Sashe 28
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
B'angaren Mum tana katse kiran key ta d'auka na mota da hijjabi ta sauka k'asa har zata gota kitchen d'in ta sai taga y'ar aikinta ta juya tana aikin nama ta k'are mata kallo tace, "Safiya." Ta juyo tace, "Na'am Hajiya."
"Baki saka pad bane naga kayan ki sun b'aci da jini?." Gaban Safiyan ya fad'i tasan Mum bata san k'azanta tace, "Wallahi ban sani bane Hajiya." Mum tayi tsaki tace, "dallah wuce ki bawa mutane waje, abincin in baki dafa ba kar ki dafa in kuma kin dafa ku cinye iya ku kije ki sake wanka ki shirya kanki then kiyi mana wani abincin."
Safiya tace, "To Hajiya." Mum har ta wuce sai wani tunani ya fad'o mata ta dawo da baya tace, "Jeki ki saka ki canja rigar jikin kizo." Da sauri ta wuce Mum ta shiga kitchen d'in ta bud'e fridge ta d'auko kwalbar flavor ta k'arasa wajan naman ds take wanke ta d'aga naman taga jini ta tsiyaya a kwalbar tana rik'e dashi ta fito har Safiya ta fito ta kalle ta tace, "kifa shirya kar ki b'ata min mota."
"Na shirya" ta furta a sanyaye Mum tayi gaba ta bita a baya suka shiga mota suka fita.
Tafiya suke har suka zo daf da gidan su Rauda daga can nesa ta tsaya ta kalle ta tace, "Karb'i wannan ki shafa a hijjabin ki ta baya." Karb'a tayi ta juyo da hijjabin tayi yadda tace ta kalle ta tace, "ki fita ki shiga gidan nan b'angaren haggu ki gaishe su kice dan Allah zaki gyara kanki ne kina hanya yazo miki baki sani ba, in sun baki hijjabi ko wani abun ki karb'a ki tawo ina nan ina jiran ki. In kika yi aiki mai kyau har suka baki kina da kyauta." Da to ta masa ta fita ta nufi cikin gidan Mum ta bita da kallo ganin yadda hijjab d'in ya lalace sai ka d'auka da gaske jinin ne.
Da sallama ta shiga b'angaren Umma tana zaune ita kad'ai Umma ta amsa Safiya ta durk'usa tace, "Ina wuni Hajiya." Umma ta murmusa tace, "lafiya lau."
"Taimako na shigo nema Hajiya, ina hanya ne naji zubar bak'on wata na ba tare da na shirya ba duk ya b'ata shine na shigo na gyara kaina in da hali." Umma tace, "Ayya, muje na kai ki band'aki" ta fad'a tana yin gaba tana binta a baya har d'akin su Rauda ta shigar da ita tace, "Ga band'aki nan ki shiga."
"Na gode Allah ya saka da alkhairi" Umma ta amsa da amin ta fita.
Kamar gaske Safiya ta shiga band'aki ta jika hijjabin jalaf duk a son ganin ta burge uwar d'akin ta ta fito ta saka shi a haka a wannan lokacin Umma ta shigo ganin haka ya saka tace, "Haba ke kuwa y'ar nan ina ke ina saka hijjabi mai danshi haka? Cire gana y'ata da bata nan kiyi amfani dashi yafi duhu koda wani abun ya zuba a jikin sa ma babu lallai a gane" ta fad'a tana bata maroon d'in hijjabi wanda tsahon sa ya wuce guiwa.
Safiya ta karb'a tana godiya tace, "Allah ya saka da alkhairi Hajiya ya biya ki. Zan dawo da hijjabin da na koma gida in sha Allah."
"Amin. Kar ki damu ki rik'e ma kema ai kamar y'ata kike. Ya sunan ki?."
"Allah ya saka da alkhairi. Suna na Safiya." Umma tace, "Ashe kakata ce shiyasa kike tsohuwa." Safiya tayi dariya daga nan sukayi sallama Safiya ta fito ta nufi motar Mum.
Tunda Mum ta hango ta da sabon hijjabin tayi ajiyar zuciya cikin farin ciki take kallon ta har ta shiga motar ta cire ta mik'awa Mum tace, "ga wannan ta bani tace na y'ar tane da bata nan." Mum tayi dariya ta karb'a ita kuma ta zauna babu hijjabin tace, "na gode Safiya, naji dad'in abinda kika yi min muna komawa gida zan baki kyauta ta ban mamaki." Safiya taji dad'i ta dinga murmushi a haka suka koma gida ta sauke Safiya ta sake buga motar ta sai gidan Sarki.
Mama na kashingid'e a falonta na ciki taga shigowar ta ta bita da kallo tace, "ya kika yo nan kuma bayan aikin da yake kanki?." Mum tayi dariya ta ware hijjab d'in tana nuna mata tace, "Har na kammala ai, kin sanni indai akace a kan abinda ya shafe kine ba wasa." Mama ta tashi zaune sosai tace, "ban fahimta ba me kike nufi?."
"Har na saka an kawo min hijjabin ta."
"Bana son wasa Sadiya." Mum tayi murmushi tana zama tace, "Wallahi ba wasa nake ba ranki ya dad'e wannan hijjabin tane."
