← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 131

Sashe 62

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin gab da sallar azahar ya shiga har cikin gidan masallacin cikin gida ya zauna yasan indai mai martaban yana gari tabbas zai fito sallah.
Hakan ce ta kasance kuwa ana yin kiran sallah ya aka sanar da isowar sa bayan an tary gabad'aya, bayan an idar mai martaba ya fita Baba yabi bayan sa ya shiga cikin makarrban sa ya k'arasa gaban sa yana fad'in, "Barka da rana ranka ya dad'e." Cak ya tsaya ya kalli gefen da Baba yake sai kuma ya d'auke kansa bai amsa ba sai yayi ciki Baba duk da haka bai daina bin bayan sa ba.

     K'aramar fada ya shiga Baba yana tsaye sai ga dogari yazo yace ya shigo suka shiga Baba yana baya shi yana gaba, a k'asa ya zube yana yi masa jinjina yace, "Allah yaja da ran sarki, Allah ya k'arawa sarki lafiya da tsahon rai, Allah yasa afi haka." Lumshe ido yayi ya bud'e shamakin sa da sauran dogarai suna amsawa da amin kafin wani dogari yace, "Fad'i matsalar ka."

Baba ya gyara zama duk sai yaji wani iri ganin yanayin Asad din shima sai yasha jinin jikin sa yace, "Ranka ya dad'e kwana biyu da suka wuce aka kai mana takarda akace wai notice ne umarni daga gare ka mu tashi za'a rushe inda muke zaune, ban d'auki abinda mahimmaci ba amma sai gashi yau anje da motar rusau za'a rushe, shine nazo gare ka duba da ban san dalilin hakan ba."

Asad yayi shiru zuciyar sa na bala'in harbawa amma kuma haushin Baban yake ji gabad'aya a zuciyar sa ba tare da ya shirya ba yace, "Ba iya gidan ku kawai bane, duk gidan da ya shiga hurumin talaka zamu rushe shi."

"Wannan gaskiya ne, dan sarki kake jikan sarki kuma sarki" aka fad'a daga zaune cikin kirari. Baba jikin sa yayi sanyi ya kuma cewa, "Amma ranka ya dad'e gidana yafi sama da shekara ashiriin a inda yake gyare-gyare kawai aka samu ba samon gini bane, a duba lamarin ranka ya dad'e" ya fad'a a sanyaye zuciyar sa na bugawa.

"Iya abinda zamu iya kenan" ya furta a hankali ba tare da ya kalli Baban ba fuskar Asad d'in a d'aure matuk'a. Baba ya kalle shi cikin mamaki ganin kamar bai gane shi ba hakan ya saka shi sake kallon sa cikin dunbin al'ajabi.
"K'asa da idanun ka, Hattara Dattijo kallon idanun mai martaba yafi k'arfin ka." Baba ya saukar da ido yace, "Allah yaja zamanin mai martaba bamu da inda zamu koma in hakan ta kasance, kuma a ina neman afuwa amma rushe gida a k'arkashin gwamnati yake ba masarauta ba."

"Hattara dattijo! Kasan a inda kake" aka fad'awa Baba cikin tsawa. Baba yace, "Tuba nake." Asad yayi shiru idanun sa a lumshe sam baya k'aunar ganin Baba ko kad'an a kusa dashi ya sunkuya ya rad'awa na gefen sa magana sai ya zabura ya mik'e yace, "Dattijo muje." Baba ya kalle shi ya kalli mai martaba ganin da gaske babu fuskar maganar sai yayi k'asa da kasa, "Tashi mana!" Aka sake fad'a da k'arfi Baba ya firgita ya mik'e ya fita jikin sa yana rawa zuciyar sa cike da zallar mamakin Asad da kuma tsoro........
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*057.*

          Mamaki ya gama dabaibaye Baba tafiya yake jiki a sanyaye kamar zai kifa kansa har juyawa yake sabida yadda lamarin ya cushe masa kai da kwakwalwar sa. "Baba!" aka fad'a daga gefe Baba ya kalli inda yaji an kira sunan sa yaga Hydar ne fuskar sa da murmushi yana k'arasowa inda yake.

Baba ma murmushin k'arfin hali yayi yace, "Ranka ya dad'e." Hydar yayi murmushi yace, "ziyara aka zo mana kenan?." Baba ya numfashi yace, "kusan hakan, matsala ce aka je mana da mota za'a rushe mana gida wai anyi gini a filin marayu, shine nazo da kaina wajan mai martaba naji abinda ya jawo hakan dan kowa yasan gidana yafi shekara ashirin a wajan da yake gyaran da kuka yi mana shine kawai ya sauya shi."

Hydar yace, "rushe gida kuma? To ya kukayi dashi?." Baba yace, "to bai ma saurare ni yadda ya kamata ba balle har yaji dalilin hakan, abinda yace min kawai iya abinda za'a iya kenan. Yanzu akan wanne dalili kenan za'a rushe mana gida? Mu ba'a kan hanya muke ba, ba'a kan titi muke ba rana tsaka azo ace za'a tashe mu ina zamu je?." Hydar ya furzar da iska zuciyar sa cike da bak'in cikin yace, "kayi hak'uri Baba, zan iya iya bakin k'ok'ari na wajan ganin hakan bata kasance ba in sha Allah. Ka kwantar da hankalin ka ya canja halayyar sane gabad'aya yanzu wani lokacin in yayi wani abun kamar bashi ba."

Baba ya girgiza kai yace, "to na gode, sai anjima" abinda yace kenan ya juya zai tafi, Hydar ya d'auko kud'i yace, "Baba ga wannan ka hau mota." Baba ya kalli kud'in ya girgiza kai kana yace, "na gode" yana fad'a ya nufi hanyar fita Hydar ya bishi da kallo zuciyar sa sam babu dad'i ko kad'an.

