Sashe 123
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A kafaɗarsa ta kwantar da kansa ya zaga da hannun sa ya rik'e k'ugun ta hannun sa d'aya yana cikin nasa, kuka yaji ta fara a hankali kafin tace, "Na shiga tashin hankali Sultan, nayi dana sanin zuwana duniya gabad'aya." Numfashi ya sauke ya d'ago da kanta yana kallon idanun ta yace, "Ban tab'a alƙawari na sab'a ba sai sau d'aya, shima a kanki ne nace wa mama na barki amma Abba ya bani zab'ina tunda yason ina sonki" yayi shiru yana sake kallon ta kafin yace, "Tunda na d'auki alƙawarin bazan barki ba Muwaddaty bazan tab'a barin ki ba kawai kafin nazo inda kike ne za'a jima but ina tare dake ko yaushe a kuma ko ina."
Tana kallon idanun sa tace, "Nayi tunanin hakan, tun can Cairo lokacin da kuka fito kai da Mama ina zaune naga kayi mata magana ta barka kazo inda nake na d'auka zaka yanke igiyoyi guda biyun ne sai naji ka furta ka mayar dani har yanzu ni matar kace, kafin na farga naga ka tafi tun a sannan na saka a raina kamar baza ka karya alƙawari ba amma daga baya sai kawai naga kayi min haka ne dan ka wanke min zuciyata amma bawai dan zaka dawo gare ni bane."
Kai ya girgiza ya goge mata hawaye cikin muryar sa mai sanyi yace, "Bana alƙawari na sab'a Muwadda, in na barki a wannan lokacin da kika fara qaunata na cutar dake har abada Allah bazai yafe min ba kema kuma haka." Cize bakin sa yayi ya kulle ido ya buɗe yana kallon ta idanun sa sun koma jajaye itama kallon sa take. Matse hannun ta yayi a cikin nasa tana kuka tace, "Shiyasa na kasa fad'a a gida, zuciyata tana rawa ne wani b'angaren yace na sanar dasu ka sake ni wani b'angaren yace kar na fad'a tunda ka mayar dani duk da nasan mayarwar bata da wani amfani sabida Mama. Umma ta lura da bani da walwala ta tambaye ni nak'i fad'a mata har na b'ata mata rai tace bazata kuma tambayata ba."
Ta sake kwanciya a kafaɗarsa tace, "A lokacin da abin ya faru badan Dr Khalifa ba ban san inda zanje ba ga security sunce saina fita ance musu ni mai laifi ce ga kaina yana min ciwo" ta fad'a da kuka tana cusa fuskar ta a kafad'arsa.
Shiru baiyi magana ba yana bubbuga bayanta a hankali shud'ewar wasu mintina kafin yace, "Haushin ki na farko dana fara ji kenan Muwaddaty, meyasa kika bi Khalifa bayan kin san bazan tab'a tafiya na barki ba? Meyasa kika bari Khalifa ya rik'e ki a lokacin da zaku bar wajan?. Kin san zafin da naji a raina kuwa?."
"Bani da zab'i ne sai na binsa Sultan, in ban bishi ba ina zanje? Ban san kowa ba ban kuma san ko ina ba sai kai kawai gashi an raba ka dani ina zani?. Dole ce ta saka na bishi gidan sa kuma rik'e ni da yayi ban sani ba Sultan sabida bani da lafiya a lokacin."
Shiru ya sake yi na wani lokaci yana sauke numfashin sa kafin yace, "Muwadda baki sanshi ba sai da kika je Cairo, meyasa kika amince har ya kaiki gidan sa? Da yayi miki wani abun fa?" Ya furta a kausashe yana d'ago da ita daga jikin sa yana kallon ta tare da rik'e hannayenta duka biyun. Idon sa take kallo ta saukar da nata k'asa tace, "Ni kaina hankalina bai kwanta ba sai da matar shi ta dawo, Sultan in ban bishi ba wa zanbi a wannan lokacin? Bani da kowa fa sai kai kad'ai ina zanje?."
Kai yake girgiza mata yana rik'e da hannunta tana kallon sa ya cize bakin sa ya sauke ajiyar zuciya idanun sa sun tara ruwa kamar zaiyi kuka amma baice komai ba. Shiru ya sake ratsa su kafin yace, "Naji wannan. Meyasa kin san da aurena a kanki kike kula wancan banzan mijin k'anwar taki? Kina da aure fa kike sauraron sa hards maganar aure tsakanin ku, meyasa Muwaddaty?."
Tace, "Sabida ban san da aure a kaina ba a lokacin na kammala iddar ka ta saki ukun da kayi min, kar ka manta a lokacin na d'auka kaine kazo ka bani takardar saki biyu ban san Aliyu bane ba. Ummana tana so taga nayi aure sabida abinda ya faru dani wata d'aya da yin aurena ya mutu na dawo gida da zama ana ta wayo dani a dangi da unguwa daman kwad'ayi ne da son abin duniya in ba haka ba ina kai ina ni?, harda wanda suke tarar Ummana face to face suna cewa Allah ya k'ara dalilin da ya saka na amince zan aure shi kenan."
Kallon ta yake yi hakan ya saka tace, "Ban san ba kai bane ba, duk wani abu da zai tabbatar min kaine na ganshi a tare da Aliyu Sultan, hatta wannan zanen daka nuna min na hannun ka na ganshi a hannun sa. Ya kira ni Muwadda cikin voice d'in da kake fad'ar sunan, na fad'a maka komai dana san nida kai kawai muka san dashi ya fad'a taya zan d'auka ba kai bane ba? Hatta yadda kake hugging d'ina yayi" ta fad'a murya na rawa.
