← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 131

Sashe 95

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rauda tayi murmushi tace, "Babu komai Anty meye na bada hak'uri dan Allah?." Ramla tace, "Ai dole na baki hak'uri duk yadda muke dake ace ban zo bikin ki ba ai babu dad'i." Rauda tayi murmushi tace, "Wallahi babu komai." Ramla tace, "To na gode da kika karb'i uzurina amarya" ta fad'a da niyar zolaya.

Rauda murmushi ta sake yi kamar tana gabanta daga nan suka cigaba da hira kafin suyi sallama ta kashe wayar ta ajjiye a kan gado nan take kuma sai annurin fuskar tata ya d'auke ta lumshe idanun ta tana jin duniyar gabad'aya tana juya Mata komai yayi mata zafi kanta ya cushe. K'arar wayar tata ta sake ji ta d'ago taga sunan Rahma yana yawo akai nan take gaban ta yayi mugun fad'uwa kamar ta share sai kuma ta fasa ta d'auki wayar ta saka a kunne tace, "Asslamu alaikum."

Daga can b'angaren Rahma tace, "Anty Rauda ashe kin dawo shine baki zo ba." Rauda tace, "Rahma kin san yanayin jikina ba lafiya ce dani ba." Rahma tace, "Haka ne, amma dai ya kamata ace kinzo." Ta sauke numfashi tace, "To zanzo in sha Allah. Amma ban ce ga rana ba zaki ganni dai kawai."
"To ina nan ina jiran ki. Ya jikin?."
"Alhamdulillah."
"Kiyi hak'uri Anty Rauda."
"Hak'uri name Rahma?."
"Na komai ma."

Rauda tayi murmushi tace, "to nayi akan komai d'in, bacci nake ji Rahma sai anjima mayi magana ko a whatsapp." Rahma tace, "shikenan sai anjima." ta fad'a tana yanke wayar ta ajjiye tana sauke numfashi k'irjin ta yana bugawa. Wai jinin ta Rahma ce matar Anas saurayin ta wanda suka jima tare suke burin yin aure ashe Allah bai rubuta ita zata aure shi ba ita ba duk wannan tsahon lokacin mijin Rahma ne ba mijin ta ba.

Hawayen da take rik'ewa suka fara zuba a bayyane tace, "Meye makomar rayuwata? Cikin da ban san uban sa ba.....;eh ban san baban saba Asad ne ko Aliyu ban sani ba" ta fashe da kuka mai sauti harda shashsheqa. Umma da take tsaye tana kallon ta sai zuciyar ta ta karye itama hawaye ya ciko idanun ta dan ita kanta yanzu zuciyar ta tafi bata tabbacin Aliyu ne a tare da ita ba Asad ba.

Da baya ta koma dan baza ta hanata kuka ba ta shiga nata d'akin ta goge hawayen idanun ta tace, "Meye amfanin mutum irin Malam? Meye ribar aure irin wannan, sabida kud'i kayi abinda ya saka jinin ka cikin wani yanayi wanda a shekaru ta yanayin ya girmi tunanin ta. Allah ka kawo mata mafita da sassauci" ta fad'a hawaye na sake sakko mata ta saka hannu ta share ta shiga band'aki.

*☆☆☆*

         Mama tayi sa'a taga Baba malam ta karb'o abinda zata karb'o ta koma gida, ana ajjiye mota aka bud'e mata ta fito taga sarkin mota ya shigo taja ta tsaya har ya ajjiye mota ganin irin kallon da take masa ya saka shi ajjiye motar da gaggawa ya k'araso inda take a guje.

Yana zuwa ya zube yana kai gaisuwa ta kalle shi tace, "Kaine kake fita da Aliyu kwana biyu, ina kake kai shi?." Gaban sa yayi mugun fad'uwa rashin gaskiya ya bayyana akan fuskar sa ya had'd'iye yawu ya fara sosa kai yace, "Ranki ya dad'e" sai kuma yayi shiru.

