Sashe 51
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yace, "Mata da za'a aurar dasu babu kayan d'aki k'ofa wannan masarauta a bud'e take wajan ganin an tallafawa wanda suka samu, baza mu ce duka zamu taimaka ba amma zamuyi iya bakin k'ok'arin mu wajan ganin mun taimakawa kaso saba'in bisa d'ari. Ga maza manoma wanda basu da gonar noma kuma suna son yi akwai bbar gonar masarauta wacce a qalla mutane sama da dubu zasu iya noma a cikin ta, zata bayar kyuata ga duk wanda yake da ra'ayin yi ya noma ya girbe ya kuma kai gidan sa ba tare da ya bamu koda kwaya d'aya na abinda ya noma ba. Muna fatan wannan mulki ya zama silar shigar mu aljanna" ya k'arasa fad'a a hankali muryar sa na shaking alamun yanayin sa yana gab da canjawa maganar tasa tayi yawa dak'yar ya iya k'arasawa dan ma abin yana ransa ne ya saka shi ya fad'a.
Kirari ake masa ta ko ina ya kalli Uncle alamun ya k'arasa abinda zai fad'a Uncle ya k'arasa bayanin kamar yadda yace sannan ya sanar da matsayin Uncle ya koma Wazirin sa aka bawa wani sarautar Uncle a nan take akayi sabon nad'i don kowa ya shaida. A haka zaman fada ya tashi cikin farin ciki da walwala musamman mutane da suka ji dad'in kalaman Asad domin kuwa kowa ya burge shi musamman yadda yake magana cikin izza da k'asaita da kuma ilimi.
Hotuna aka dinga yi dashi y'an jarida suna cigaba da d'auka ana watsa labaran a duniya kafin a gama Mai martaba ya nufi komawa gida a k'asa ba tare da mota ba, shamaki ne a gefen sa na haggu waziri a gefen sa na dama sai mai rik'e da lema da masu fifita yana takawa a hankali ana cigaba da zubewa ana gaishe shi cikin girmamawa shi kam kai kawai yake d'agawa domin ya gaji matuk'ar gajiya.
"Allah yaja zamanin sabon sarki, Allah ya taimake ka ya bada ikon gudanar da mulki lafiya." Cak Asad yaja ya tsaya jin muryar wanda bai yi zato ba ya had'd'iye yawu mai d'aci ya juya yana kallon Baba suka had'a idanu Baba yayi murmushi shima Asad d'in murmushin yak'e yayi domin bai kai zuciya ba. Da hannu ya yiwa Baba magana da ya tashi daga durk'uson da yake yi sannan ya bada umarnin ya biyo shi ciki.
Kan Baba ya fasu ya washe baki yana take masa baya har k'aramar fada ta cikin gida aka raka shi ya zauna yana sauke numfashi ya rad'awa shamaki wata magana nan take kowa ya fita har Uncle aka barshi shida Baba kawai.
Asad ya kalli Baba yayi murmushi yace, "Baba barka da Rana."
"Allah yaja zamanin ka" ya fad'a yana yi masa jinjina. Asad ya nuna masa kujera yace, "Bismillah." Ba musu Baba ya tashi ya zauna Baba yace, "Ina neman Afuwa anyi shagali babu ni babu dangina, ina fatan an yafe mana."
Gaban Asad yayi mugun fad'uwa jin abinda yace zai zuciyar sa ta fara rawa ya daure yace, "Babu komai." Baba yace, "Allah ya bada ikon gunadar da mulki lafiya ya bada lafiya da tsahon rai, ya kare ka ya kuma tabbatar maka da duk abinda ka saka a gaba" ya amsa da amin Baba yace, "Mutanen gidan duka sunce a mik'a musu gaisuwa har ita uwar gidan."
Dammm gaban Asad ya buga ya runtse ido domin zargin sa ya tabbata bata fad'a musu abinda ya faru ba nan take tausayin ta ya sake mamaye masa zuciyar sa har yana jin ruwa na taruwa a idanun sa yace, "Ina neman afuwa Baba, Amma in sha Allah yau zan shigo gidan da kaina."
Baba da farin ciki yace, "Mai martaba da kansa zai ziyarce mu..? Alhamdulillah wannan abin farin ciki ne babba da ya same mu muna dakon zuwan mai martaba, Allah ya bada ikon zuwa muna maraba da bak'untar mai martaba har inda muke."
Murmushin yak'e yayi yace, "in sha Allah." Shiru fadar tayi kafin Baba yace, "Ina neman izinin tafiya domin naje na sanar da mutanen gidan baban bak'on da zai ziyarce mu yau."
Asad yace, "A sauka lafiya, muna godiya." Daga nan sukayi sallama Baba ya tafi Asad ya tashi ya shiga cikin gida ta k'ofar da take fadar a nan ya tarar da hadiman sa suka rakaya suka bi bayan sa zuwa ciki yana jin zuciyar sa kamar ana tafasata saboda tashin hankali ga kansa yana ciwo.
*Asad is coming*💃🤣
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*051.*
Shigar sa babban falon sa na k'asa ya tarar da Mama a zaune a kan kujera ta hakimce fuskar nan tata a d'aure ganin wannan yanayin ta sai da gabansa ya fad'i ya k'arasa inda take ya zauna a k'asa kusa da k'afafun ta hadiman sa suka ja da baya falon ya rage daga ita sai shi. Ta kalle shi taga fuskar sa tayi y'ar k'arama jijiyoyin kasa sun tashi alamun kansa na ciwo sosai har bak'i yayi.
