← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 116

Sashe 99

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu ma mama na ta shirin su kwanta, ruma ta sha magungunan ta, tana ta shafa dogon gashin jaririnta, tana kallon dogon hancinsa.

"Meyasa ka yi kama da babanka, dama babarka ka yi kama, da ka fi haka kyau boy na" ta yi maganar tana kissing
in sa a goshinsa, tana murmushi da jin soyayyar Sabir na shiga zuciyarta.

Yaya Abubakar ya dubeta ya ce "Mama boy, zan tafi gida, gobe in Allah ya kaimu zan biyo mu yi sallama, zan koma school zamu fara exams".

Ruma ta
ata fuska ta ce "Dan Allah kar ka tafi, bana son ka tafi".

"Ki hi ha
uri, exams
in nan ce zata saka na koma, ba dan haka ba a kusa da ke zan kasance in ta kallonki gudan jinina"
Ta yi murmushi ta ce "Allah ya bayar da sa'a"
Mama ta ce "Ka zo ka tafi kar ka yi dare"
"To mama, ban gaji da ganinku bane" kan mama ta yi magana Adam suka shigo.

Ruma ta kawar da kai tana fa
in "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" domin ta gaji da ganin takawa, da kullum sai ya zo sau biyu, kuma duk zuwa sai ya
aga mata hankali a kan ta gaya masa in da Aisha take.

Ba ta
ara ha
e rai ba sai da ta ga Jabir, sarai ta gane shi, da shi aka ha
a baki Adam ya
aukota yayi mata wula
anci.

Cikin girmamawa suka gaisa da ammi, yayin da jabir ya
urawa rumaisa ido, da ta ha
e rai.

Suka gaisa da Abubakar ma, da yake tsaye yana shirin tafiya.

Mama ta ce "Ana ta
awainiya da rumaisa fa, mun gode sosai Allah ya yi albarka, ya shiga lamarin ka ya kareka da ga sharrin ma
iya".

Adam ya ce "Bakomai mama, yi wa kai ne, ki daina godiya ma, addu'a muka fi bu
ata"
Rumaisa a ranta ta ce "Ji shi, wai mama sai ka ce babarsu, dan tsabar kuturun iyayi, wallahi mamanmu ce kawai" ta yi maganar a zuciyarta.

Abubakar ya ce "Ruma baki iya gaisuwa bane?"
ago ta ce 'Au wai ba
i mama ta yi, sannunku"
"Ya jiki kuwa?" Jabir yayi maganar yana kallon ruma.

"Da sau
"Ai da yake ban san meyafaru ba, sai yau, shiyasa bamu zo da shi na dubaki ba, mu ga jaririn"
Maimakon ta mi
o shi, sai saka hannu ta dafe shi, tana harare-harare.

Abubakar ya matsa ya
auko masa jaririn, ya bashi sannan ya fara yi wa ruma mita "Wai ke wace irin yarinya ce ne?

Ke shikenan ba wanda zai ta
a yaron nan sai ke, ke da kece uwassa ban san yadda za'ayi ba".

"To ai nice mamansa, ai dai bar mini shi ta yi".

Ya ce "Ke tafi can, ke ma
in ai Haryanzu rainonki ake yi, mama bari na wuce na je gida na ha
a kayana"
"Yaya Sadik, sai da safe ka gaishe da su"
"Ba yanzu duk suka tafi ba, duk kuna tare sai da safe, ban da yi wa mama rigima dan Allah, a bari sai mun zo mu ayi mana" murmushi ta yi Abubakar ya kama hanya ya fita.

Jabir ya zubawa yaron ido, Adam da ke zaune a gefensa ma, ya zuba masa ido yana sa
a abubuwa daban daban a ransa.

Mama ta juya tana amsa waya, ruma ta lalla
a a hankali ta sauko daga kan gadonta, ta saka hannu ta
auke jaririn daga hannun jabir, a gabansa ta ce "A'uzubi kalaimatillahi tammat" ta
arasa gadonta ta kwantar da jaririnta, ta hau gadon tana ta ha
e fuska.

Adam ya
an kalli jabir, kallon irin ka gani ko?.

Jabir ya girgiza kai ya ce "Rumaisa, na ji duk abun da ya faru, ina fatan Allah ya tsare gaba, amma yakamata ki bayar da ha
in kai wurin ku
utar da maman yaron nan in dai kina
aunar
an ta da gaske, da haka zaki tabattar mana son gaskiya ki ke wa
an ta".

A wula
ance rumaisa ta kalli Jabir ta ce "An gaya maka ina abu dan na burge mutane ne?

To kar Allah ya sa ku yadda
in mana ina ruwana, wata
ila shi sai in gaya masa kai ban gaya maka ba, mugwaye kawai, kuma ni ba dan ta bar mini jaririn nan ba, ba abun da zan yi da
an ku, dan ni bana ko
aukar yara, idan aka bani ri
a ma, mintsini yake sha da cizo, wannan kuwa
ana ne, ba wanda ya isa ya
wace mini shi ehe" ta yi maganar tana fari da murgu
a baki".

Jabir ya ce "Kan uba, haka ki ke?"
"Ai na fi haka ma, idan kun gama zaman kwa tafi, ko ku cigaba da zaman jirana in gaya muku in da take,
tun da ni na saceta" tana gama maganar ta juya ta kwanta.

Jabir ya ri
e ha
a yana jinjina kai, Adam kuwa tuni ya fusata ya tashi fuuuu ya bar
akin, a waje ya tarar da mama yayi mata sallama suka wuce.