Fusata Hydar yayi ya nufi b'angaren Mai martaba yayi sa'a har lokacin bai tashi ba ya shiga kansa tsaye ya same shi shida makarraban sa kowa ya bishi da kallo har Asad d'in dan yadda ya ganshi yasan ransa a b'ace yake, ganin hakan Hydar yace, "Ina son ganawa da mai martaba ni kad'ai, ko zaka iya bamu waje?."

Suka kalli Asad ya d'aga musu kai alamun suje auka Mike suna fad'in, "A tashi lafiya." Hydar ya kalle shi yana zaune yayi zaman sarkai akan kujera cikin shigar da ya saba in ba zaman fad'a zaiyi ba yace, "Amma kasan abinda kake aikatawa ba daidai bane ba ko?." Bai bashi amsa ba yasan daman bazai amsa masa ba yace, "Ina ruwan gidan su tsohuwar matar ka zaka saka aje a rushe musu gida? Duk kyautatawar da suka yi maka da abinda zaka saka musu kenan?."

Asad ya sauke numfashi kamar bazai yi magana ba ya kalle shi yace, "Ina matsayin shugaba a gare ka zaka zo kana yi min ihu a kaina dan kaga ina k'yale?." Sai ya cize baki ya girgiza kansa kana ya kuma cewa, "Bana son su, bana qaunar ahlin su yarinyar gabad'aya sai me?."
"Ka kyauta, kayi abinda kake so akwai limit d'in da za'a zo in akace kayi baza kayi ba." ya fad'a rai a b'ace yana kallon Asad da shima shi yake kallo cikin mamakin da ya kasa barin sa. Tashi Asad yayi ya shiga ciki ya bar Hydar a tsaye yana kallon sa har ya b'ace ya girgiza kai ya fito.

          B'angaren Baba lokacin da ya shiga gida a babban falo ya samu matan sa sai Rauda da Rahma k'ananun sun tafi makaranta yanayin da ya shiga ya saka suka bishi da kallo har ya zauna ya cire hular kansa ya dafe kansa, Umma tace, "Malam lafiya?." Baba yayi kalle su kafin yace, "Wanne gida kuke ganin zamu samu haya daga yau zuwa gobe?."  Rauda tace, "Kenan sai mun tashin? Nifa bazan bari hakan ta faru ba wallahi zan iya shiga gidan rediyo akan maganar nan."

Baba yace, "Dakata malama! Babu yadda zamuyi tashin ya zama dole dan yanzu ma daga gaban mai martaban nake amma nayi dana sanin zuwa tunda nake ban tab'a jin to tozarcin da ya tab'a min zuciya kamar wannan ba." Umma ta girgiza kai tace, "bai saurare ka ba kenan?." Baba yace, "Yace iya abinda zasu iya kenan, a tak'aice dai sai an rushe badan Anas bama ai da ba wannan zancen ake yi ba."

Rauda ta zabura ta mik'e tace, "Akan wanne dalili wai za'a rushe mana gida? Me muka aikata?. Wallahi bazai yu ba dan kawai a tozarta mu kawai sai ace za'a rushe gida? Daman can ai ba mu muka ce su gyara gidan haka ba; sune sukayi niya da ra'ayi, fili namu ne dan haka basu isa suce zasu rushe mana gida ba wallahi. Ina zuwa" ta fad'a tana niyar fita Baba yace, "Kee Rauda, dawo nan." Ba musu ta dawo ta zauna Baba ya kalle ta yace, "Kome ya faru nine na jawo Rauda, na nuna musu ina son dukiyar su a kanki shiyasa suke yi mana duk abinda suka ga dama, kar naji kinje gidan wata radio akan wannan ku fara had'a kayan su zamu tattara mu bar gidan kar a wulaƙanta mu."

    Rahma tace, "Amma Baba Anty Rauda tana da gaskiya banga dalilin....." baba ya dakatar da ita yace, "Rahma ya isa haka, kuyi abinda nace kawai" yana fad'a ya mik'e ya fita ya hau saman sa jikin sa a salub'e.

Rauda ta runtse idanun sa sabuwar tsanar Asad take ji tana zaga ko ina na jikinta fiye da wacce take ji a baya, da ace tana da dama sai tayi masa abinda bai tab'a tunani ba a yanzun ma kuma bazata fasa ba sai ta nuna masa daidai take dashi.

Umma tace, "Abin mamakin in dai ba shirin to tozarta mu akayi ba ina masarauta ina hurumin rushe gidajen mutane?." Inna tace, "Abinda na gani kenan, sai dai in anso a wulaƙanta mune kawai." Rahma tace, "In Allah ya amince baza mu wulak'anta ba sai dai yaga wulaƙanci akan sa." Rauda ta furzar da iska tana jin wani iri a jikinta gani take kamar ko meye ya faru itace ta jawo, jin dad'in tama dasu Walida suka tafi da bata san yadda zatayi ba kunya ba.

*☆☆*

        B'angaren Mama kwana d'aya ta rame sabida ciwon kan da ta kwana ta tashi dashi babban tashin hankalin ta kuma rashin kiran wayar da Mum bata yi mata ba har lokacin, duk ta damu hankalin ta ya tashi matuk'a kana kallon yanayin ta zaka fahimci hakan. Tana zaune dafe da kanta Suhaima na zaune a k'asan ta tana matsa mata k'afafun ta suka ji sallamar Mum tare da shigowa. Mama ta kalle ta Mum ta k'araso tana fad'in, "Tuba nake ranki ya dad'e,  Allah ya wuci zuciyar ki" ta fad'a tana k'araso ta zauna a kan carpet.
Chapter 62 · 0% Book details