D'auke kai tayi daga kallon sa hakan ya saka yace, "Allah yaja da ran mahaifiyata, da an sanar dani da nayi tattaki na amsa kira." Mama tace, "ba dole nazo da kaina ba kana neman kashe ni Asad." Da sauri ya d'ago kai ya kalle ta tace, "eh, kana neman kashe ni, daga fara gudanar da mulki kwana biyu yau har ka fara yanke hukunci ba tare da izinina ba?." Asad ya sunkuyar da kansa tace, "waye yace kace zaka bada babar gona ga duk namomin da bashi da wajan yin noma? Kasan burin da nake dashi a akan wannan gonar?."
Asad yace, "Mai martaba ya sanar dani nayi dukkan abinda talakawa zasu amfana shiyasa na yanke wannan hukuncin."
"To a soke shi! Mallakina nake so wannan gonar ta zama dan haka bata aro bace. Gidan gona zan mayar da ita shine burina a kanta ba tun yau ba. Girman ta ya wuce tunanin ka k'afa bata iya zagata sai dai da helicopter."
"Allah ya wuci zuciyar ki."
"Wucewar zuciyata shine a soke abinda ka fad'a, kuma daga rana irin ta yau kar ka sake yanke hukunci ba tare da izinina ba."
Asad yace, "Za'a yi Mama. Amma dan Allah ina neman alfarma badan ni ba badan kuma na isa ba, ki bari su amfana da wannan shekarar in lokacin ya wuce sai komai ya dawo hannun ki...." ya dafe kansa da yake masa mugun ciwo kana yace, "na riga na furta Mama, in aka canja maganar zasuyi tunanin wani abun za kuma su fara d'aukata mara cika alƙawari daga farawa. Kiyi min alfarman nan dan Allah."
Numfashi ta sauke tayi shiru ganin hakan ya saka yace, "Godiya nake, Allah yaja da rai ya jiqan Abie da Ummi." Ta juyo ta Harare shi kana tace, "Meyasa ka kasa sauke hakkin yarinya da yake kanka yau kwana uku da auren ku?." Ya sunkuyar da kansa k'asa baice komai ba yana jin maganar tayi masa mugun nauyi dan bata tab'a fad'a masa ita gata gashi ba sai dai ta fad'a a waya dalilin da ya saka kunya ta lullub'e shi ya kasa motsin kirki amma yaga ita ko a jikinta.
"Magana nake maka." Ya sauke k'aramin numfashi ya d'ago idanu ya kalle ta yace, "Kiyi hak'uri."
"Ba laifi nace kayi min ba tambayar ka nayi ka bani amsa." Nan ma yayi shiru ya kasa furta komai ta sake cewa, "Akwai matsala ne?." Ya girgiza kai alamun A'a ta bishi da kallon tuhuma sai kuma taji gabanta ya fad'i tunawa da abinda ta aikata a baya ta girgiza kai zuciyar ta na bata tabbacin wannan shine dalilin da ya saka komai ya tsaya.
Kawar da zancen tayi a zuciyar ta kana tace, "Na samu labarin mahaifin wannan shegiyar yarinyar yazo har kuka gana kai dashi, wanne matsayi yake dashi a wajan ka da zaku keb'ance haka?." Asad ya d'ago kai yace, "Babu."
"Meye dalilin aikata hakan to? Bana ce kar ka sake shiga abinda ya shafe ta ba?, kenan ban isa na hana ba ko?."
"Allah ya wuci zuciyar ki."
Taja tsaki kana tace, "wani lokacin kayan haushin ka kamar na shak'e ka haka nake ji Asad. Komai akayi ka bada hak'uri kuma baza ka tsaya ka yiwa mutane bayanin abinda aka tambaye ka ba."
Nan ma shiru yayi bai amsa ba ta girgiza kai tare da yin k'wafa ta mik'e tsaye shima ya daure ya mik'e duk da ciwon da kansa yake yi masa tace, "Tunda abin naka haka ne zanyi maganin su dukkan su." Jin abinda tace ya saka yace, "babu wata alaqa da take tsakanina dasu, yazo taya ni murna ne bayan hakan babu komai."
"To ya tsaya iya hakan! Magana bana so ta sake had'a ka da wani daga cikin y'an gidan su, ka san cewa yanzu kai shugaba ne kowa a k'asan ka yake ba ko wanne talaka zaka dinga yin magana dashi ba."
Kai ya girgiza alamun zai kiyaye har tayi gaba sai ta dawo da baya tace, "naji batun kashe kashen kud'i da ka d'orawa kanka na jama'ar gari, shima ban lamunce ba komai zakayi ka tabbatar ka sanar in ka zartar da hukunci ba tare dana sani ba Asad ranka zai b'aci."
"Zan kiyaye" ya furta a hankali burin sa ya daina magana gashi in tana yi bazai iya shiru ba dolen sa ya bata amsa.
"Na tuna da batun uncle d'inka Mubarak, waye ya baka ikon bashi sarauta mafi kusa dakai Asad? Ban fad'a maka zan baka list d'in wanda zaka yiwa sarauta ba?." Asad ya lumshe idanun sa zuciyar sa cike da mamakin Mama ganin ita take so ta zama sarkin bashi ba yace, "Ina buk'atar sa a kusa dani ne Mama, ban san komai ba shi nake so ya nuna min komai dashi Abbana ya amince nima dashi na amince."