Mama tace, "Baza ka fad'a ba kenan?." Yace, "Tuba nake ranki ya dad'e, amma ni babu inda muke zuwa tare." Kai ta girgiza tace, "K'arya zaka min kenan ko? Shikenan jeka."
Da sauri yace, "Tuba nake ranki ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ki. Tsakani da Allah gidan sa muke zuwa."
"Mata kake kai masa ko?."
"Ranki ya dad'e wata yarinya ce dai guda d'aya amma bayan ita babu ko wacce mace."

Ran Mama ya kai matuk'ar wajan b'aci ta juya ta wuce ta shiga ciki ya sauke ajiyar zuciya yace, "Na tsallake nata hukuncin sai na jira nasa kuma" ya fad'a kamar zaiyi kuka yana bin Mama da kallo dan da bai fad'a mata ba akwai matsala babba.

Kai tsaye Mama b'angaren Asad ta wuce ta same shi da Hydar kamar yadda ta barsu tana shiga ta k'arasa inda yake kwance ta d'auko ruwan maganin da aka bata ta fara sha masa a fuskar sa da tafin hannu dana k'afa, ta saka Hydar ya d'ago shi ta zuba masa ruwan maganin a baki, kamar wanda aka bawa poison sai ya fara jijjiga idanun sa suna k'afewa suka firfito waje nan take. Hankalin Mama da Hydar yayi bala'in tashi suka rik'e shi dukkan su Mama na kuka tana kiran sunan sa amma har lokacin jikin sa rawa yake bai dawo daidai ba.

Sai da yayi mintina biyu a haka kafin kuma ya lafa sai bacci ya d'auke shi Mama ta sauke ajiyar zuciya tana kuka. Kallon sa take yi ya koma wani iri kamar bashi ba a bayyane tace, "Lokacin da ya nuna min baya son sarautar nan da na k'yale shi da duk hakan bata faru ba, meye amfanin sarautar da babu lafiya a cikin ta? Asad ya koma kamar bashi ba kalli yadda ya koma kamar wanda ya shekara goma yana ciwo. Ka yafe min Asad" ta fad'a tana kuka sosai Hydar yana gefen ta yana goge hawaye.

"Lokaci ya k'ure miki Rabi'atu!" Aka fad'a ana shigowa d'akin ita da Hydar suka kalli k'ofar dan sun san dai babu wanda ya isa ya shigo b'angaren. Mai martaba ne ya shigo da kansa bayan sa Uncle ne ya kalle su ita da Hydar sai yayi murmushi Hydar ya k'arasa inda yake yace, "Abbana." Kallon farin cikin da yake kan fuskar Hydar yayi sai ya girgiza kafad'ar sa yace, "Mazan gaske, sannu da k'ok'ari." Hydar yace, "Ina farin cikin samuwar lafiyar mai martaba, Allah ya k'ara lafiya." Uncle ya amsa da amin.

Mama ta sunkyar da kanta k'asa ya Mai martaba ya kalli Asad da yake kwance a kan gado yace, "Hydar ban amince a fita da Asad wata k'asa ba zaman sa a nan nake so." Hydar ya kalli mahaifin nasa ya kalli Asad d'in da yake kwance amma babu damar musu sai yace, "duk abinda kace daidai ne." Mai martaba ya kalli Mama yace, "Ki daina saukar da kai Rabi'a lokacin saukar da kai d'in ya kusa amma ba yanzu ba. Bama ke kad'ai ba duk wanda ya shuka tsiya a bayan idanuna lokacin girbewar sa yazo."

Shiru sukayi babu wanda yayi magana kafin yace, "duka mutanen gidan nan nake so a tattaro min duk wanda ya shafi gidan nan a had'o shi gobe in Allah ya kaimu ina son magana da kowa. Ina matar Asad?" Ya fad'a yana kallon Hydar. Hydar yace, "Tana gidan su wai bata da lafiya."
Mai martaba yayi murmushin takaici yace, "Matar sarkin katagum guda ace tana gida bata da lafiya. An cutar da masarautar nan an b'ata mata suna an lalata garkuwar ta, amma yanzu lokacin gyaruwar tane."

