← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 131

Sashe 125

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baza kisha tea ba?." Ta kalli abincin tace, "Wannan kawai nake so naci." Baiyi musu ba ya ware spoon din da yake nannad'e a tissue ya fara bata tana ci sai yaga ta tsaya kuma tana kallon sa tana yamutsa fuska, da ido yayi mata alama da ya dai sai ta mik'e daga jikin sa tayi wajan sink a guje ta fara shara amai.

A hankalin sa ya tashi sosai ya k'araso inda take ya rik'e ta har ta gama aman ta d'ago ta dafe kai ya rik'o ta suka dawo ta zauna tace, "Abincin babu dad'i." Asad ya bita da kallon tausayi yace, "Sannu." Ta kwanta a jikin sa tace, "Ina jin yunwa Sultan amma bana son duka wannan abincin."

"Me kike so?."
"Farfesun dankali da hanta." Waya ya d'auka zai kira Suhail ta rik'e wayar tace, "Ni kai nake so ka dafa min." Wara ido yayi yace, "Muwaddaty babu komai na girki a nan taya zan iya miki abinda kika ce?." Kawai sai ta fashe da kuka tana fad'in, "ni shi nake son ci in banci ba zan iya mutuwa" ta fad'a tana dukan k'irjin sa tana kuka.

"Oh my god!" Ya furta a bayyane kafin yace, "Is okay!." Suhail d'in ya kira daga can b'angaren yace, "Allah ya taimake ka."
"Suhail potatoes nake so." Suhail mamaki ya kama shi yace, "Ranka ya dad'e akwai dankali a abincin dana kawowa mai martaba." Asad yaja tsaki ya kashe wayar ya rubuta masa text dan ya fahimci baya ganewa.

Kuka take yi har lokacin yace, "Ya isa mana Muwaddaty yanzu Suhail zai kawo." Tace, "Ni kai nake so ka dafa min." Kai ya d'aga yana jiran kiran wayar Suhail. Tsaki yaja ganin mintina biyar Suhail baizo ba ya tashi ya kwantar da ita yace, "Ina tare da Suhail kar ki fito" yana fad'a yayi gaba da sauri.

A falon suka had'u da Suhail ya shigo yaja tsaki yana kallon Suhail yace, "Tuba nake ranka ya dad'e,  akwai abinda ya bani wahalar nema shiyasa." Kitchen ya wuce dole Suhail yabi bayan sa ya same shi ya hard'e hannu a k'irji Suhail ya ajjiye kayan yana kallon sa amma baiyi magana ba.

"Ranka ya dad'e akwai abinda ake so?." Asad ya kawar da kai ya dawo da kallon sa ga Suhail yace, "Dafa min zakayi." Suhail ya kalli dankalin da yake a leda yace, "An gama. Soyawa za'ayi ko farfesun sa za'ayi?."
"Na k'arshen" ya fad'a yana kallon sa Suhail yace yanzu za'ayi a gama.

Suhail ya d'auko wuk'a yana feraye dankalin Asad yana tsaye yana kallon sa ganin yana yi a hankali, wayar sa da take hannun sa yaji tana k'ara yaga sunan ta ya dafe kai yace, "Oh Muwaddaty! Suhail kayi sauri mana tana jin yunwa babu abinda taci fa" ya fad'a ba tare da ya d'auka ba ya ajjiye wayar ya d'auki wuk'a shima yana yin yadda yaga Suhail d'in yanayi.

Suhail dariya yake b'oyewa  ya yanka dankalin ya d'auko kayan miya daman a markad'en su suke ya d'auki tukunya ya d'ora akan gas ya kunna nan da nan ya fara had'a mata abinda take so. Asad yana tsaye yana kallon sa ya k'agu a gama ya kai mata ya kalli Suhail yace, "I'm coming" ya fad'a yana ficewa Suhail ya kyalkyale fa dariya harda rik'e ciki.

