Sashe 39
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun fita yaso ya kira Hydar amma bazai iya ba haka ya kwanta lamo yana jinyar zuciyar sa ya lumshe ido abubuwa da dama suna yi masa yawo a ido ya bud'e yana jin sautin muryar ta a lokacin da take cewa yayi mata alqawari. Wani irin nauyi yake ji a zuciyar sa karo na farko a rayuwar sa yayi alqawari bai cika ba nan take tashin hankalin sa ya sake ninkuwa. Wayar sa da take kusa dashi yaga kira na shigowa ya kalla yaga Khalifa ne yake masa waya ya sauke numfashi dan ya tabbatar maganar Rauda zaiyi masa shi kuma bai san me zaice masa ba haka ya share har ta katse.
Numfashin sa ya cigaba da janyowa da dak'yar kafin kansa yayi mugun sarawa k'irjin sa ya fara up and down daga zazzaɓi ya rufe shi lokaci d'aya. Suhaima ce ta shigo ganin halin da yake ciki ta kwallawa Mama kira ta tawo a guje ganin kamar zai mutu ya saka su danna emergency bell nan take sai ga ma'aikatan hotel d'in sun bayyana aka d'auke shi zuwa asibitin hotel d'in.
A b'angaren Rauda lokacin da suka bar Four Seasons hotel a mota ya saka ta yaja suka wuce estate d'in ma'aikata y'an Nigeria wanda suke aiki a garin irin sa. Gida ne mai kyau plat mai d'auke da ado tun daga wajan sa har ciki, fita yayi ya bud'e gate d'in sannan ya dawo ya shiga da motar ya kuma fita ya sake kulle gate d'in kana ya zagayo ya bud'e bayan mota dan tana kwance a bayan motar yace, "Zaki iya fitowa?." Kai ta d'aga alamun eh dan bata so ya rik'e ta ta fito dak'yar ta iya tsayawa tana takawa a hankali har cikin falon gidan ya gyara mata waje ta zauna.
Fita yayi ya shigo da kayanta sannan ya ajjiye ya shiga cikin gidan Jim kad'an ya dawo da magani da allura a hannun sa, ajjiyewa yayi ya k'arasa fridge ya d'auko yogurt ya dawo ya mik'a mata yace, "karb'i kisha sai kin saka wani abu a cikin ki magani zai miki aiki." Kallon sa tayi tana so tayi magana sai kawai hawaye ya fara zubo mata sharr duk sai yaji ya damu yace, "Haba chocolaty wannan kukan da kike yi wai duk na meye ne? Koma meye yake damun ki ki adana shi a gefe kisha magani tukunna."
Mik'a mata ya kuma yi yaga ta kalla tana goge idanun ta sai tace, "kaina."
"Na san yana miki ciwo shiyasa na baki dan ki sha sai kisha magani."
"Bazan iya sha ba."
"Zaki iya, karb'i" ya fad'a yana sake mik'a mata ta karb'a ta kai bakin ta tayi kurba d'aya ta ajjiye shi a jikin ta bata kuma sha ba.
"Bazan cutar dake ba Rauda, ina miki kallon k'anwata duk abinda zan yiwa k'anwata da muke jini d'aya shi zan miki. Ki kwantar da hankalin ki ki nutsu in ma zuciyar ki na rawa a kaina kar ki damu wallahil azim bazan cuce ki ba. Asad ya sanni farin sani in koda na cutar dake zai nemo ni duk inda nake" ya fad'a cikin sigar kwantar da hankali yana kallon ta.
Bata tanka ba ta d'aga gorar nonon tana sha har ta d'an sha da yawa ta ajiiye ya bata magani ta sha ya kalle ta yace, "shiga wannan d'akin da yake kallon ki huta zan kira deaf d'in naji ina yaje ya barki security suka yi miki haka. Kayan ki suna ciki in zakiyi wanka. Matar gidan bata nan ne tana wajan aiki amma nasan tana hanya." B'oyayyiyar ajiyar zuciya tayi jin yana da aure sai hankalin ta ya kwanta daman tunanin ta ta inda zata zauna dashi a gida d'aya shi ba wani nata ba bata ma tab'a ganin sa ba sai da tazo k'asar.
Bayan ta shiga d'akin kwanciya tayi wai ko zatayi bacci amma ina bacci ya k'auracewa idanun ta sai tunanin da tasan zai damu zuciyar ta, babban tashin hankalin ta in ta koma gida me zata cewa iyayen ta? Auren da bai cike sati hud'u ba ya mutu ko mutu ko kuma shiru zatayi da bakin ta?, sanar dasu zatayi ta zama bazawara ko kuma shiru zatayi?. Da wannan tunanin bacci ya d'auke ta dan a maganin da ya bata harda na bacci dan ta huta.
Ta jima sosai tana baccin bata farka ba sai dare ta kuwa tashi ciwon kan ya tafi sai kad'an ta kalli agogo ganin sallah ta wuce ta sai ta mik'e ba shiri ta shiga band'akin tayi wanka tare da alwala ta fito ta bud'e kayanta, gabad'aya sababbin kayan aka zuba mata a cikin akwatin wanda taje dasu guda d'aya ce. Hawaye taji suna niyar zubo mata tayi saurin mayar dasu dan bata ga amfanin kukan ba ta d'auki wacce taje da ita d'in ta saka ta tayar da sallah.
