← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 131

Sashe 111

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asad yayi shiru baice komai ba Mai martaba yace, "Munyi magana da mahaifinta d'azu sun san da batun dawowar ta jibin an gama gyara b'angaren da zata zauna komai an tanadar mata ita akwai ake jira ta dawo dan cikar martabar ka." Asad ya girgiza kai alamun gamsuwa kafin yace, "Allah ya taimake ka ba'a ce komai akan Maman ba."

Yayi y'ar dariya yace, "wato hankalin ka yana kan Maman ka ba matar ka ba, zanje naga yanayin jikin nata kawun ka ma an sanar dani d'azu a wajan zaman makoki ya yanke jiki ya fad'i an kaishi asibiti." Asad ya girgiza kai yace, "Ina godiya mai martaba Allah ya k'ara lafiya, Allah ya bashi lafiya shima." Ya amsa da amin kafin Asad yace, "Abba Aliyu."

Mai martaba yace, "Zai samu lafiya in sha Allah ka kwantar da hankalin ka sai a hankali komai zai wuce. Kun had'u da Hydar ne?." Ya d'aga kai alamun eh yace, "Akan hanyar mu ta dawowa daga wajan Mama jiya muka had'u."
"Kar hankalin ka ya tashi a duk abinda zaice yana neman hanyar da zai fusata kane shiyasa zai fad'a maka maganar da ranka zai b'aci, ka kwantar da hankalin ka babu abinda zai faru." Daga nan suka cigaba da tattaunawa akan lamarain gidan ciki da wajen sa.

Da daddare Asad ya kira Suhail bayan ya d'auka ya sanar dashi yana neman sa ba jimawa kuwa ya bayyana a falon Asad ya bashi umarnin zuwa sama ya hayo ya same shi a tsaye yace, "Suhail zamu je wajan Mama, but bana so kowa yasan zamu fita ina nufin nida kai kawai."

Suhail yace, "Amma ranka ya dad'e fita babu jami'an tsoro akwai ganganci duba da yanayin dake ciki yanzu." Asad yace, "Haka nake so."

Suhail zaiyi magana ya d'aga masa hannu dole yayi shiru yace, "Allah ya wuci zuciyar ka" ya fad'a yana komawa k'asa shima ya sakko k'asan yazo da mota har k'ofar b'angaren sa ya shiga bayan motar suka fita.

Yadda suka barta d'azu haka suka kuma ganin Mama sai dai Suhaima taji sauk'i ita ta samu kuzari ya umarci Suhail da ya barshi a nan yaje aka siyowa Suhaima abinda zata ci da abinda zata sha ya dawo ya same shi.

Basu jima sosai ba suka baro asibitin suna tafiya a kan titi Asad baice komai ba ya zubawa titi ido kawai ba tare da yayi magana shi kad'ai yasan abinda yake zuciyar sa. Abinda ya gani shine ya firgita shi ya kalli Suhail ya masa alama da ya tsaya yaja ya tsaya yana kallon gefe inda yake kallon abinda yake haddasa masa bugun zuciya.

Rauda ce a tsaye a wajan mai siyar da kayan marmari hannunta rik'e da leda da alama ta gama siya ma tana bashi kud'i, ransa yaji yayi mugun b'aci ya zuba mata ido kawai yana kallon ta ya saukar da glass d'in K'asa kasancewar akwai duhu a wajan ba kowa ne zai gane shi ba.  Suhail ganin abinda yake kalla sai shima ya kalli wajan ya ganta sanye da dogon hijjabi har k'asa fuskar ta a buɗe tana k'okarin tsallaka titi.

Titin ta tsallaka ta tsaya tana yatsine fuska alamun gajiya a tare da ita tana kallon titin, Suhail ya kalla baiyi magana ba sai ya juya kan motar yaje daidai da ita ya tsaya amma basu sauke glass ba. K'aramin tsaki taja tayi gaba tana sake kallon hanya Suhail ya sake yin gaba ya sauke glass lokacin ta juyo take idon su ya had'u dana Asad.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*084.*

        Kallon idon Asad yayi sai kuma ya kyalkyale da dariya ya jiya bindigar a hannun sa yace, "Relax our king babu bullet a cikin bindigar, taya zan kashe ka Abba yana raye? Ai kamar na kashe maciji ne ban sare kai ba. Sai na gama da Abba na gama da babyn cikin Rauda then sai na dawo kanka" ya fad'a yana kallon bindigar yana dariya.

Asad yayi murmushi shima ya kalli taga kafin ya dawo da kallon sa ga Hydar yace, "Hydar babu abinda zaka iya yi min, wani nawa ma baza ka iya yi mashi komai ba balle ni." Hydar ya sake yin dariya yana girgiza kai yace, "Asad d'in Mama, babu dalilin da zai saka na kasa ganin bayan ka, burina shine na d'auki ran kowa ciki harda naka ran" ya fad'a yana kallon sa.

Asad baiyi magana ba Hydar yace, "Ya jikin Mama? In ta farka kace ina gaishe ta ka kuma sanar da ita ina kan cika burin ta ne dan naga kai babu abinda zaka iya" ya fad'a yana kallon idanun sa. Kallon sa shima yake yi Hydar ya d'aga riga ya sake yin dariya yace, "Asad nasan kana jin Hydar a zuciyar ka" ya dafa kafaɗarsa yana bubbuga ta yace, "Hydar ina son Asad amma kuma yafi son mulki a kanka."

