← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 131

Sashe 113

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan mintina biyu suna haka kafin yace, "Daga ina kike?." Ta d'ago ta kalle shi ta shagwab'e fuska tace, "na rako Yaya Ummi titi."
"Da izinin wa?." A sama taji maganar ta d'ago ta kalle shi taga tamkar bai tab'a yin dariya ba a duniya sai taji tsoro ya mamaye mata zuciya tace, "Ba kowa."

Ya sauke numfashi ya jingina da kujerar yana kallon ta ji yake tamkar ya tsinka mata mari sabida yawan haushin ta da yake a cikin zuciyar sa, ya d'auki sacannin baice komai ba kafin yace, "Zaman kanki kike kenan?." Gajiya tayi da bashi amsa cikin k'osawa tayi tace, "A'a." Kai ya girgiza ya kalli titi kafin yace, "Shine kika tsaya bakin titi kina siyayyar banza da wofi?."

Kai ta kawar domin bazata bashi amsa ba itama sai dai yayi duk abinda zaiyi yadda yake jin haushin ta itama nasa haushin take ji sosai bai kuma isa ya juya ta ba, ganin ta juyar da kai bata bashi amsa ba itama ta d'aure fuskar ta sai ya share ta ransa ya sake b'aci bai kuma kallon ta ba ya kira number Suhail yana ganin kiran ya shigo motar kai tsaye gidan su Rauda aka nufa.

Babu wanda yake magana a lokacin da yake babu tafiya sosai lokaci d'aya akazo gidan su Rauda ya tsaya ya bud'e motar ya fita ya sake barin su. Buɗe motar zatayi taji an saka lock ta koma ta zauna tana kallon gidan nasu da yake tarr da haske tamkar ba dare ba.

Mota ce ta tsaya a k'ofar gidan Rahma ta fito daga gaban motar Anas ya fito shima yana yi mata magana kafin Rahma ta shiga ciki ta barshi a wajan a tsaye. A tare Rauda da Asad suka kalli juna ta sake kallon Anas da yake taaye ta sauke numfashi kafin tace, "Ka Buɗe min motar zan shiga gida."

In motar da suke ciki ta amsa tabbas shima ya amsa yayi mata bama ita yake kallo ba wani wajan yake kallo zuciyar sa kamar ana bulbula mata kalanzir ganin Anas a tsaye a k'ofar gidan su. Kamar tayi kuka sabida takaici tace, "Ka buɗe min." Nan ma yyi mata banza ta kalle shi idanun ta ya taru da hawaye amma bama ita yake kallo gabad'aya.

Itama banza tayi ta juya hawaye ya sakko mata ta girgiza kai tana cize bakin ta dan tasan babu abinda zata iya, kusan minti biyu suna a haka kafin ta juyo ta kalle shi tace, "Ka bud'e zan shiga gida bacci nake ji" ta fad'a cikin muryar kuka tana kallon sa. Juyowa yayi ya kalle ta ya d'aga gira sama ya tab'e bakin sa ya sake mayar da kallon sa ga wajen gidan.

Ganin kiran mai martaba yana shigowa ya saka shi kallon ta yace, "In kika sake kika kula wancan sai ranki ya b'aci" ya fad'a yana danna lock d'in ya buɗe ta fita daga motar bayan ta d'auki ledar kayan ta. Yana kallon ta har taje kusa da Anas d'in sai yaga tayi saurin shiga gida bata tsaya ba sai a sannan ya d'auke ido daga kan gidan Suhail ya shigo suka tafi bai san itama bata son had'a ido dashi dan kunyar sa take ji.

Akan hanyar su ta tafiya Suhail yace, "Ranka ya dad'e zan iya magana?."
"Uhum" ya furta yana danna wayar sa. Suhail yace, "ayi haƙuri zan shiga abinda bai shafe ni ba, amma ranka ya dad'e bai kamata a dinga barin fulani tana fita ita kad'ai ba, akwai tarin mak'iyan da suke nufin kawo mata hari ko a mutanen gari y'an unguwa akwai wanda baya qaunar ta yake neman hanyar cutar da ita, barin ta tana fita ita kad'ai akwai matsala. Allah ya taimake ka bawai zan koyawa mai martaba abinda zaiyi bane amma yana dakyau ace tana da personal driver wanda aka amince dashi before ta dawo gidan sarauta."

Asad yana jinsa yasan kuma gaskiya ya fad'a ya girgiza kansa alamun gamsuwa amma baiyi magana ba daga nan bai sake mgana ba shima ba suka cigaba da tafiya.

        A b'angaren Rauda rai a b'ace ta shiga falon Umma ta samu Rahma a zaune suna gaisawa da Umma ganin ta sai ta d'an saki rai Rahma ta mik'e ta rungume ta tana dariya tace, "Yanzu nake tambayar ki, duk da fushi nake dake Anty Rauda har yanzu baki je inda nake ba." Rauda tayi murmushi tace, "Banda son wayo Rahma ina ke ina fitowa yanzu?."

Umma tace, "Nima haka nace Rauda, amma dai baki kyauta ba da baki je ba." Rauda ta zauna kafin tace, "Allah zan zo." Rahma tace, "to ya zanyi ina nan ina jira, bara na shiga wajan Inna" ta fad'a tana fita Rauda ta bita da kallo ganin tayi haske har kib'a tayi ta juyo da kallon ta ga Umma da itama ita take kallo.

Umma tace, "Ina kika je kika dad'e haka daga rakiya?." Rauda ta fito da ledar gefen ta tace, "Wallahi masu kayan marmari na gani a gefen titi na tsaya na siya" ta fad'a tana d'auki apple guda d'aya ta fara ci. Umma tace, "bakya jin magana Rauda, ina ke ina tsayawa akan titi kina siyayya? Kin manta matsayin da Allah ya baki? Ko kin manta abubuwan da aka fad'a a gaban ki ke kanki kin san baki wuce a nemi kashe ki a wannan yanayin ba."