Ya jima yana dariya sosai domin yadda Asad din ya rud'e shine abinda ya bashi dariya yagirgiza kai yace, "Lallai a gaida mace, yanzu badan ni ba ko taya zai iya girki oho, nidai nasan babu abinda ya iya sai had'a coffee shima bai jima da iyawa ba da muna makaranta sai dai a dafa a bashi." Motsin sa yaji a bayan sa hakan ya saka shi yin shiru Asad ya k'araso yana kallon tukunyar Suhail yana juyawa.

D'an tsaki Asad yayi yana kallon sa yace, "in banda dole ina ita ina cin abincin wannan." Suhail ya sake fashewa da dariya kafin yace, "Afuwan ranka ya dad'e an kusa gamawa."

Yana nan tsaye Suhail ya gama ya d'auko bowl ya zuba a ciki ya saka spoon yace, "An gama ranka ya dad'e." Asad ya karb'a yace, "Allah yasa da dad'i, jira ni" ya fad'a yana sake fita Suhail yayi murmushi yana cin wanda ya rage dan sosai girkin nasa yayi masa dad'i.

Tana kwance ya kai mata ta tashi zaune ta karb'a tana murmushi tace, "Na gode Sultan" ta fad'a tana fara ci. D'an yamutsa fuska tayi tace, "Yayi yaji, amma babu laifi ya d'an yi dad'i" ta fad'a tana ci. Yana zaune yana kallon ta har ta cinye tass ya sauke ajiyar zuciya ya tashi ya koma wajan Suhail ya ganshi a falon a zaune.

"Ka cika yaji" ya fad'a yana kallon sa Suhail da ya mik'e tsaye yayi murmushi ya sosa kai yace, "Afuwa ranka ya dad'e, a haka na siyo kayan miyan wataƙila suna cika yaji." Asad yayi murmushi yace, "Na gode Suhail, banda kai ba ban san ya zanyi da ita ba."  Suhail yayi murmushi yace, "Haba ranka ya dad'e meye abin godiya?." Asad yayi murmushi ya dafa kafaɗarsa sai kuma yanayin sa ya canja alamun ya tuna Hydar.

Suhail ya sassauta murya yace, "Sai haƙuri ranka ya dad'e, dukkan matakin nasara a rayuwa akwai qalubale, qalubalen kuma shine sirrin nasarar a rayuwa gabad'aya." Asad ya d'aga kai kafin ya juya ya koma shi kuma ya fita.

Lemo ya same ta tana sha ya zauna kusa da ita ya nuna mata leda ta buɗe taga undies ne sama da goma a ciki harda doguwar riga ta kalle shi tace, "A ina aka samo?." Tab'e baki yayi ya wara hannun sa alamun bai sani ba tace, "Har kwana nawa zanyi a nan ne na gansu da yawa?." Nan ma baiyi magana ba ta kalle shi sai ta d'auki ledar tace, "Bara naje na saka baa......." da baya ya dawo da ita ta fad'a jikin sa gabad'aya ya girgiza mata kai alamun A'a.

"Allah Sultan bana jin daɗin zama haka" ta fad'a yana kallon sa shima kallon ta yayi ya rad'a mata abu a kunne tayi dariya ta kifa kanta a k'irjin sa tana b'oye fuskar ta.
"Ina kika samo Sultan?" Taji ya tambaya a sama ta kalle shi tace, "Sultan shugaba kai shugaba ne a ko ina, nima shugabana ne kai."

Tab'e baki taga yayi sai ta kalle shi tace, "Ko baiyi maka ba?." Ya juya idanun sa yace, "It's not a romantic name."
"Wanne kake so nace?." Ya cizi bakin ta yayi murmushi ganin sai ta sake kwanciya a jikin sa shima ya rik'e ta.