"Ina so aje azo da ita da mahaifiyar ta a goben, hatta tsohuwar matar sa wacce uwar sa ta raba su ina so na ganta a taron gobe ita da nata iyayen. Iya iyalan gidan nan nace a gayyato bance a gayyato min kowa ba, masu tunanin na nakasa bazan sake motsi ba gobe zasu tabbatar da har yanzu da lafiyata. Hydar kaji me nace?" Hydar yayi firgigit ya kalli mai martaba hankalin sa gabad'aya yana ga Asad yace, "Naji ranka ya dad'e, in sha Allah za'a yi abinda aka umarta."

Kai ya d'aga ya k'arasa inda Asad yake ya dafa kansa yaji yadda kan yake harbawa a guje ya kalli Mama da robar maganin a hannunta ya girgiza kansa har zai magana sai ya fasa ya fita Uncle da Hydar suka take masa baya kowa da abinda yake cikin zuciyar sa hatta Mama da take tsaye wannan taro da za'a had'a ya tashi hankalin ta sosai ba kad'an ba.

*Gobe akwai kura kenan*💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼🤣🤣🤣
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: *Arewabooks@nanahaleema11*
*076.*

           Da kallo Mama tabi mai martaba k'irjin ta yana dokawa jin ya ambaci Rauda babban tashin hankalin ta bai wuce ita kuma me zatayi a taron da ya shafi iyalan cikin gidan su?. Bata da bakin magana haka ta juya ta kalli Asad da yake kwance ta zauna a gefen sa ta d'ora hannunta a kansa taji har lokacin yana harbawa.

Numfashi ta sauke haka kawai fuskar Rauda ta fad'o mata a yadda ta tarar da ita sai ta samu kanta da fad'uwar gaba har ta dafe k'irjin ta a bayyane tace, "Fad'uwar gaban me nake ji akan yarinyar nan?." Ta dafe kanta da hannu biyu idanun ta a lumshe sai kuma ta d'ago kai tayi murmushi tace, "Rayuwa kenan." Sake juyawa tayi tana kallon Asad ta rik'e hannun sa tana jin wani irin d'aci a zuciyar ta.

           B'angaren mai martaba yana fita daga b'angaren Asad jama'ar gida da suke so su  tabbatar shine kowa ya zube ana gaishe shi ana mamakin samuwar lafiyar sa lokaci d'aya ba wanda yayi tunanin hakan. Amsawa kawai yayi ya shiga b'angaren da yake bayan ya shiga d'aki Uncle yace, "Amma ranka ya dad'e sai nake ganin kamar anyi kuskuren bayyanar da samuwar lafiyar mai martaba ga iyalan gidan nan, akwai wanda baza su so hakan ba za kuma su so ace mai martaba ya sake kwanciya ciwo."

Mai martaba ya zauna a gefe ya kalle shi yayi murmushi yace, "Mubarak kenan, dukka masu kawowa lafiyata farmaki a yanzu babu wanda ban gano shi ba, duk wanda yake a gidan nan kallon sa nake hatta Asad d'in ya bani mamaki matuk'a ban d'auka haka abin zai kasance ba da banyi gangancin damk'a amanar mutane a hannun sa ba."

"Ranka ya dad'e amma sai nake ganin Asad kamar sharrin sihiri ne a tare dashi." Mai martaba ya sake yin murmushi yace, "Akwai sharrin sirihi sannan kuma akwai....." Sai kuma yayi shiru sai yace, "Allah dai ya nuna mana goben akwai abubuwan da dama da zaku sani wanda zuciyar ku sai ta motsa da junsu, in ba'ayi sa'a ba wasu zasu suma na wucin gadi." Sai ya sake yin murmushi yace, "Akwai kuma wanda baza su so na kai goben da rai ba."
Chapter 95 · 0% Book details