A mota Jabir yake cewa Adam "Ban ta
a zaton azabar taurin kan yarinyar nan ya kai haka ba, ji yarinya
arama da iya shege".

"Shawarar da bashir ya bayar, ita ce last option
ina, idan ta
i ba da ha
in kai, zan yi abun da ba ta zato" a haka suka tafi gida suna tattaunawa.

Washegari da safe Ammi ta shirya, zata asibiti Nusaiba da Iman sun so bin ta, amma ta ce a'a su yi ha
uri ba yanzu ba, ta saka aka she
a girki, ta saka a mota, tana shirin shiga motar su tafi, ta ji yo muryar Mummy "Giwa, waye Babu lafiya ne na ganki da kulolin abinci da safiyar nan?

Ko wani ne a cikin yaran amma ki ke
oye mini?"
Ammi mamaki ne ma yakamata, ya aka yi ta fito da sassafe haka, har ta ganta.

'Ba
aya yara duk suna lafiya, wani abu ne mai muhimmanci" daga haka Ammi ta shige motar, ba tare da sake tanka Mummy ba.

Mummy ta ri
ugu ta jinjina kai ta ce "Lallai ta tabbata akwai abun da ki ke
oyewa giwa, kuma da alama yana da muhimmanci a wurinki, bari mu ga idan na banka
o ko menene in da zaki saka kanki, zan saka a bi bayanki, domin ganin in da ki ke zuwa"
Rumaisa tana jin zuwan Ammi, suna ta hira ita da mama, amma ta yi bakam kamar bacci take yi, alhalin idonta biyu maganar ce kawai ba ta son yi.

Sai da likita ya shigo, sannan ta tashi suka gaisa da Ammi, likita ya duba X-ray
in ta ya ce babu wata matsala, ha
ararin nata ma buguwa ce kawai, zai rubuta mata magani.

Mai sunan baba ma tuni sun zo, tare da Abubakar ya biyo yayi musu sallama zai koma makaranta.

Ammi take tambayar mama ko 'yan biyu ne saboda kamanin da suke yi, ba ta gane su, kawai dai ta lura da
aya yana da fara'a
aya baya yi.

Mama ta ce "Eh 'yan biyu ne, Abubakar da mai sunan babana, shi ne sa, ba ka dariya sai hamma".

Ammi ta yi murmushi ta ce "Tubarkallah Allah ya ray miki, familynki sun burgeni sosai da sosai, rumaisa a yayyen nan naki ki bani biyu mana, na je na
ara da nawa yaran mana, ni nawa duk rasuwa suke yi, saura uku a raye"
Mama ta ce "Allah sarki, Allah ya raya wanda suka rage, ya ji
an wanda suka rasu".

Ammi ta amsa da Amin.

Aka zubawa ruma abinci, Abubakar yana bata a baki, tana ta shagwa
Bashir yayi sallama, da shi da 'yan sanda hu
u cikin uniform.

Ruma ta tsaya cak tana bin su da ido, nan suka gaggaisa da kowa, Ammi ta bi bashir da kallon ko lafiya.

"Maman Boy, ya jiki?

Yau zaki ganni da police, su ne case
in binciken aisha yake hannunsu, dan haka za su yi miki tambayoyi ne" a take rumaisa ta ha
e rai, ta kawar da kanta gefe.
aya daga cikin 'yan sandan ya ce "Baby girl, ki amsa mana tambayoyinmu, zai taimaka mana
warai wurin binciko wanda suka yi garkuwa da ku".

Ruma ta zum
ura baki ta ce "Ni fa bana ri
e abubuwa, na manta komai, likita ya hana ayi mini zancensu"
"Ki yi ha
uri ki bamu ha
in kai, ba zancen su zamu yi miki ba, yaya aka yi aka sace ki?

Yaya aka yi ki ka ha
u da aisha har ta baki jaririnta da
ankwalinta?".

"Ni kawai sace ni aka yi, muka gamu da ita, ta bani yaron, na taho" yanayin yadda ta yi maganar zaka san
arya take yi.
an sandan ya sake nutsuwa ya ce "Ki yi ha
uri ki kwantar da hankalinki, a ina kuka ha
un da ita?"
Kawar da kanta gefe ta yi, irin idan ka gaji ka tashi
in nan.

Duk yadda ya so lalla
a rumaisa sai da ta fara hasala shi, rarrashin duniya amma fafur ta ce ba ta san komai ba.

Mama ta yi kanta da zagi, Abubakar yana lalla
ata amma ta yi mursisi tana hawaye, ta ce ba ta san komai ba ita ta manta.

Mai sunan baba da tun
azu yake jin su bai yi magana ba, sai yanzu ya tashi ya nufi gadonta, ya ture Abubakar shi ya zauna ya kalleta, ta sunkuyar da kai
asa, cikin muryarsa mai razanar da ita ya ce "Kalleni" ta
ago da
yar ta kalleshi.

"Gaya musu abun da suka tambayeki" ta kallesu
aya bayan
aya sannan ta mayar da idonta kansa
ta shiga girgiza masa kai.

Idonta ne ya cika da hawaye, amma ta kasa magana.

Mama ta ce "Ruma ba kya ji ana yi miki magana ne?".

Ammi ta ce "Ku bita a hankali, kar ku tsoratata".

"Ba zaki fa
a ba sai na saka sun saka miki sar
a sun tafi da ke, ana magana kina kallon mutane" yadda mai sunan baba yayi mata maganar cikin hargowa sai da ta tsorata, jikinta ya hau rawa, tana girgiza masa kai.
Chapter 99 · 0% Book details