← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 131

Sashe 65

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yana k'ofar gida bai shigo ba." Rauda tace, "meyasa ya tsaya a waje?, Khalil!" Ta fad'a da d'an k'arfi Khalil yazo a kuje tace, "maza jeka kace wanda yake waje ya shigo." Ya kuwa fita a guje Rauda ta zauna suna cigaba da gaisawa da Ramla cikin fara'a. Ba jimawa ya suka shigo Rauda tace, "Yanzu dan Allah Dr sai ka zauna a waje?." Murmushi yayi ya zauna tace, "Ina wuni."

"Lafiya lau Rauda, ya mutanen gidan kowa lafiya?." Rauda tace, "Suna nan lafiya. Khalil yiwa Baba magana yace in kunzo a sanar dashi zuwan ku bara na kira Umma" ta fad'a tana tashi ta shiga d'aki jim kad'an suka fito tare da Umma.

Cikin girmamawa suka gaisa da Umma Baba ma ya shigo har da Inna suka gaisa cikin girmama juna kamar sun san su Baba yace, "Ta sanar damu duka taimakon da kukayi mata angode Allah yasa da alkhairi ya bar zumunci." Dr Khalifa yace, "babu komai ai yiwa kaine." Umma tace, "Ko ruwa baki kawo musu ba Rauda." Da sauri ta mik'e tama fad'in, "Murnar ganin Anty Ramla ce." ta kawo ruwa tare da abinda ta dafa musu lokacin da ta dawo su Umma basa nan.

Dr Khalifa yace, "Su Umma suna da kirki sosai har sun fiki." Tayi dariya tana fad'in, "Musamman na dafa musu abincin nan Allah yasa kuna ci" ta fad'a tana bud'ewa Ramla tace, "kaii ai ko a k'oshe nake sai naci, favorite food d'ina ne fa" ta fad'a tana gyara zama Rauda taji dad'i ta fara serving d'in su ta basu ta zauna suna hira suna ci da alama kuma sunji dad'in sa.

Bayan sun gama Dr yace, "Gaskiya kin samu lada Rauda, na jima banci d'anwake ba sai yau gashi yayi dad'i sosai da alama Umma ce tayi." Dariya ta kuma tace, "Nima naji dad'i da kuka ci wallahi." Ya kalli Ramla yace, "ya kamata muje magriba tayi" ya fad'a yana duba agogon hannun sa. Ramla ta kalli Rauda tace, "Yauwa Rauda, kin sani Baba Malam wani babban malami ance ya tsufa a garin nan yake amma bamu san wacce unguwa ba."

Rauda da mamaki tace, "Baba Malam dai tsohon malamin nan da ake masa layi?." Ramla tace, "Shifa."
"To ai Yayan Ummana ne, shine babba a d'akin su gobe ma naji tana cewa zata je wajan sa." Ramla ta kalli Khalifa da farin ciki a akan fuskarta tace, "Alhamdulillah, kice ta kwana gidan sauk'i ma kenan." Rauda tace, "ta kwana kam, ganin sa zakuyi?."
"Eh Rauda."
"Tabd'ijam ai kafin ku samu ku ganshi wallahi a kwana goma layi baizo kanku ba, amma yanzu tunda da Umma zai iya cewa goben ma kuzo tare da kunje kuma cikin gida zaku shiga zaizo da kansa inda kuke."

Ramla ta rik'e hannun Rauda cikin farin ciki tace, "Na dad'e banji labari mai dad'i ba kamar yau Rauda, yanzu yaushe zamu ganshi?." Rauda tace, "Umma zata yi masa waya ta fad'a masa zai baku rana sai aje nasan in akace masa ba'a nan kuke ba zai bada ranar kusa."
"Na gode Rauda Allah ya bar zumunci, kinga dad'in zumunci ko? Ta dalilin ziyarar da nazo miki ga abinda ya faru."

