Sashe 117
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wacce nazo na tilasta shi ya aura sai gashi ita da babar ta suke so su kashe ni, daman yasha fad'a min Mama bata dace dani ba amma nak'i ji nace ko baya so dole ya aureta, ya aure ta d'in ya hak'ura ya zauna da ita ya fara mulkin da nake so na fara saka shi yana yin duk abinda nake so koda shi baya so koda kuwa ya sab'awa shari'a. In ban nemi yafiyar Asad ba me zanyi?. Ta silar mulkin da baya so aka masa kurciya ya bar k'asar nan ya koma wata k'asar amma da ya dawo sai ya cigaab da fafutukar neman ganin bayan makiya na" Ta fad'a tana sake fashewa da kuka.
Asad yayi shiru ya kasa magana Mama ta kuma cewa, "Hydar da Asad yake so sama da komai a duniya dashi kad'ai ya yarda ya kuma aminta amma shine yake cin dunduniyar sa yake neman kashe shi duk ta silata kuma, da ace ban nuna k'arara Asad nake so yayi mulki ba da hakan duk bata faru ba. Ga Aliyu ma da yaso kashe Asad....Kai na cutar da Asad cuta mai tsanani" ta fad'a tana dafe kanta ta sake fashewa da sabon kuka.
Murya na rawa ta fara cewa, "Hydar! Aliyu!. Hydar d'ina shine yake so ya kashe Asad Hydar fa? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Duk abinda ake shiryawa ashe Hydar ne sila shine yake komai amma a zahiri sai ya nuna bai san komai ba, ya zanyi da rayuwata?. Y'ay'ana biyu duka babu na zab'e." Ta sake fad'a tana sake fashewa da sabon kuka ta kwanta a kan kujerar.
Asad ya tashi akan guiwar sa ya rik'e ta yace, "Mama likita yace kar ki shiga damuwa dan Allah ki kwantar da hankalin ki komai ya wuce."
"Ta ina ya wuce Asad? Bayan Hydar ya tabbatar da bai gama d'aukar fana a kanka ba yana nan zai dawo, in ya kashe ka ya zanyi Asad?. D'an uwanka jinin ka wanda kuka fito duniya lokaci d'aya ace shine yake neman d'aukar rayuwar dan uwan sa? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ina ma na mutu kafin wannan ranar. Meye amfanin maza ukun da nake alfahari ina dasu? Makisa, makirai, masu son kansu, masu son duniya akan D'anuwan su?, meye abin alfarahin da zanyi dasu? Basu da wani amfani dukkan su ina ma Allah ya d'auki rayuwar su gabad'aya na huta."
Mama Jamila tace, "bai kamata kina fad'ar wannan kalmar ba Mama, dan Allah kiyi haƙuri. Ya kike so Asad d'in yayi shida a lokaci d'aya ya rasa y'an uwan sa da babar sa suka juya masa baya? Ya kike so yayi lokacin da aka kwantar da mahaifin sa mai share masa hawaye?."
Mama ta tashi zaune ta dafe kai da hannun ta tace, "Duka ta silar Hydar wad'annan abubuwan suka faru, da kuma son tawa zuciyar badan na bayyana burina ba da duk hakan bata faru ba, da yanzu suna nan tare shida Hydar kamar da." Asad yace, "Dan Allah Mama ki daina kuka kodan lafiyar ki."
"Ka yafe min Asad, kace ka yafe min dan Allah."
"Mama dan Allah" ya fad'a a raunane yana kallon ta kamar zai zubar da hawaye shima.
Mama tace, "ku taya ni rok'on yafiyar sa dan Allah kar na mutu da hakkin sa a kaina." Asad yace, "Mama baki min komai ba, kina da iko dani har yanzu; ko yanzu kika ga abinda baki so a tare dani zaki iya cewa na hak'ura kuma na hak'ura domin kin isa." Mama ta girgiza kai tace, "A'a Asad, bazan sake hana ka abinda kake so ba har abada duk abinda kake so shi nake so, su wanda nake bawa abinda suke so d'in sune suke k'okarin ganin bayana kai da nake tauyewa kaine kake k'okarin ganin na rayu kake tsaye a kaina kana nema min lafiya. Naji dad'i da ya kasance Aliyu yana cikin yanayin hauka da lafiya saura Hydar shima Allah zai hukunta shi daidai da abinda ya aikata."
Mama ta kalli su Mama Jamila tace, "Ku kira min Suhaima tazo ta raka ni wajan matar sa na bata haƙuri." Asad yace, "Dan Allah Mama ki kwantar da hankalin ki baki da cikakkiyar lafiya fa."
"Nidai a kaini inda take na bata haƙuri nayi mata abubuwa da yawa a rayuwa wanda bazata manta dani ba." Mama jamila ganin yadda Mama ta rude lokaci d'aya sai tace, "Ranka ya dad'e a kira Fulanin taka tunda hakan take so ko dan sabida jikinta."