"Lokacin da na dawo Nigeria zan yi swapping sim card me ka bani abinci naci?" Asad ya tambaya yana kallon sa. Dariya Hydar ya sake yi yana tafa hannu kana yace, "Y'ar dabara ce irin tamu ta k'ananun yara ba wani abun bane ba" ya fad'a yana kallon sa har lokacin fuskar sa da murmushi.

Asad baiyi magana ba Hydar yace, "kana da yarda da yawa shiyasa a ko yaushe ake cutar dakai, nasan tun a Germany ka gano ni musamman lokacin da ka dage akan a kai Abba India nak'i tun a sannan nasan ka saka min question mark baka nuna min bane ba amma kar ka manta harara Asad yayi nasan me yake nufi, shiyasa tun a lokacin nayi maganin ka."

Ya sake kallon Asad d'in suka had'a ido sai ya d'an yi k'aramin tsaki yana runtse ido yace, "idon ka yana saka ni jin wani iri a jikina ka daina kallona haka bafa sata nayi maka ba."  Kafin Asad yayi magana ya kuma cewa, "in kuma ba haka ba a juya akalar auren ka da Rauda ya dawo kaina, cikin sauk'i zan raba ku na aure ta daman can tawa ce. Kaga sai ayi 2_0 Aliyu ya rik'e Jidda ni har da albarka an samu ni kuma na rik'e Rauda" ya fad'a yana d'agowa ya kalle shi.

Asad ya lura so yake ya hasala shi ransa ya b'aci sai yayi murmushi yace, "Hydar!." Hydar ma yayi murmushi yace, "Asad! Sai fa kayi haƙuri na shirya wasu abubuwan da yawa za'a rasa rai za kuma a rasa lafiya. Tabbaci nake baka akan cikin jikin matar ka sai ya zama babu shi dan in zan k'yale komai bazan k'yale cikin ba, ka shammace ni ban san za'ayi ciki da sauri haka ba dan ban bari an zo wajan ba. Duk d'auka nake har yanzu abin sautin ya daina d'aukar sauti ashe ya gyaru har amo yake fitarwa ba iya sauti ba" ya fad'a yana kallon sa shima shi yake kallo.

Hydar yace, "Ashe sitiyarin motar ya dawo da aiki yadda ya kamata na d'auka tunda Mama ta lalata shi bai dawo daidai ba ashe nine nake haukan banza tunda gashi harda ciki."

Asad ya sau ke numfashi yace, "Ko a mafarki kar ka d'auka wannan abinda kake fad'a zai kasance." Hydar ya hard'e hannu a k'irji yace, "to muyi deal mana, in na zubar da cikin ta me zaka bani? Ni kuma indai ban zubar da cikin ba ka saka a kashe ni."  Asad yace, "bani da lokacin da zan tsaya yin deal dakai Hydar, bana da lokacin da zan saurari shirmen ka mai kama da tatsuniya. In kayi nasara a kaina a kwanakin baya tabbas yanzu ni zanyi nasara a kanka."

Hydar ya murmusa yace, "Kana nan yadda na sanka confidence d'inka yana nan, to in ban tabbatar da shirina a kanka ba ai ba sunana AliyuHydar ba." Asad yace, "fitar min a mota." Hydar yace, "Daga na ambaci Rauda sai a kore ni daga mota? Ayi haƙuri tuba nake ranka ya dad'e ba wani abun nace zanyi da ita ba ai" ya fad'a yana yi masa jinjina kafin ya sake kyalkyalewa da dariya yace, "Zan fita Asad koda baka ce ba, amma ina so kasan zan dawo gare ka bazaka tab'a zama lafiya ba matuk'ar ina raye sai na raba ka da komai da ka mallaka ni na mallake shi ciki kuma harda matar ka da kake so. Zamu had'e nan bada jimawa ba, ina nan zuwa gare ka" yana gama fad'ar hakan ya fita daga motar ya shiga tasa motar yaja a guje.

A lokacin escorts d'in sa da Suhail suka dawo Suhail ya shiga motar uana fad'in, "Ranka ya dad'e fatan komai lafiya? Naga bindinga a hannun sa." Asad ya masa alama da su tafi kawai driver yaja motar kai tsaye gida suka wuce.

Shiru Asad yayi suna tafiya tunani yake yi ta ko ina Hydar ya gama gano lagon sa, ta ko wanne b'angare ya karance shi sosai shiyasa cutar dashi bazai yi wahala ba. Tambayar da yake yiwa kansa itace anya Hydar zai iya kashe shi? Yasan har yanzu Hydar yana sonsa anya zai iya kashe shi?. Bai gama nemo amsar tambayar ba suka iso cikin gidan kai tsaye b'angaren sa ya wuce.
Suhail yana bayan sa bayan sun shiga falon yace, "Suhail a tabbatar an sake k'ara tsaro a kaf gidan nan, inda babu camera ina so a saka" ya fad'a yana dafe kansa.

Suhail yace, "An gama ranka ya dad'e. Allah yaja zamanin ka Fulani Hajiya ce take neman izinin ganin ka." Asad ya sauke numfashi a wahale yace, "Suhail bana jin zan iya ganin kowa. Suhail na gaji sosai."
"To ranka ya dad'e sai a sanar da ita" ya fad'a yana juyawa zai koma.

"Tazo" ya fad'a a hankali Suhail ya amsa ya fita. Zama yayi a kan kujerar da take mallakin sa ba jimawa Hajiya ta shigo da kaf y'ay'anta mata da namiji ganin hakan sai ya mik'e tsaye suka k'araso yace, "Hajiya da an sanar dani da nazo da kaina."
Chapter 111 · 0% Book details