Sashe 53
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba ya zauna a akan kujera kana yace, "Eh kuma fa gaskiyar kine, amma ai nan gidan sirikan sane ba wani abun zamu bashi da zai cutar dashi ba." Umma tace, "Kaine kake ganin hakan."
"Amma yanzu haka zai zo babu abinda zamu bashi?."
"Sai a d'ora ai Malam" ta fad'a tana kawar da kanta gefe ba tare da tace komai ba.
"To ki tashi kije ki shirya sai wani sanyin jiki kike yi kamar ba mijin ki ne zai zo ba" Ya fad'a yana kallon Rauda bata musa ba ta tashi ta shiga d'aki shima ya fita Umma ta bishi da kallon mamaki, wato shidai duk inda akace kud'i a nan jikin sa yake rawa.
Rauda koda ta shiga d'akin bata iya aikata komai ba tsayawa tayi tana tunani kafin ta samu waje ta zauna ta rafka uban tagumi zuciyar ta na harbawa dan bata san me zai kawo Asad d'in gidan su ba. Sallah ce kawai take tashin ta a nan take zaune har akayi magariba babu Asad babu labarin sa har lokacin Baba bai sare da zuwan Asad ba ita kam daman tasan bazai zo ba.
Wanka tayi lokacin ana kiran sallar i'sha ta fito ta saka doguwar riga ta bacci mai gajeren hannu jikinta yana rawa sosai kalar ja da bak'a ta saka hula ta d'ora hijjabi ta tayar da sallah. Bayan ta idar tayi shafa'i da wutri ta mik'e ta zare hijjabin kenan Baba ya shigo jikin sa har rawa yake yana cewa, "Ke Rauda yi maza-maza kije ga Asad d'in can yazo yana sitirum d'ina na waje." Gabanta yayi mugun fad'uwa ta dafe k'irji sabida yadda zuciyar ta ta buga fattt ji tayi kamar zata fito.
"Ba magana nake miki bane kin tsaya kina kallona? Dallah malama kiyi da jiki kije yana jiran ki an gaisa dashi ke kad'ai ake jira" Baba ya fad'a cikin fad'a hakan ya dawo da ita hankalin ta ta d'auki hijjabin data cire ta saka tana kallon Baba ta fita. A falo ta tarar da Umma ta wuce ta jikinta duk a mace gabanta yana cigaba da tsantanta bugawa haka ta wuce ta fita daga falon ta fito tsakar gida ta fita harabar gidan a nan ne set room d'in Baba yake.
Tare da Baba suka fita ya tsaya a bakin k'ofa yace, "Shiga." Yawu ta had'd'iye ta saka kanta cikin falon nan take khamshin turaren sa ya bata tabbacin shid'in ne da gaske ba wasa bane. Kanta a k'asa take takawa jikinta yana rawa ta zauna a kan carpet har lokacin bata kalli inda yake ba gabad'aya tsoro ya gama mamaye mata zuciya.
Tunda ta shigo yake kallonta k'irjin sa yana bugawa da sauri-sauri ya runtse idanun sa ya bud'e yana jin wani iri a zuciyar sa, shiru falon yayi babu mai magana tsabar bugawar da k'irjin ta yake yi ta kasa magana sai raba idanu da take a k'asa tana kallon k'afar sa da take sanye da takalmi ta mayar da kanta k'asa ba tare da tayi magana ba.
Yadda tayi shiru haka yayi shiru baice komai ba kallonta kawai yake yi ta k'asan idanun sa domin tasan dai bazai mata magana ba sai dai in a kwana a haka.
Gajiya tayi da zaman ga bugun da zuciyarta take yi ta yunk'ura ta tashi zata fita taji an rik'o hannun ta zuciyar ta ta cigaba da gudu ta runtse idanunta hawaye na ciko mata idanun ta, kwace hannun ta tayi daga rik'on da yayi mata sai a sannan tace, "Meya kawo ka gidan mu?."
Hannayen sa duka biyun ya saka ya juyo da kafad'ar ta kanta na k'asa hawaye suna sauka daga idanunta ya d'ago fuskar ta suka had'a ido sa a sannan ta kalli fuskar sa ta ganshi sanye da face mask da kuma bak'in glass da alama yayi b'adda kama ya saka hannu ya zare glass d'in ya cire face mask d'in fuskar sa ta bayyana sosai ya lumshe idanun sa ya bud'e yana kallon fuskar ta da idanun ta suke zubar da hawaye har lokacin.
"Na mayar dake d'akin ki Muwaddaty! You're still my wife!" Ya fad'a a sanyaye yana bin fuskar ta da kallo yana so ya fahimci reaction d'inta. Wara idanun ta waje tayi cikin tsananin bugun zuciya tana k'arewa fuskar sa kallo ya d'aga mata kai alamun tabbacin abinda yace ya jawota ya had'a ta da jikinsa hannun sa na zagaye da k'ugun ta yace, "Yeah, you're still my wife!."
*Tofa anya Asad yana cikin hankalin sa kuwa?*😱🏃🏼♀️
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*052.*
Yanayin yadda yaga ta gigice ta zuba masa ido fuskar ta ta nuna tsantsar tashin hankali da mamaki had'i da al'ajabi a kai k'arara sai zare idanu take tana binsa da kallon da alama mamaki ya hana ta magana. Shima baiyi magana ba yana rik'e da ita har lokacin ganin kamar bata hankalin ta ya saka shi ya rik'e hannunta guda d'aya ya murza yatsun hannunta ta kalli yatsun nata ta sake kallon sa tana bin hannun nasa da kallo nan tayi karo da abinda take nema a hannun nasa ta sake kallon fuskar sa dan ta tabbatar shi d'in ne.