Asad ya kalli Suhaima da ta fito da kai yayi mata alama da ta kira Rauda ta amsa ta fita. Ba jimawa suka dawo tare da Rauda ta zauna akan k'asa kamar yadda Asad d'in yake tace, "Barka da dawowa Mama." Jin muryar Rauda sai Mama ta kalle ta tace, "Tun kina asibiti lokacin da Hydar ya buge ki ban tab'a ganin ki ba amma na d'auki tsanar duniya na d'ora miki, na saka aka kore ki daga asibitin ta silar hakan kika samu matsalar k'afa, ta silar hakan abubuwa da yawa suka faru dake wanda na samu labari da wanda ban samu ba. Na saka akazo har gidan ku aka ci muku mutunci aka daki mahaifiyar ki, daga nan ban hak'ura ba na sake dawowa da kaina na sake ci miki fuska akan kud'urina wanda Allah ya riga ya rubuta ke matar sace. Na sake turowa har gidan ku a kashe ki Rauda, kisa nayi k'okarin yi a kanki a karo na farko a rayuwata" ta fad'a da kuka sosai ta kasa cigaba da magana.
Dukkan su shiru sukayi kafin Mama ta cigaba da cewa, "Allah ya nuna min ikon sa akan aure ku akayi ba tare da na sani ba amma maimakon na hak'ura na d'auka haka k'addarata take sai na sake sakawa ana yi miki aikin da zaki bar duniya, har hijjabin ki an tura an samo a gidan ku dan ayi miki aiki a kashe ki amma Allah bai nufa ba duka ban hak'ura ba na skaa aka yiwa Asad aiki...." Sai ta sake fashewa da kuka Asad yace, "Dan Allah Mama ya isa haka duka komai ya wuce ki daina kuka Mama bana so" ya fad'a yana rik'e hannunta idanun sa sunji ja sosai.
Mama tace, "barni na fad'a, har abada bazan yafewa Sadiya ba dukkan abinda ya faru itace take shiryawa haka kawai bana iya tsallake maganarta komai tace sai nayi bana iya tsallakewa ban san meyasa ba. Nayi abubuwa da yawa akan ka da kuma matar ka Asad, inda ace nasan akwai idda a kanta da a lokacin da na saka ka sake ta bazan bari ta fita ba sai ka yanke igiyoyi biyun da suka rage ba, amma da yake Allah yana so ya nuna min in ya rubuta abu ban isa na goge ba sai gashi matar kace har yanzu ko a wannan yaci ace na fuskanci ikon Allah akan bayin sa."
"Duk wad'annan abubuwan da nayi miki keda iyayen ki baki rike shi ba kika tura min anniyata nazo har gidan ku neman alfarma maman ki ta tashe ki kika raka ni inda na samowa Asad da mahaifin sa da kuma Hydar, a kan hanyar dawowa akaso kashe ni kika cece rayuwata. Ban sani ba ashe kece kika kawo silar samuwar lafiyar mai martaba, tabbas kin turo min aniyata gata nan kuma ina gani tunda gani a zaune babu lafiya y'ay'ana biyu dukka sun zama y'an ta'adda. Ki yafe min Rauda dan Allah iya hakkin ki bazai barni na zauna lafiya ba dan nasan nayi miki abinda babu wanda ya tab'a yi miki shi a duniyar nan."
Rauda hawaye take yi ta girgiza kai tace, "Babu komai Mama ni komai ya wuce a wajena kin wuce neman alfarma a gare ni, ki yafe min in na tab'a b'ata miki rai nima." Mama tace, "Baki tab'a ba Rauda ba kuma zaki tab'a ba, babban burina kice kin yafe min dan Allah." Rauda tace, "Na yafe Mama."
Mama tace, "Na gode Rauda Allah ya saka miki da alkhairi ya raba ki da abinda yake jikin ki lafiya." Ta kalli Asad tace, "Na dawo kanka banji kace ka yafe min ba Asad, kaga y'ar albarkar matar ka ta yafe min saura kai." Asad yace, "Mama baki min komai ba dan Allah ki daina fad'ar haka, in ma kinyi na yafe miki Mama."
"Na gode Asad, tabbas zaka cigaba da ganin sakamakon biyayya a rayuwar ka, Allah yayi maka albarka ya kare ka daga y'an uwanka masu nufin ka da sharri a duk inda kake." Aka amsa da amin kafin ya tashi tsaye ya tasar da Mama ya kaita har cikin d'aki yana rik'e da ita ta zauna ya bata maganin ta da kansa ta kwanta yace, "Ki huta Mamana, dan Allah ki daina saka damuwa a ranki ina tare dake har abada."
Hannun sa ta rik'e yana zaune a gefen ta a haka bacci ya d'auke ta. Sai da ya tabbatar baccin yayi nisa ya fito bai samu Rauda ba sai kannen Maman ya kalle su yace, "Mama dan Allah a kula da ita." Tace, "in sha Allah ranka ya dad'e zamuyi iya bakin k'okarin mu." Daga nan ya fita dan baiga Rauda ba.
Kai tsaye b'angaren mahaifin sa ya wuce ana take masa baya kamar d'azu shi kad'ai ya shiga ya same shi zaune dashi da Uncle yana shigowa Uncle sai ya tashi ya shiga ciki Asad ya zauna a k'asa yayi ahiru baice komai ba, Mai martaba yace, "Fuskar ka akwai damuwa a tare da ita Asad, meye yake faruwa?."