Sashe 63
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama ta saki kanta ta kalle ta tace, "tun jiya nake kiran ki baki d'auka ba kuma baki kira ni ba." Mum tace, "Shiyasa nace tuba nake ranki ya dad'e." Mama ta kalli Suhaima tace, "Jeki." Ba musu ta tashi ta basu waje Mama ta kalli Mum tace, "akwai abinda yake faruwa a gidan nan kin sani?."
Mum da alamun mamaki tace, "kamar me kenan ranki ya dad'e?." Mama tayi tari kad'an kana tace, "Ki fad'a min gaskiya mai kuka yiwa Asad keda y'ar ki Jidda?." Mum ta zaro idanu tare da dafe k'irji tace, "kamar ya me muka yi masa ranki ya dad'e? Me kuwa muka yi masa?." Mama ta jingina da kujera tace, "Don't pretend like baki san komai baSadiya, kin san abinda nake nufi. Wanne malami kika samu ya mallake min d'ana haka?."
Mum ta rausayar da kai tace, "Haba ranki ya dad'e wanne irin mallaka ana zaune lafiya? Ni ban yiwa Asad komai ba." Mama tayi mata kallon kin raina min hankali sannan tace, "Sadiya kin san karrr nake kallon ki, ki fito ki fad'a min abinda kika yiwa Asad tun muna shaida juna nida ke."
Mum tayi murmushi ta gyara zama tace, "Irin malaman da kika samu suka mallake miki mijin ki da kuma y'ay'an ki, irin malaman da kika samu suka mayar da mijin ki tamkar gawa, irin malaman da kika samu aka mayar dake tauraruwa a wajan mijin ki wajan su nima naje." Gaban Mama yayi mugun fad'uwa tabi Mum da kallon mamaki tace, "Sadiya! Me kike cewa ne?."
Mum tayi dariya ta tashi daga kan carpet ta dawo kan kujera ta d'ora k'afa kan d'aya tana kad'awa tace, "Abinda kika ji shi nace. An fad'a miki zan bar Jidda ta shigo gidan nan ba tare da na shirya ba duk da nasan halin ki? Kar ki manta nice fa Sadiya wacce kike fad'awa zaki mallake masarautar nan ko shi sarkin sai abinda kika ce masa, to kin fad'a min wannan ni da yake doluwa ce mara wayo sai na zuba idanu y'ata ta zama bora duk da kasancewar ta matar sarki?. Keda kike uwar sa ace kece zaki san komai kafin ita? Impossible kema kin san bazai yuwa ba ai Rabi" ta fad'a cikin murmushi tana kallon Mama.
Mama ta kasa magana sai kallo da take binta dashi cikin tashin hankalim da ya bayyana a tare da ita tace, "Sadiya....!." Tayi farr da ido tace, "Na'am Rabi'atu. Kinyi saurin karaya bayan yanzu aka fara wasan ai, yadda kike tunanin mallake komai ni sai na riga ki mallakar sa, yadda kike juya kowa nima sai y'ata ta juya ki kina ji kina gani d'anki sai yafi k'arfin ganin ki."
Mama binta take kawai da kallo cikin mamaki ta kasa cewa komai dan gani take kamar ba ita ba Mum ganin hakan ya saka tace, "kina ta kallona kamar baki san komai ba, tunanin ki kin amince min na butulce miki ko...? Hhhhhhh Rabi'atu kenan. Kin manta kema mijin ki ya amince miki kuma kika butulce masa har kika kai shi ga kwanciya dashi da gawa banbancin su kawai numfashi ne?. Yanzu aka fara wasan Rabi'atu burin ki na zama cikakkiyar mai iko nima shine burina, y'ata ta zama sama da komai da kowa a gidan nan kuma hakan zata kasance" ta fad'a tana mik'ewa tana kallon Mama.
Mama ta kasa magana sai kallonta kawai da take yi baki a bud'e zuciyar ta na bugawa da gudu sabida tashin hankali kanta har rawa take ji yana yi sabida yadda yake mata mugun ciwo, Mum ta kalle ta tace, "na barki lafiya babar sarki kuma sirikar Jidda, kin kusa yin jika ma domin sirikar ki Jidda tana da juna biyu kin san kin samarwa mijinta maganin da ya samu lafiya yadda zai kasance da matar sa yadda ya kamata dan baki so tayi kuka. Magani yayi aiki kam domin zancen da akeyi yanzu har anyi ciki. Na barki lafiya Rabi na gode da kika yi iya k'okarin ki wajan ganin Jidda ta shigo gidan nan matsayin mata kuma matsayin sirikar ki, sauran aikin nawa ne" tana fad'a ta fita ta bar Mama a zaune kamar an dasa ta a wajan.
Mama kawai ganin ta tayi a d'aki ba tare da tasan lokacin da taje ba ta zube a kan tiles kawai taji idanun ta na zubar da hawayen bak'in ciki wanda bata shirya musu ba. Tunanin fa daman haka duniya take wanda ka amincewa shine yake k'ok'arin ganin ya cutar dakai....? Me ta yiwa Sadiya haka da ta yanke mata wannan d'anyen hukuncin lokaci d'aya haka. Kuka take yi sosai iyakar iyawar ta kafin wani lokaci zazzaɓi ya rufe ta ruf ga ciwon kai mai zafi da suka tarar mata.