Rauda tace, "Lah babu komai Anty Ramla kun wuce haka wallahi." Dr yace, "mun gode sosai Rauda, naji dad'i sosai wallahi." Rauda tace, "babu komai, yadda mukayi da ita anjima zan fad'a miki ko a chart." Daga nan sukayi sallama da Umma da Baba Rauda ta raka su k'ofar gida a nan Khalifa yake cewa, "Rauda ina Asad kuwa?."

Gabanta ya fad'i matuk'a amma bata nuna ba tace, "Yana gidan su." Yace, "kwanaki munyi waya dashi, yanzu samun sa a waya sai kayi da gaske abubuwa sun masa yawa, ya zama shugaban katagum baki d'aya jan aji ya k'aru. " Shiru tayi bata bashi amsa ba ya d'an kalle ta sai yayi murmushi Ramla tace, "Sai munyi waya Sis. Ga wannan tsaraba tace" ta fad'a tana d'auko leda a mota, Rauda tayi musu godiya daga nan suka ja suka tafi itama ta koma gida.

       Rauda tana shiga gida ta tarar da Umma da Ummulkhairi da Rahma a zaune su Rahma suna cinye ragowar d'anwaken ta kalle su tace, "Ku kam kuna da abin haushi, yanzu da zanci fa kuka cinye?." Umma tace, "Sai dai kiyi hak'uri ai." Ta k'arasa ta nunawa Umma k'aramar ledar tace, "Umma kinga abinda suka bani wai tsarabar Egypt."

Umma tace, "kin gode, suna da kirki sosai kamar mun saba." Rauda tace, "mun saba sosai a waya Umma tunda na dawo ai ban yarda dasu ba muna zmuncin sosai. Kuma kin san wa suke son gani?." Umma ta girgiza kai alamun A'a Rauda tace, "Baba Malam suke nema an musu kwatancen sa basu san inda zasu ganshi ba." Umma tace, "Baba malam dai Yayana?."
"Shifa Umma."
"Allah sarki, sai nayi masa magana sai ya basu lokacin da zasu ganshi, sun huta bin dogon layi."
"Haka nace musu, sai godiya suke yi."
Umma tace, "Babu komai ai."

Rauda ta kalli Falon ganin duk sun fita sai su biyu tace, "Kin san basu da yara kusan shekara bakwai da auren su bata tab'a samun ciki ba, har cewa tayi nayi mata addu'a ina jin matsalar ce zata kai su wajan sa." Umma tace, "Allah Akbar! Kice gwara da Allah ya hane ni d'azu k'iris nace musu ina yaran."
"Wallahi fa Umma."
"To in ma itace matsalar da zata kaisu Allah ya basu na gari in suna da rabon haihuwar."

"Amin Umma" Rauda ta amsa Umma ta kuma cewa, "zan masa waya gobe in Allah ya kaimu yadda mukayi dashi sai na fad'a miki ki sanar dasu." Rauda tace, "To Umma." Rauda ta tashi ta shiga d'aki.

*☆☆☆*

          K'arfe sha d'aya na safe a garin Kano ta yiwa Mama ko gidan sarki ma bata je ba gidan yayar ta ta wuce kai tsaye tana zuwa bata zauna zaman hutu ba suka d'auki mota suka d'auki hanyar k'auyen kura. Isarsu kura ba wuya suka tsaya a k'ofar wani gidan k'asa da motoci manya a k'ofar gidan mata da maza suna ta shiga da fita suma suka fito suka shiga ciki.

Basu jima da zama sosai ba aka kira su suka shiga wajan malamin yana ganin su yayi murmushi yana fad'in, "Barkan ku da zuwa." Zama sukayi kafin Babbar Yaya tace, "mun same ka lafiya malam?."
"Lafiya lau ranki ya dad'e."
Ta nuna masa Mama tace, "itace wacce na sanar dakai zuwan ta jiya, mahaifiyar sarkin katagum sarki Asad Nasir Sa'ad."