Wayar ta taji tana k'ara ta d'ago ta mik'a hannu ta d'auka ta kalli wayar ta kalle shi tace, "Kaga number outside country ce." Ya kalla yaga number Saudia ce yace, "pick it." Ta wara ido tace, "Na sani ko scammers ne? Wa nake dashi a k'asar waje?." Da kai yayi mata alama da ta d'auka tana kallon sa ta d'aga wayar ta saka a speaker.

"Rauda Umman kice!." Jin muryar Umma a cikin wayar sai ta zabura ta mik'e daga jikin sa ta zauna tana rik'e da kafad'arsa sa tace, "Ummana?." Umma tace, "Na'am Rauda, kinga number Saudia ko? Ai jiya muka tafiya gabad'ayan mu yanzu haka muna Madina."

Rauda ta kalle shi sai taga ba ita yake kallo ba tace, "Umma Saudia kuma? Wai da gaske Ummana kece nifa gani nake kamar bake bace ba." Muryar Yaya Ummi taji tana cewa, "Sai nayicmagana zaki tabbatar itace?."
"Lahh Yaya Ummi? Harda ke? Nifa kun kulle min kai dan Allah kuna ina?."
"Ke Rauda wallahi da gaske muna Madina gabad'aya y'an gidan mu keda Rahma ne kawai babu."

Rauda tace, "Amma shine zaku tafi ko a sanar dani ai da nazo munyi sallama ko?. To wai waye ya biya muku dukkan ku kuka tafi ban sani ba?." Yaya Ummi tace, "Mijin ki mana, akwai wanda zai biya mana ne in bashi ba Rauda?." Gaban Rauda ya fad'i ta kalle shi sai ya d'aga mata kai tace, "Amma Yaya Ummi ban sani ba."

"Mijin kine yace kar mu sanar dake shiyasa mukayi shiru, yanzu kin ganmu har mun fito daga Rauda munyi gaisuwa a kabarin annabi mun koma masaukin mu." Rauda ta lumshe ido hawaye suna sakko muryar ta na rawa tace, "Har su Yayar mu?." Yaya Ummi tace, "Na fad'a miki gabad'ayan mu ne, kin gan mu zaune ma gama cin abincin mu kenan." Rauda ta fashe da kukan farin ciki Yayar mu da take jin komai tace, Kaji min Rauda da shashanci, to meye na kukan keda zakiyi farin ciki ki taya mu godiya sai ki fara kuka kuma?."

Datse kiran Rauda tayi ta kwanta a k'irjin sa tana kuka sosai, shiru yayi yana sauraron ta dan yasan babu lallai ta daina in yace ta daina tana jikin sa baice mata komai ba. Sai da tayi mai isar ta sannan ta d'ago ta kalle shi tace, "Shine ko ka fad'a min." Yayi murmushi yaja kumatun ta amma baice komai ba.

Bud'e baki tayi zatayi masa godiya ya d'ora hannun sa bakin ta ya girgiza kansa yace, "Bana son jin komai." Rauda tace, "Addu'a zanyi maka."
"Kiyi a zuciyar ki. Tashi muyi sallar la'asar" ya fad'a yana sauke ta daga jikin sa ya rik'e hannun ta suka shiga d'aki.

Alwala sukayi sukayi sallah ita dai har suka idar ji take wani iri wai iyayen ta da y'an uwan tane duka a Saudia ta dalilin ta, me ya kai wannan dad'i da farin ciki a duniya? Ace ta dalilin ka iyayen ka sunje Saudia ai abin murma ne. Yana lura da ita ganin zata sake yi masa kuka ya saka yace, "Bana son kuka Muwadda kin sani." Tace, "Farin ciki ne yayi min yawa Sultan, na rasa inda zan saka raina sabida farin ciki ji nake kamar bani bace. Ta dalilina iyayena suna Saudia sai naji kamar ana wanke min zuciyata sabida farin ciki Sultan shine yake sani kuka."
Chapter 125 · 0% Book details