← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 131

Sashe 68

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi tayi kawai taji Ramla tace, "gashi duk matsayin ki sai kin bi layi baya tauyewa talakawan da suke zuwa wajan sa hakki akan masu kud'i. Yanzu ka duba motar da muka bari kamar ta gidan sarauta amma layi take bi." Dr yace, "Ai ba ganin Idanun Rauda ba ban tab'a ganin malami kamar sa ba."

Ita dai murmushi kawai take yi Ramla tace, "Sis badan kar kice na cika tambaya ba dana ce daman kin tab'a aure ne?, naji yana miki zancen idda." Rauda ta sauke numfashi tayi shiru tana kallon hanya annurin fuskar ta ya d'auke gabad'aya ganin hakan sai Ramla tace, "Kiyi hak'uri dan Allah."

Rauda ta wayance tace, "Lah babu komai fa Sis, abin ne in na tuna yana saka ni a wani yanayi mara dad'i. Na tab'a aure ban jima da fita daga idda ba Sis." Ramla tace, "kenan lokacin da kina Egypt da auren ki?." Rauda ta girgiza kai tace, "Eh, wanda muke tare dashi shine mijina. Hydar k'anin Asad shine silar samun matsalar k'afa ta shine ya buge ni a mota har k'afata ta samu matsala. Daga nan Asad ya nuna yana sona amma Maman sa ta hana hakan, da yake dai Allah ya rubuta sai na kasance matar sa ban sani ba Mai martaba mahaifin sa ya karb'i aurena wajan Babana akayi auren ba tare da Maman sa ta sani ba, bama iya ita kad'ai ba da yawa mutane basu san anyi auren ba muka tafi nan Egypt aka samar min da lafiyar k'afa ta. At the end dai auren bai wuce sati hud'u ba ya mutu wannan lokacin da Dr ya taimaka min har nazo gidan ki anyi sanki Maman sa tace kuma sai na fita" ta k'arasa fad'a muryar ta na shaking.

Ramla ta kalli Khalifa shima ya kalle ta cike da mamaki da al'ajabi Rauda tayi shiru ta mayar da hawayen idanun ta tace, "Na d'auke ku y'an uwana shiyasa na fad'a muku dan Allah bana so maganar nan ta fita dan bani so mani asan nayi aure, yadda mutane basu san ya aure ni ba d'auke suke aikin k'afa aka yi min muka dawo muje a hakan kawai." Ramla tace, "in sha Allah babu wanda zaiji Rauda. Allah yabi miki hakkin ki domin dukkan su sun cutar dake daga shi har Babar tasa."

Shi dai Dr baice komai ba zuciyar sa cike da mamakin abin har suka je gida suka sauke ta har  gida Ramla ta shiga ta yiwa Umma sallama sannan suka wuce.

Bayan sallar la'asar Umma da Rauda suna zaune suna hira Baba ya shigo yana fad'in, "Rauda har kunje wajan Baba malam d'in?." Rauda tace, "Munje Baba tun d'azu muka dawo." Ya zauna yana fad'in, "To yayi kyau." Ya kalle ta yace, "Binta Anas yazo min da maganar yana neman izinin fara zuwa wajan Rauda mtsayin me neman auren ta a karo na biyu, tun jiya yayi min maganar yanzu kuma yazo yana can k'aramin d'akin can yana jiran ta."

Gaban Rauda ya fad'i ta kalli Umma itama ta kalle ta sai taga Umma tayi murmushi tace, "Alhamdulillah, na jima ina jiran wannan ranar tun bayan kammala iddar ta. Amma Malam kaine ka sanar dashi ta gama idda?." Baba yace, "hira ce tazo har maganar ta shigo ciki ashe ya rik'e bai manta ba." Umma tace, "Allah sarki, wallahi ni daman can shi nake mata sha'awar aure Allah ma ya sani dan ka auri namiji mai sonka shine morewa." Baba yace, "in ya kasance mijin ta sai kiga anyi an gama kamar wancan." Ya kalli Rauda yace, "Saka hijjabin ki kije yana jiran ki zaku tattauna."

Ba musu ta tashi ta shiga d'aki ta d'auki hijjabi ta fita Umma ta bita da kallo shima Baban kallon ta yake yi yana ji kamar komai ya faru da ita shine sila amma babu yadda zaiyi ba'a goge k'addara.

Tunda ta doshi d'akin sai take jin fad'uwar gaba ta sauke numfashi ta shiga da sallama yana zaune cikin farar shadda anyi mata aikin bak'in zare sai khamshi yake yi ya amsa yana kallon ta, a gefe ta zauna tace, "Ina wuni." Yayi murmushi yace, "lafiya lau Rauda ta, ya naga kina jin kunya kamar bamu zama y'an uwa nida ke ba?." Murmushi tayi shima shi yayi ya gyara zama yace, "Nasan Baba ya sanar dake qudirina a kanki a karo na biyu Rauda, a karo na biyu na dawo gare ki ina neman auren ki Allah yasa zaki amince.:

Ta d'ago ta kalle shi tayi murmushi tace, "Yanzu ba dah bane ba, kar ka manta na tab'a yin aure." Yayi murmushi yace, "Na sani ai, k'addarar auren kice ta zama silar raba mu har iyayena suka min zab'i da Allah yayi nufin dawowar ki sai ya d'auki ran wacce aka bani tun ban aure ta ba kema ya raba ki da naki mijin. In kika duba zaki ga Allah ya tsara mana faruwar hakan tun farko K'addara ki kalar tawa ce." Kai ta girgiza cikin gamsuwa da abinda yace iya tsara kalaman sa da nutsuwar sa yana daga cikin abinda yake burge ta a tare dashi tace, "Baka ganin a wannan karon ma zasu iya yi maka zab'in?."