Ya sake yi mata jinjina yace, "An gaida y'ar sarki mahaifiya ga shugaban Katagum." Babbar Yaya ta kuma cewa, "Zancen mai martaba Asad d'in ne d'anta gabad'aya an mallake mata shi yanzu ko inda take baya zuwa bayan da yana da tsananin biyayya a gare ta." Malamin ya fara istihara yana duba lamarin kafin ya kalle su yace, "Tsakani da Allah na jima banga bak'in aiki kamar wanda aka yi masa ba, wannan sai dai a kira shi da tsafi ma ba sihiri ba."

Mama suka kalli juna hankalin ta ya tashi jin abinda akace mata a can an kuma maimaita mata Mama tace, "Karya shi nake so ayi da gaggawa." Ya sake yin shiru yana istihara kafin yace, "Karya shi ba abu bane mai sauk'i dole sai anyi da gasken gaske sannan za'a iya karya shi kuma dole sai an raba shi da matar sa sannan za'a samu abin yayi nasara, Matuk'ar suna tare bazata barshi shan duk wani magani da aka bashi ba." Mama ta gyara zama tace, "Wannan ba matsala bane zan saka shi ya sake ta koda baya so, duk da shugaba ne Bai kamata ace yayi saki ba amma dole yayi." Babar yaya ta kalle ta tace, "Kina ganin zai amince ya sake ta cikin sauk'i?." Mama ta kalle ta tace, "Zai yu."

Malam yace, "Indai zai yu zan bada maganin da za'a bashi ya dinga wanka dashi, sannan akwai rubutun da zan bayar ya zama kamar ruwan shan sa koda yaushe ya dinga sha. Sannan akwai wani babban malami a can garin naku Allah ya bashi ilimin maganin gargajiya sannan yasan ayoyin alkur'ani yana karya tsafi komai munin sa indai Allah ya bashi iko." Mama tace, "waye shi? A ina yake?." Malamin yace, "A nan katagum d'in yake ana ce masa Baba Malam ya tsufa amma kuma akwai ilimi ba kad'an ba."

Mama tace, "Wacce unguwa yake?." Malamin yace, "a nan gaban katsalle yake ni kaina in abu ya shige min duhu ina zuwa wajan sai kiga an samu nasara." Mama tace, "Zanje wajan sa da zarar na koma, yanzu bamu naka taimakon."

Malamin ya juya yana had'o mata maganin kafkn yace, "Amma fa ganin sa yana da wahala sosai sai ka jera kwana goma layi bai zo kanka ba sai an jure. Baya duba mulki ko kud'i gaskiya in layi bai zo kanka ba bazai ganka ba." Mama taja k'aramin tsaki domin ita kam a ganinta babu wani wanda bai mata wahalar gani tana da kud'i da mulki kome take so zatayi.

Maganin ya basu suka zube masa kud'i suka koma gidan Baban Yaya sai a sannan Mama ta samu ta huta ga zazzaɓin da yake cin jikinta sai da tasha magani sannan tayi bacci.

Washe gari ta sauke d'aukar hanyar Katagum da sassafe, kafin rana tayi ta isa katagum tana takawa a hankali tana shiga cikin gidan tazo giftawa ta wani d'an lungu da ake aikin abinci a wajan taji hadimai mata d'aya tana cewa, "Bikin yarinyata yazo amma ban san da wacce fuska zan tunkari Mai martaba da maganar nan ba, ya canja gabad'aya ni tsoro ma yake bani shiyasa na yanke shawarar samun Fulani mai babban d'aki da maganar."

D'ayar tace, "Me ta isa tayi a yanzu? Hmmm ai dama matar tasa kika samu Zakanyar Sarki in ta saka baki sai kiga yayi miki." D'ayar ta kuma cewa, "Allah mai iko, yanzu wai mai martaba ne baya zuwa inda Fulani take? Lallai duniya juyi-juyi. Amma fa maganin ta kenan kodan wulaƙanta mu d'in da take yi alhaki sai ya kamata." Da sassarfa Mama ta wuce wajan zuciyar ta na suya zazzaɓi na sake rufe ta ruf haka ta isa b'angaren ta.
Chapter 65 · 0% Book details