Rauda ta sauke numfashi tace, "sha'awa suka bani wallahi shiyasa na tsaya." Umma tace, "Wannan ba inda zaki dinga tsayawa siyayya bane malama, ki nutsu ki fuskanci abinda yake tankaro ki domin kuwa jibi ake zancen komawar ki gidan sarautar." Rauda ta tsaya da cin apple din da take yi ta wara ido waje tace, "Wacce jibin Umma?."

Umma tace, "Juma'a." Rauda ta dafe k'irji tace, "Kuma Umma sai kuka amince?." Umma ta bita da kallo tace, "to sai muce A'a? Daman ba ranar muke jira tazo ba ki koma gidan ki kema a daina miki kallon bazawara?." Rauda idon ta ya ciko da hawaye tace, "Amma Umma jibi yayi kusa, kamar wata y'ar tsana za'a ce wani jibi zan koma."

Umma ta bita da kallo kafin tace, "ke zmaan gidan bai ishe ki ba Rauda?." Tayi shiru ta sunkuyar da kanta k'asa Umma tace, "in ke bai ishe ki ba ni ya ishe ni Rauda, bawai don bana sonki ba sai dan kin wuce zaman gida zaman gidan miji shine ya dace dake. A unguwa da y'an uwa ana ta yawo dake a baki bakya jin tsoron bakin mutane?."

"Wanda suka san shi mijin kine sun sani domin ni babu wanda zan fad'awa komawar ki daga ke sai y'an uwan ki ayi komai a gama Allah yasa kin shiga a sa'a ya d'ora ki akan dukkan maqiyan ki dana mijin ki ya baku zaman lafiya mai d'orewa."

Rauda ta sauke numfashi bata ce komai ba ta tashi ta shiga d'aki ta bar kayan marmarin a wajan dan ji tayi sun fita daga ranta.
D'aki ta shiga ta cire hijjabin jikinta ta cillar tace, "Aikin banza, bai san nima haushin sa nake ji ba zai dinga wulaƙanta ni shi a lallai ga shugaban al'umma. Aikin banza ni gabad'aya haushi yake bani ya cika nuna isa."
Zama tayi a gefen gadon tana tunani kafin taja tsaki ta tashi ta shiga band'aki ranta duk a jagule.

*☆☆*

         B'angaren Asad lokacin da ya koma a fusace yake bayan ya kammala shirin sa na kwanciya yana zaune yana aikin jan tsaki zuciyar sa cike take da b'acin ran abinda ta aikata. 'Ta tsaya a kan titi tana siyayya kamar wata namiji, anyi mata magana kuma ta yiwa mutane banza da yake bata da kunya, da ace ta yiwa wannan banza magana da sai na b'ata mata rai sai tayi dana sanin kula shi din da tayi' abinda yakr fad'a kenan a zuciyar sa cikin fad'a.

"Aikin banza" ya furta a bayyane yana jan tsaki gabad'aya ransa a b'ace yake a haka ya kwanta zuciyar sa babu dad'i yana ta fad'an sa shi kad'ai.

Bayan kwana biyu.

Tun daga bakin gate d'in masarautar ta zaka san ana gagari min biki domin tambari ne yake tashi da busa algaita da abubuwa masu dad'i. Duk da babu jama'a da yawa a gidan amma kana ganin kasan akwai abinda ake gabatarwa a cikin sa.

Da yamma aka tura da babbar mota da jiniya aka d'auko Rauda daga gidan su zuwa gidan sarauta bayan tasha adon lalle da duk abinda ake yiwa amarya an mata itama y'an uwanta suka rako ta zuwa gidan.

Babu b'angaren da ba'a kaita ba har na Mama duk da bata nan amma y'an uwanta sun zo tarbar Rauda cikin mutunci da girmamawa suka karb'e ta kafin a zaga da ita ko ina daga baya aka kaita b'angaren da ya kasance nata.

A wannan lokacin jakadiyar ta mai suna Samira da bayin ta da komai suka gabata a gaban ta ita dai bata yi musu ba sai Yaya Ummi ce ta sallame su suka tafi itama kafin su barta dukkan su su watse suka barta ita kad'ai tana kuka kamar yarinya k'arama.

Sai da akayi sallar i'sha tana zaune a gefen gadon da ya kasance nata bayan ta idar da sallar i'sha akayi sallama a k'ofar d'akin tare da fad'in, "Barka da hutawa ranki ya dad'e." Rauda ta kalle ta dan ita bata saba da irin wannan maganar ba hakan ya saka tace, "Barka."

"Fulani Hajiya ce ta aiko ni da kanta domin na raka Fulani b'angaren mai martaba." Rauda ta sauke numfashi kamar tace bazata je ba sai ta d'aga kai tace, "ki jira ni ina zuwa." Jiki na rawa ta mik'e ta fita Rauda tafi minti biyu bata tashi ba kafin ta tashi tayi wanka ta saka kaya da dogon hijjabi ta bata umarnin ta shigo.

Jiki na rawa ta shigo ta k'araso da sauri ta tsaya a bayan ta Rauda ta kalle ta tace, "Kece zakiyi gaba ai ni da ban san wajan ba." Hadimar tace, "Wane mutum, ranki ya dad'e ni wacece da zaki bi bayana? Sai dai ni na biyo naki bayan." A guje ta zabura ta kwasowa Rauda takalmi ta skaa mata da kanta sannan tace, "Ranki ya dad'e zamu iya tafiya?."
Chapter 113 · 0% Book details