Suhaima ce ta shigo ganin halin da take ciki bata yi k'asa a guiwa ba ta kira likita ba jimawa ya k'araso aka yi mata allura aka saka mata ruwa nan da nan bacci ya kwashe ta Suhaima na kusa da ita haka Hydar ma. Bayan tayi bacci likitan ya fita Hydar ya kalle Suhaima yace, "Meya same ta ne lokaci d'aya haka?." Suhaima tace, "Wallahi a nan kawai nazo na ganta a kwance a kan tiles, nasan dai na bar su tare da Mum ban san lokacin da Mum d'in ta tafi ba."
Hydar ya girgiza kai yace, "duk yadda akayi ciwon nata yana da alaqa da zuwan Mum, ki kula da ita ina zuwa" yana fad'a ya fita daga d'akin.
Mama bata farka ba sai bayan sallar la'asar ta tashi dak'yar har lokacin kanta yana ciwo ta shiga band'aki tayi alwala ta fito tayi sallah bayan ta idar karo na farko cikin addu'ar da take yi taji bakin ta yana furta, "Allah ka bawa mijina lafiya, Allah ka tashi k'afadun sa shine kad'ai zaiyi iya maganin Jidda da babarta, Allah ka dube ni ka fitar dani daga halin da nake ciki" ta fad'a tana kuka sosai ta shafa addu'ar ta tashi da hijjabi a jikinta duk da kanta da yake ciwo hakan bai hanata nufar b'angaren mijin ta ba.
Babu wanda baiyi mamakin ganin ta a b'angaren mai martaba ba dan tunda ya dawo sau d'aya tak taje inda yake amma sai gata da yamma ta shiga ta samu Hydar da Uncle da sauran y'an uwan Abba su uku a ciki, ganinta ya saka suka fita aka barta daga ita sai shi idanun sa a bud'e alamun ba bacci yake ba ta k'arasa kujerar kusa dashi ta zauna ta rik'e hannun sa hawaye yana sakko mata tace, "Mijina sun raba ni da Asad d'ina, sun juyar masa da hankali daga gare ni Sadiya ta cuce ni ita da y'arta. Mamaki nake wai da gaske ne abinda yake faruwa ko mafarki nake? Yau nice aka mallake min yaron dana fi cin buri a kansa?."
Bai motsa ba sai kallonta da yake yi hakan ya saka tace, "Kaina ya kulle na rasa me zanyi ka taimake ni mijina kar kwakwalwa ta ta fashe. Daga jiya zuwa yau na shiga tashin hankali mara iyaka dan Allah ka taimake ni. Allah ya baka lafiya da gaggawa ka taimakawa d'ana ya dawo hankalin sa zasu iya yin komai ganin sun raba shi da duniyar gabad'aya." Kuka take yi sosai a kan hannun sa hawayen ta na tab'a fatar sa sai da tayi mai isar ta sannan ta kalle shi tace, "zan fara nema masa magani ka taya ni fatan Allah yasa na dace."
Ta jima tana kuka kafin ta saki hannun sa ta goge idanun ta ta fita jikinta a sanyaye ta koma b'angaren ta. Da Suhaima suka had'u da Hydar Suhaima tace, "Mama sannu." Kallon ta tayi tace, "Ina key d'in motar ki?." Suhaima tace, "yana d'aki."
"D'auko ki kaini unguwa."
Hydar yace, "Mama ina zaki je baki da lafiya fa?."
"Yanzu zamu dawo Hydar" ta fad'a dafe kanta da har lokacin yake ciwo.
Hydar yace, "to muje na kai ki." Mama tace, "Zamu je da Suhaima" tana fad'a Suhaima ta fito suka fita a babban falo hadiman ta zasu bita ta girgiza musu kai alamun su sha zaman su, ko jakadiya bata d'auka ba ita da Suhaima suka hau mota suka bar gida.
Sunyi tafiya mai nisa suka isa gidan malamin Mama ta bata umarnin ta tsaya ta fita ta shiga ciki tace ta jira ta a ciki, da jama'a sosai ta samu a gidan amma sanin ita wacece yana sallamar ta gaban sa ta shiga ya mik'e yana kawo gaisuwa, zama tayi ta kalle shi tace, "Ya jama'a?."
"Alhamdulillah ranki ya dad'e."
Ta sauke numfashi tace, "babar matsala ce ta kawo ni Malam." Ya gyara zmaa yace, "To ina sauraren ki."
Ta sauke numfashi tace, "dakai na amince nasan baka fitar min da sirrina kana kuma k'okari wajan yi min duk abinda nace ina so. Sadiya wacce muke zuwa tare ta butulce min sun juyarwa da mai martaba kansa gabad'aya baya jin maganar kowa sai tata data matar sa." Malam yace, "Ashsha! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, amma Sadiya tayi butulci ba kad'an ba. Tazo min da maganar kwanaki na amsa mata zanyi amma banyi ba sabida bazan iya cin amanar ki ba."
Mama tace, "Meyasa a lokacin baka sanar dani ba?."
"Kiyi hak'uri ranki ya dad'e naso fad'a miki sai kuma nayi tunanin kar na raba zumuncin ku."
"Yanzu gashi ai komai ya lalace" ta fad'a tana dafe kanta shi kuma ya shiga duba mata abinda yake faruwa. ya jima yana yi kafin ya girgiza kai yace, "Tsakani da Allah ranki ya dad'e bak'in tsafi aka yiwa Mai martaba ba asiri ba, an bashi yaci ya kuma sha anyi amfani da makusantan sa anyi abin cikin sirri ba tare da ya sani. Hak'ik'a tsafin da yake jikin sa ba k'arami bane ba dan zan iya cewa ba'a k'asar nan akayi shi ba."