Bayan ta idar tayi addu'a kamar ko yaushe ta tashi ta koma gefen gado tana yamutsa fuska ji take gefen marar ta yana riƙewa, d'an k'aramin tsaki tayi dan tasan hakan yana nufin period d'in ta yana gab da zuwa.
Tagumi tayi hannu biyu da tunanin abinda ya fad'o mata zata kawar dashi ta koma wani amma ta kasa sai da ta tuna.
_i promise you I will never ever leave you no matter what!._ kalmar sa k'arshe kenan tsakanin su ta mayar da kwallar idanun a lokacin aka fara k'wank'wasa k'ofar d'akin.
Sai da ta nutsu sannan ta amsa bai shigo ba yace, "In zaki iya ki fito ku gaisa da Madam." Ba musu ta tashi ta yafa mayafin ta ta fita falon ta same su a zaune suna cin abincin ta zauna da murmushin yak'e a fuskar ta kafin tayi magana matar tasa tace, "Sannu Rauda, ya jikin naki?."
Ganin matar ta sakar mata fuska sai taji dad'i tace, "Da sauk'i. Ina wuni."
"Lafiya lau, ya zaman bak'unta?." Rauda tayi murmushi bata ce komai ba tace, "kiyi hak'uri yau aiki ya min yawa shiyasa ban dawo ba kina ta zaune ke kad'ai. Ga abinci kici ko zaki samu k'warin jikin ki" ta fad'a tana tashi ta zuba mata dankali mai Romo da naman kaza a cikin sa an yanka shi k'ananu.
Rauda tace, "da kin barshi bana jin yunwa." Ta kalli Khalifa tace, "kaji fa Dear wai bata jin yunwa" ta fad'a tana mik'a mata tana fad'in, "kici Rauda mara lafiya sai da abinci." Ba yadda zatayi ta fara ci a hankali bata jin d'andanon abincin gabad'aya dan tayi loosing appetite. Matar tasa ta koma kusa dashi ta zauna suka cigaba da hira harta ci iya yadda zata iya ta ajjiye.
Khalifa ya kalle ta yace, "Rauda na kira shi bai d'auka ba nayi masa message still bai reply ba, kin gwada kiran sa ke?." Shiru tayi bata amsa ba ya kuma cewa, "Halin Asad ne sai shi wallahi, wataƙila yana can ya keb'e kansa yace baya son magana amma duk da baya baici ya barki ke kad'ai ba." Rauda ta kalle shi idon ta na kawo ruwa tace, "ni dan Allah kasa na koma Nigeria basai kayi magana dashi ba."
Da mamaki yace, "meyasa zaki koma ba tare da sanin sa ba? Naga tare kuke kuma yayan kine yana dakyau yasan halin da kike ciki kafin ki tafi." Rauda idanun ta yayi rau-rau tace, "basai ka sanar dashi ba ko kayi masa maganar ma bazai saurare ka ba, dan Allah ka saka ni na koma gida na gaji da zaman nan ina son ganin Ummana." Kallon Ramla matar sa yayi itama ta kalle shi Khalifa yace, "kar ki damu zaki tafi Nigeria in sha Allah. Amma ina shi Asad d'in yake? Meyasa ya tafi ya barki?, ke ba k'anwar sa bace ba?."
Rauda tayi shiru bata amsa Khalifa yace, "ko ke ba k'anwar sa bace?." A hankali tace, "k'anwar sace."
"To ina yake? Kin kira shi ke da kanki?." Sai kawai ta fashe da kuka Ramla ta kalle shi ta girgiza masa kai alamun ya k'yaleta sai yace, "Yaushe kike son komawa Nigeria d'in?."
"Gobe" ta fad'a murya na rawa.
Khalifa yace, "Allah ya kaimu sai ki tafi." Ramla matar sa tace, "Ba jibi daman zaka tafi ba? Ta bari sai jibin sai ku tafi tare kaga ba wani sanin kan garin nan tayi ba bai kamata ta tafi ita kad'ai ba. Kema a bauchi kike?." Kai ta girgiza alamun a'a tace, "Katagum." Ramla tace, "bauchin kenan ai, shima a can yake abokin Yayan kine zai mayar dake har gida kinga ba saba tafiya kikayi ke kad'ai ba gwara ki bari in Allah ya kaimu jibin sai ku tafi."
Rauda ta d'aga kai alamun to sukayi shiru dukkan su Ramla ta lura a takure take sai tace, "ki shiga d'akin ki huta." Kamar jira take ta mik'e ta shiga ciki tana goge idanunta. Ramla ta kalle shi tace, "Shine yace maka k'anwar sace?." Khalifa ya girgiza kai alamun a'a yace, "Nine dai nake ganin hakan amma bai fad'a min ba gaskiya."
"Ni sai nake ganin kamar ba k'anwar sa bace."
"To wacece d'in sa da zasu zauna waje d'aya shida ita? Kin san waye shi kuwa wajan kamewa?."
"Ka sani ko matar sa ce?." Wara idanu yayi yana kallon ta yace, "Dan sarkin Katagum ne fa ta yaya zaiyi aure ba tare da an sani ba? Koma ace ba kowa bane ta yaya Asad zaiyi aure bamu sani ba?." Ramla tace, "to ka sani ko baya buk'atar a sani d'in ne? Kayi tunani yanayin ta bai gwada k'anwar sa bace in ba kuma ta tabbata ba k'anwar tasa bace wacece d'in sa? Budurwa sa kenan zamu ce?."