Yayi murmushi yace, "A wannan karon sun bani ikon zab'ar wacce nake so na riga na sanar dasu kece wacce nake so sun amince min yanzu taki amincewar kawai nake so. Bana so a d'auki lokaci nan da wata biyu nake so ayi bikin a gama bana so wata k'addarar ba fata nake ba ta sake kawo mana barazana tsakanin mu. Dan Allah Rauda ki fad'a min gaskiyar abinda yake ranki, kin amince na zama mijin ki? Kina sona a kafo na biyu ko A'a....?.Kar ki b'oye min abinda yake ranki." Shiru tayi ta sauke ajiyar zuciya ta lumshe idanun ta ta d'ago ta kalle shi tace,..........
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*060.*

            Shiru tayi kanta na k'asa sai kuma ta d'ago kai ta kalle shi ta fitar da sigh kafin tace, "zanyi tunani a kai a bani lokaci." Ya d'an wara ido yace, "Yanzu ashe ina da wani hali da sai anyi tunani a kaina?." Ta girgiza kai tana murmushi tace, "A'a ba haka nake nufi ba, kawai ina so nayi tunani ne a bani wannan damar."
"An baki ranki ya dad'e, ina fatan dai baza'a d'auki lokaci ba." Tace, "Babu lokaci in sha Allah."

"Godiya nake gimbiya." Sai tayi murmushi kad'an shima yayi murmushin tayi shiru bata ce komai ba kafin yace, "Ina sonki wallahi Rauda, duk abinda ya faru a baya ban tab'a jin sonki ya ragu a zuciyata ba. Har fa addu'a na dinga yi Allah ya cire min ke a zuciyata nasan kina da aure amma kuma na kasa daina sonki, ashe kina nan dawowa gare ni." Lumshe ido tayi ta bud'e ta kalle shi kamar zatayi magana sai kuma ta fasa tayi murmushi kawai shima sai yayi murmushin.

"Naga alama yau sarautar kike ji da ita, shikenan to zan koma yamma tayi sosai." Ta kalle shi tace, "a gaida mutanen gidan." Yace, "Zasu ji in sha Allah. Zan fad'awa Mamana sirikar ta Rauda tana gaishe ta." Murmushi ta kuma yi kafin ya fita ita kuma ta ta shiga cikin gida fuskar ta har lokacin d'auke da murmushi. D'aki ta wuce ta zame hijjabin ta har lokacin bata daina murmushi ba Umma da ta shigo d'akin tace, "Rauda."

     Juyowa tayi ta kalle ta tace, "Na'am." Umma ta kalle ta tace, "ya kike ji a zuciyar ki akan Anas?." Ta sunkuyar da kanta Umma tayi murmushi tace, "Allah yasa kin amince dashi dan ni wallahi ina miki sha'awar auren sa sabida yana sonki so na hak'ika sosai." Rauda tayi d'ago tace, "Umma indai kina son na aure zan aure shi." Umma ta wara ido tare da rik'e hab'a tace, "Ni zan zauna miki dashi da zan so ki aure shi Rauda? Kawai ina fad'a miki ra'ayina ne amma yankewa ai yana wajan ki."

Tayi murmushi bata ce komai ba Umma ta sake cewa, "Allah ya zab'a abinda yafi alkhairi, ki cigaba da addu'a" tana fad'a ta fita Rauda ta zauna a gefen gado tana murmushi ita kad'ai wanda bata san dalilin sa ba.

Tunawa da kalmar Anas da yace sarauta take ji da ita sai fuskar Asad ta fad'o mata a zuciyar ta tayi saurin kawar da ita tare da runtse ido ta cize baki tare da dukan goshin ta a lallai sai ta kawar da tunanin da ya kawo mata ziyara ta tashi ta fita daga d'akin gabad'aya gudun ma kar tayi tunanin sa.

Washe gari da yantsi Rauda ta shirya ta tafi gidan Baba Malam dan karb'o sak'on Ramla da kuma nata, kamar ko yaushe layi kamar babu gobe ta wuce zuwa cikin gidan mutane sai kallon ta suke wanda suka ganta jiya sun gane ta wasu kuma a ranar suka zo bata jima sosai ba aka sake ganin ta fito da leda a hannun ta alamun ta karb'i sak'on ta.

Kusa da wata mota tazo wucewa sai ta wayar ta tayi k'ara ta d'auka ta tsaya a jikin tagar motar ta baya ta saka a kunne tare da fadin, "Kin kira a daidai Sis yanzun nan kinga sak'on a hannuna na karb'o miki." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin tayi dariya tace, "Har na ganshi tuni ma, layi kam akwai shi har yafi na jiya ma wallahi."

"Eh to mu had'u a gida sai ki karb'a" tana fad'a ta kashe wayar ta cigaba da tafiya. Mama da take zaune a mota ita da Suhaima ta kalli Suhaima tace, "Ita wacece yarinyar nan da naga jiya tazo bata jima ba ta tafi yanzu ma haka?." Suhaima ta kalli bayan Rauda tace, "Wataƙila ta san shine shiyasa." Mama ta kalle ta daidai lokacin da ta samu keke napep tace, "bita Suhaima muje ko wani abun ne a biyata ta kawo mu na gaji da dogon layin nan" ta fad'a tana dafe kanta domin ita kam bata saba bin layi ba.
Chapter 68 · 0% Book details