← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 116

Sashe 83

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jabir ya gyara tsayuwarsa ya ce "Kayi aikinka ko ka
atawa kan ka lokaci, wata
ila akwai dalilin da ya sanya yake yi maka yawo da hankali, ka yi ha
uri ka bi komai a hankali, ka bashi yau zuwa gobe in Allah ya kaimu mana".

Adam ya girgiza masa kai ya ce "No, ba zan iya ba" ya juya zai nufi mota.

Jabir ya ri
o shi ya dube shi ya ce "Bashir amintaccen ka ne, bana tunanin zai yi wani abu da zai yi maka yawo da hankali, ko ya cutar da kai, Please ka bashi ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ne" da
yar jabir ya lalla
a takawa dan ba laifi Adam akwai ba
in taurin kai".

A hankali take motsawa, ta fara
arin juyawa, dan gaba
aya a tunaninta bacci take yi, sai dai ta ji wani irin azabar ra
i a
eyarta, zuwa kanta da wuyanta, a hankali ta tashi zaune tana waige-waige.

Jaririn yana nan in da ya fa
i, yana ta motsawa a hankali yana zura hannunsa a bakinsa, yana ta numfashi sama-sama.

Rumaisa ta zuba masa ido hawaye na zuba daga idonta, haryanzu jikinsa da
azantar haihuwa, duk ya fita a hayyacinsa.

Wani irin jiri take ji, ta kalli in da ta fa
i ta ga jini, na in da ta fasa
eya ta fa
Ta kalli
ugunta haryanzu tana
aure da
ankwalin Anty Aisha da ta bata, ta ja jikinta zuwa kusa da jaririn, ta ri
e hannunsa tana kuka "Ka yi ha
uri yarona, na kasa baka kulawar da yakamata, kaga nima yarinya ce ban san me kake bu
ata a matsayin ka na jariri na, na rasa yadda zan yi mu bar wurin nan, dan Allah kar ka mutu kamar yadda mamanka ta tafi ta barni" tayi maganar kamar tana yi da sa'anta.

A haka cike da tsananin muradin cigaba da rayuwa, ta sake
aukarsa ta mi
e cikin
arfin hali, ta cigaba da tafiya, sai dai ba ta je ko ina ba ta kasa, ta silale ta zauna a jikin wani dutse ta zubawa sarautar Allah ido.

Kamar a mafarki rumaisa ta ga wasu irin dandazon shanu sun cika wurin, ita dai ba ta san ta in da suka
ullo ba, ta hangi mai kiwonsu, yana ta ratsawa ta cikinsu.

A gefenta ta din ga ganin wata inuwa, ta
aga kai sai ta ga wata bafulatana, doguwa do jerin
orrai a kanta, ta kalli rumaisa ta ce "'yar nan dan Allah taimaka mini na sauke
orran nan".

Ruma ta harari matar ta kawar da kai, kamar ba ta ga a halin da take ciki ba, take cewa ta sauke mata wannan uban
waryoyin, can matar ta kuma cewa "Rumaisa da ke fa nake" ruma ta kalli matar cikin mamaki za ta yi magana ta fasa, ta kwantar da yaron, ta mi
e ta kamawa matar suka sauke
orran.

Ta koma ta zauna ta na cigaba da kallon jaririnta, matar ta din ga auna nono, ba tare da kuma tankawa rumaisa ba, can rumaisa ta ce "Dan Allah baiwar Allah ki taimaka mini da ruwa da nono na bawa yaron nan, ni ko ba zaki bani ba, shi ki bashi dan Allah".

Matar ta yi murmushi ta ce "Ai na zata ba zaki kulani ba, na tashi na yi tafiyata".

Ta mi
awa rumaisa battar ruwa, ta kar
a ta
ago jaririn za ta bashi, matar ta kar
e shi ta bashi ruwan, sannan ta bu
e wata
warya ta tsiyayo madara fresh ba a da
e da tasota ba, ta fara bashi, aikuwa duk da bashi da lafiya, haka ya din ga kar
a yana sha, kamar zai cinye da mazubin.

Rumaisa sai murmushi take, ganin ya samu ruwa da abun da zai ci.

Matar ta kalli ruma ta ce "Ba dan halinki ba bari na san miki ruwa ki sha, ruma manyan gari, ruma kaya da yani, gwagwarmaya na gaba ba ta zo ba kuma ba ta wuce ba".

"Wai ke a ina ki sanni?" Ruma ta tambayi matar.

Matar ta yi murmushi ta ce "Ke waye bai sanki ba, kar
i ruwan ki sha, kar kuma ki manta ki kula da amanar da aka baki, Allah ya taimake ki baki mini rashin kunya ba, Kodayake jikin ta
aura yayi la'asar, wallahi da a dajin nan zan barki, amma ki ka taimaka mini, sha ruwan na rage miki hanya " rumaisa ba ta gama gane me matar ke cewa ba, ta kar
i abun ruwa ta kafa kai, sai dai ma
warwa biyu ruwan ya
are ba ta
oshi ba.

Lumshe ido rumaisa ta fara yi, tana jin yadda kanta yake
ara nauyi, ta kar
i yaronta daga hannun matar ta rungume, sai sunkuyar da kai take, kamar ta yi shaye-shaye saboda ji take kamar zata fita daga hayyacinta.

"Ke!ke!

Baiwar Allah me ki ke yi a gefen titi haka?" Rumaisa ji ta yi kamar ta farka daga bacci, ta bu
e idonta sosai, irin zaman da tayi ta rungume yaron a haka take, sai dai a wani wurin ta ganta daban, jeji ne wurin sai dai tana zaune a gefen titi, kwalta
"Me ki ke yi a nan, ina zaki je?"
aga kai ta kalleshi amma ta ba ta kula shi ba.