"Nine a gaban ki kar kiyi tunanin wani abun daban" ya fad'a cikin maganar sa mai d'aukar hankali yana cigaba da kallonta. Sakin ta yayi ya kalle ta yace, "where is your phone?." Bata iya magana ba sai bin sa take da ido gani take kamar baya cikin hankalin sa in ta tuna yadda aka rabu bata d'auka zai dawo har yace ya mayar da ita ba.
"Kin san yanayina bazan iya magana da yawa ba, amma I'm sorry." Wani irin abu take ji yana tasowa daga jikinta ta lumshe ido dan ji take yana tafiya kamar kiyashi yana zaga ko wanne b'angare na jikinta har cikin gashin kanta take jin maganar sa.
Sake rik'e hannunta yayi duka biyun yace, "kace mace ta biyu a duniya dana bawa hak'uri because nasan na cutar dake, forgive me please." Numfashi ta sauke a hankali sai taga ya saki hannun ta ya juya gefen sa ya d'auki wata k'aramar leda ya ajjiye mata yace, "Is for u."
Dafe kai taga yayi ya zauna yana runtse idanu alamun maganar da yayi da yana tana affecting d'insa ya lumshe idanu yana sauke ajiyar zuciya. A nan ta tabbatar Asad ne domin kuwa yadda yake yatsine fuska da zanen hannun sa da yadda yake magana ya tabbatar mata shine, babar shaidar ma itace zanen hannun sa. "Na sake ki saki biyu!." Abinda taji ya furta kenan ta sake kallon sa a gigice taga ya mik'e tsaye yana mayar da abubuwan da suka hana fitowar fuskar sa gabad'aya yace,
"Na yiwa Mama alqawarin zan rabu dake gabad'aya har abada that's why na yanke duka igiyoyin aurena a kanki. Ki yafe min banyi dan na cutar dake ba sai dan na barki ki huta ki auri wanda kike so yake sonki. Ina sonki har gobe amma nafi son Mama akan komai, kiyi haƙuri" yana fad'a yana gifta ta zai wuce k'unar zuciyar ta na k'aruwa tayi sufa ta sha gabansa tana binsa da banzan kallo cikin tsanar data mayaye mata zuciya lokaci d'aya tace,
"K'arya kake wannan ba alqawarin da ka yiwa Maman ka bane iya ita kad'ai harda zuciyar ka, na dad'e da sanin wannan ranar zata zo a cikin rayuwata, na jima da sanin za'a zo wannan gab'ar da saka wulaƙanta ni dan na kasance kaskantacciya a wajan ka."
"Kayi abinda kake so ka mayar dani bazawara da k'aracin shekaruna, kasan babar ka bata sona meyasa ka aure ni? Kasan Babar ka bata sona meyasa ka b'ata min k'uruciya ta?." Kallonta yayi yace, "Ba'a san shugaba da sakin aure ba a wata masarautar an haramta hakan amma ya zama dole a wajena shine kwanciyar hankalina da naki."
"K'arya ne wallahi, burin kane kawai kuma ka cika sai kaje ka k'arata daman Allah ya sani tun farko ba son auren ka nake ba k'addara ce ta had'a kuma ta raba, ban damu da kai waye ba amma ina so ka sani sai Allah ya saka min." Runtse ido yayi ya kalle ta ganin kamar an canja ta kamar zaiyi magana sai ya fasa ya cize bakin sa ya fita daga falon zuciyar sa na zafi shi kansa inda tasan abinda yake ji baza tayi masa wannan zargin ba, amma ya zaiyi umarnin zuciyar sa kawai yake bi maganar da yayi mata ma ya daure ne amma bala'in haushin ta yake ji.
Zubewa tayi a wajan tana kuka sosai zuciyar ta nayi mata ciwo ranta na suya haka take zubar da hawaye masu zafi, ta jima a wajan bata san adadin lokacin data d'auka a wajan ba taji an dafata ta baya, bata d'ago ba bata daina kukan ba kuma sai da taji muryar Baba yana cewa, "ke kuma lafiya kike yiwa mutane kuka? Ina mai martaban yaje?." Ta sake k'ara kaimi wajan kukan ta sai a sannan take ji a zuciyar ta komai ya faru da ita Baba ne silar komai da bai bada auren ta babu sanin ta ba da duk hakan bata faru ba.
Umma tace, "tashi muje d'aki ki daina wannan kukan." Umma ta d'aga ta ta jinginar da kanta a kafad'ar Umma suka fita Baba yaga ledar da aka ajjiye ya d'auka yabi bayan su jikin sa na rawa tsoro duk ya dabaibaye masa zuciyar sa.
A falon Umma ya tarar dasu a zaune daga ita sai Umma tana ta kuka har lokacin Baba ya zauna kusa da ita yace, "meya faru ne wai?." Cikin kuka gabanta yana fad'uwa tace, "Baba tun a Egypt ya sake ni saki d'aya, yanzu kuma......" Sai kuma ta kasa k'arasawa ta sake fashewa da sabon kuka. Murmushi Umma tayi tace, "Daman nasan za'a rina ai, yanzu da yazo ya k'arshe guda biyun ko?." Rauda ta d'aga kai alamun eh tana sake cigaba da kukan ta.
Baba cikin tashin hankali yace, "ban fahimta ba, mayar dake yayi sannan ya kuma sakin ki?." Kai ta d'aga alamun eh tana jikin Umma tana kuka tare da jan numfashi Umma tace, "Shine ya had'o ki da kud'i a jaka da yake ga kwad'ayayyiya wacce take neman kud'in hannun sa ko?."