"Subahanallah!" Ya furta yana cize bakin sa jin kalaman ta na k'arshe ya sauke numfashi mai k'arfi ya matse mata hannu sosai yana jin kamar ya goge kalmar da ta fad'a cikin tarihin rayuwar su amma bazai yu ba.
Rauda ta kuma cewa, "Ba nice na haife ku ba dole na d'auka kaine yadda yayi min magana da rauni sai na sake tabbatarwa kaine Sultan domin ta ko wacce fuska a yanayin ka yazo. Dalilin dawowar sa rayuwata kenan da niyar aurena a karo na biyu bani da zab'in da ya wuce amince masa dan ni da farko ban so ba makaranta naso na koma Umma ta nuna min auren take so nayi shiyasa na amince."
Ya sauke numfashi yana kallon sama yayi shiru itama tayi shiru tana goge hawayen idanun ta.
"A ranar kika tsane ni ko?." Jin yadda yayi maganar sai ta kalle shi ya juyo shima ya kalle ta ta d'aga masa kai tace, "Tabbas a ranar naji ina ma ban tab'a sanin mai iri Sunan ka a duniya ba, nayi dana sanin sanin ka na kuma yi dana sanin mallaka maka kaina da nayi a wannan lokacin, na tsinewa zuciyata da ta fara son naji kamar na cire zuciyata na cillar sabida abinda nake ji a cikinta. Na haƙura na mik'awa Allah komai abinda ya sake b'ata min rai rushe gidan mu daka aiko ayi, na fusata sosai tsanar ka ta ninku a raina nake ji da ina da iko dana zo har cikin fadar da kake na tsinke ka da mari na fita. Hydar shine ya daidaita komai a lokacin amma duk da hakan ban daina jin haushin ka ba."
Yayi murmushi kad'an yana kallon bango tare da lumshe idanun sa amma baice komai ba sai dai yana sauraren dukkan abinda take cewa. Shiru itama tayi ta goge idanunta ta mayar dasu ta kulle yana ajiyar zuciya.
"Duka kinyi min hukunci ba'a kan laifina ba, bazan iya rabuwa dake ba Muwaddaty, bazan iya sakawa a yiwa kowa abinda Hydar ya saka ayi akan gidan ku ba balle ke, ko babu ke Umma da Baba ina musu kallon iyayena bazan iya ganin an yiwa wanda ya shafe su ba balle ke Muwadda" yayi shiru yana ajiyar zuciya idanun sa a kulle sannan yace, "Kika tsane ni kina jin haushina duka kuma bani nayi miki laifin ba, in na tuna kin tab'a tsana ta a duniya ina jin duniyar tayi min zafi" ya fad'a yana rik'e jijiyoyin kansa da suke harbawa da sauri sabida halin da yake ciki.
Rauda tace, "Ban san ba kai d'in bane ba Sultan a ganina kabi umarnin Mama ne ka yanke duka alaqar dake tsakanin mu dalilin sakin da sake yi min kenan." Ya sake kallon ta na wani lokaci ko kifta idanun sa bayayi kafin ya janye idon sa ya sake sauke numfashi yace, "Tunda kika baro Cairo duk motsin ki na sani Muwadda, ko fita kikayi kikaje wani waje sai an sanar dani. Ko lokacin da na bar Nigeria na koma Bahrain da zama ina bibiyar ki, abinda akayi min ya karye da tasirin addu'a da kuma tasirin aure da naji ance zakiyi, hankalina ya tashi sosai har sai da na dawo Nigeria shine na saka aka d'auko min ke Muwaddaty."
Jin yayi shiru sai sake matse ta da yayi a jikin sa ya sakata sauke ajiyar zuciya itama kusan minti biyu suna a haka kafin yace, "Amma da kika zo sai naga kin canja kina ta min fad'a da rashin kunya na rasa gane me kike nufi Muwaddaty, a wannan lokacin banyi niyar maki komai ba wani dalili ne ya gifta har hakan ta kasance." Ta kalle shi tace, "wanne dalili ne?." Ya sauke numfashi ya kalle ta ya rik'e fuskar ta yana kallo yayi shiru kamar bazai kuma magana ba.
Har ta fitar da rai bazai ce komai ba sabida d'aukar lokacin da yayi baice komai ba kafin ya kai bakin sa idanunta yayi musu kiss kafin ya sake rik'e hannunta yace, "Ranar da na sake sanin ki a karo na biyu a Cairo Muwaddaty wani ciwo ya same ni wanda bazan sake iya sanin wata mace ba shine dalilin wannan ciwon da kika ga nayi." Rauda ta mik'e daga jikin sa tace, "Amma wannan ciwon da aljanu yayi kama fa, yadda nake maka addu'a kana firgita aljanu ne."
Yayi murmushin takaici yana girgiza kansa ya kalle gefe guda d'aya ya sake yin shiru kamar bazai ce komai ba kafin ya sake kallon ta yace, "Aikin aljanun ne Muwadda, duk dan a raba ni dake." Rauda tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amma mutane basu da tausayi da imani, ina ruwana a wannan lamarin da za'a cutar dakai? In ba'a so ka zauna dani basai ka rabu dani ba lallai sai an cutar dakai?. Ni na rasa abinda mutane suke nema a duniya suka mayar da cutar da d'an uwan su musulmi ba koman komai ba."