"Ko dai mahaukaciya ce ne?

Wannan yaron na waye, ni da na zaci tsohuwa ce ashe yarinya ce, daga ina ki ke
an waye a hannunki?"
ana ne" ta bashi amsa.

Mutumin ya ce "A'a ba dai
anki ba, ina hijjabinki, ina ne gidanku?".

"Kai dan Allah ka
yaleni haba" tayi maganar tana neman wurin kwanciya.

"Karki kwanta da jaririn nan a wurin nan, ki gaya mini in da zaki in kai ki".

Ta kalleshi ta ce "Ka san
orayi?".

"A'a wanne gari ne?"
"Tun da baka sani ba Shikenan, na gode sosai" gani yayi kamar maganar da rumaisa take yi, haukacewa ta yi ba a hayyacinta take ba.

Wata dan
areriyar mota ce ta yi parking a wurin da mutumin yake tsaye a kan rumaisa, da tuni mutane suka fara taruwa a wurin.

"Bawan Allah lafiya, meyake faruwa ne?".

Ya kalli na cikin motar ya ce "Wallahi kaga yanzu nake dawowa, na biyo hanya ns ga wannan yarinyar da jariri, ta ma dai
i bari na ga yaron, amma kamar dai mahaukaciya ce".

"A'a dawanau ce ni ba mahaukaciya ba, kai haka ake tainako
ishirwa nake ji, amma ko ruwa bai bani ba yake ce mini mahaukaciya".

Na cikin motar ya
auko ruwan roba, ya fito ya bawa rumaisa, ta kar
a ta ta
are ta shanye shi a ma
warwa uku tayi jifa da jarkar.

Ya kalli rumaisa a tsanake ya ce "Na ji kin ambaci dawanau, ke 'yar kano ce?"
"Eh, dawanau asibitin mahaukata ne, dan Allah idan ka san kano ka kaini, kar jaririna ya mutu, bashi da lafiya" tayi maganar cikin magiya.

Ya ce "Ok babu damuwa, amma Meyasa na ganki a haka?

Ina hijjabinki kalleki futu-futu fa, ga raunuka a jikinki, kalli kanki yana zubar da jini, jikinki babu hijjabi,
afarki babu takalmi, dole ayi zaton ko baki da hankali".

"Kwana kusan sittin fa a dajin nan, saceni aka yi, dan Allah ka tashi ka mayar da ni gida" salallami mutanen wurin suka
auka.

A take ya ciro id card
in sa, ya nunawa mutanen, shi jami'in tsaro ne, dan haka ya ce zai tafi da rumaisa babban asibiti na cikin garin katsina.

Rumaisa ta ce ita fa ba ta so a kaita ko ina sai gida, ya fuskanci yarinyar kafaffiya ce, dan haka ya
yaleta ya ce ta taso sai ya
auki wakilcin mutum
aya su tafi, su tsaya su yi reporting wa police, su wuce da ita asibiti.

Sai dai duk yadda rumaisa ta so ta tashi ta kasa, saboda ji ta yi
affuwanta kamar ba nata ba,
arshe sai
aukarta aka yi aka saka a motar suka tafi.

Sai dai fa fafur ta hana kowa jaririn nan, yana
ame a jikinta, jin abubuwan take kamar a mafarki, Allah ya ku
utar da su, ta din ga jera hamdala ga Ubangiji.

Sai dai rumaisa na sanya ran an kama hanyar kano ne, ta gansu a asibiti, aka zo da wheel chair, aka
orata a kai, nurses zasu kar
i jariri ta ce ba ta san zance ba.

Emergency aka shiga da su, aka yi ta lalla
a rumaisa ta bayar da jariri ta
i, ta ce idan aka matsa mata, ko da rarrafe sai ta gudu daga asibitin.

Kasancewar mutumin da ya tsinceta shi ma ba
an gari bane ba, idanya barta babu wanda zai kula da ita, ya sanya a ka bawa rumaisa
an taimakon gaggawa, ya
au rumaisa tare da rakitar 'yan sanda biyu, suka taho kano.

Suna tafe a hanya rumaisa tana ta surutai, masu kama da na fita a hayyaci, ta ce wanna ta ce wancan, ita dai gata nan kamar mai barci kuma kamar zautacciya.

Ba su suka iso kano ba sai bayan tara na dare, suka biya suka kuma report ga police na kano, aka yi rubuce-rubuce, sannan suka wuce da rumaisa asibiti.

Suna zuwa aka kar
i su rumaisa, da tuni hankalinta baya jikinta, tun a hanya aka sai abin ci aka bata, amma ta
i ci, ba ta ma da nutsuwar da zata ci Abincin.

Aka zare jaririn hannunta, da a yanzu numfashi ma yake neman ya gagare shi, da yawa sai da wasu suka yi hawaye, ganin halin da jaririn
anyen haihuwa yake ciki, cibiyarsa ta ya
une tayi ba
i, jikinsa duk
azanta, aka samo kaya aka saka masa aka wice da shi nursery domin bashi taimakon gaggawa.

Ita kanta rumaisan sai ka kai zuciyarka nesa zaka iya ta
ata, saboda yanayin da take ciki na
azanta da dau
a, ba yadda ba su yi ba su kwance
an kwalin
ugunta, amma aka kasa,
arshe suka
yaleta suka fara kokawar ceto rayuwarta, ita kanta sai da aka saka mata oxygen, saboda sama-sama take numfashi, aka
ebi jininta aka tafi yi mata gwaje-gwaje.

Kusan mintuna uku tana zaune a dining tana ta juya cokali a cikin kofin shayin, amma ta kasa
agawa ta sha ko da sau
aya, sai zancen zuci take.
Chapter 83 · 0% Book details