Mama ta kalleta ta kalli Hijjabin tace, "ta yaya har kin samo ko cikakken mintina talatin bamuyi da maganar ba?." Nan Mum ta warware mata komai Mama tayi dariya tace, "Shiyasa a koda yaushe nake sonki Sadiya, basirar ki bata yara bace." Mum tayi murmushi tace, "da zafi zafi ake dukan k'arfe."
"Gaskiya ne. Yanzu za'a kaiwa malam shi kuma ya aiwatar da aiki a kawar da ita har lahira."
"Shikenan magana ta k'are mu huta da tashin hankali" Mum ta fad'a da murmushi Maman ma murmushi take na farin ciki kafin tace, "Wa zan samu ya mik'a masa yanzun nan?."
Mum tace, "meye amfanina ranki ya dad'e? Bara kiga" Ta fad'a tana d'aukar hijjabin ta fita da sauri Mama tayi shewar farin ciki maganin matsalar ta yazo kusa-kusa.
*Hajiya Mama kenan*😊
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*040.*
Tunda Asad ya fita daga d'akin da take bayan an yanke kiran sa da Mama bata kuma ganin sa ba har akayi sallar i'sha, bayan ta tashi daga bacci wanka ta kuma yi kamar yadda Yaya Ummi take yawan fad'a mata akan yawan yin wanka, sosai taji dad'i zazzab'in jikin ta ya sauka sai ciwon kai kad'an ta kuma shan magani tayi sallah ta zauna a d'akin ta kira y'an gidan su suka gaisa. Bayan ta gama wayar ta gaji da zaman d'akin hakan ya saka ta fito falon ta zauna tana kallon tv.
Remote ta d'auka tana dubawa dan ba sanin kan TV tayi sosai ba duba da bata taso da ita a gidan su ba ta canja ta mayar mbc bollywood suna haska film d'in kalank. Film din ya burge ta ganin na sarauta ne kuma ba'a jima da farawa ba ta fara gani tana fahimtar wasu abubuwan kad'an a ciki. Jingina tayi da kujerar dan gabad'aya bata jin dad'in jikinta sakayau take jin ta kamar an cire wata garkuwar da take tokare ta a jikinta.
Film d'in ya d'auki hankalin ta ganin an yiwa yarinyar labarin auren dole an kaita gidan sarauta tana kuka bata so, ji tayi kamar itace jikinta yayi sanyi ta cigaba da kallon film d'in yadda mijin baya nuna mata wata kula sai matar sa hakan ya sake karya mata zuciya amma bata fasa kalla ba ta cigaba da kallon bayan tayi tagumi. Ba zato taji an cire tagumin da tayi ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido ta d'auke idon ta ya zauna a gefen ta ba tare da yace komai ba itama haka ta cigaba da kallon.
Shiru ya ratsa tsakanin su babu wanda yace komai kafin ya bud'e abincin da yazo dashi ya tura mata pack d'in shinkafa da kaza da kuma ice cream da burger da roll d'in shawarma, kalla tayi ta d'auke kai tace, "Bana jin yunwa" ta furta tana cigaba da kallon ta ba tare da ta kalle shi ba. Pack d'in shinkafar ya bud'e ya d'auki spoon d'in ciki ya cika shi ya kai bakin ta, kallon sa tayi ya d'aga gira idanun sa a cikin nata sai ta sauke kai k'asa Allah ya sani bata son kallon idanun sa bari ma yanzu da take jin kunyar sa.
"Na k'oshi fa" ta fad'a da shagwab'a idanun ta a k'asa. Bai janye abincin ba ta sake kallon sa taga still ita yake kallo ta sauke k'aramin numfashi ta bud'e baki a hankali ya zuba mata a baki tana taunawa a hankali gabad'aya bata jin d'andano daman kuma ga abincin larabawa babu isashshen maggi a cikin sa. Dak'yar ta had'd'iye ya sake debowa ya sake kai bakin ta ta sake karb'a tana yamutsa fuska kwata-kwata abincin baiyi mata ba.
A karo na uku kafin ya debo tace, "dan Allah ka bari wallahi bana jin dad'in sa baki na babu taste ga kaina ciwo yake" ta fad'a idanun ta na kawo hawaye ta mayar da kanta cinyar ta hawaye na sakko mata. "Ohh Muwaddat! Meye na kukan?" Ya fad'a a sanyaye yana kallonta ta tashi ta goge idanun ta tace, "Ba kaine ba nace na k'oshi kana sake bani, bana jin dad'in bakina" ta fad'a cikin shagwab'a. Ture pack d'in yayi alamun shikenan an bari. D'an shiru yayi kafin yace, "muje kiga Dr" ya fad'a yana niyar tashi tayi saurin rik'e hannun sa ya kalle ta tace, "Basai munje ba."
Da kansa yayi mata alama da meyasa tace, "Bana so ne kawai, kuma naji sauk'i." Komawa yayi ya zauna na wani lokaci kafin ya saka hannun sa ya rik'e kanta yaji ba sosai yake harbawa ba ya dawo da hannun sa wuyan ta yaji babu zazzab'i a jikinta ya kalle ta yace, "What do u want? Fad'a min ko meye I will give it to you." Lumshe ido tayi hak'ik'a in yayi magana kome girman ka da ajin ka sai kaso ya sake maimaitawa sabida yadda maganar take fita daki-daki da wani salo ba hayaniya sai kwantar da hankali da saka nutsuwa a zuciyar mai sauraron ta musamman ita da zuciyar ta take da rauni a kansa, bud'e ido tayi ta saukar k'asa bata ce komai ba itama.