake sosai sai shige da fice yake so yake private get d'in Asad da za'a d'auke shi a kaishi Germany ya zama ready domin yanayin jikin sa ya gigita shi.

Dukkan iyalan sa suna zagaye dashi har y'ay'an sa mata da suke gidajen mazajen su sun hallara suna zaune an saka shi a tsakiya kowa yayi shiru ana yi masa tofi masu kuka suna kuka masu jimami suna jimami.  Fari siririn mutum ne zaune kusa dashi sanye da lab court kana ganin sa zaka fahimci likita ne sabida yadda yake yake ta had'a magani da allura yana yi masa ko za'a samu ya motsa amma abin yaci tura sai idanu kawai da yake bin mutanen d'akin dashi.

Bayan ya kammala ya kalle su yace, "I'm sorry to say, na kasa gane abinda yake damun sa tafiya Germany d'in kamar yadda Hydar ya fad'a is better." Mai martaba sarki mai rik'on kwarya yace, "Dr jiya fa lafiya lau yake meya same shi da sauri haka?." Dr yace, "Allah ya taimaki sarki bana ce ba, kuma ita k'addara tana samun mutum ne a ko wanne lokaci koda bai shirya ba."
Chapter 33 · 0% Book details