← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 116

Sashe 50

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hauwwaliya ta kwashe da dariya ta ce "Yi ha
uri, Galadiman da ya rasu gidansa a bayan gidan sarki yake, wani
aton gida gari guda, baki ga katangar gidan ba, doguwa sosai a nan dai gidan yake"
"To kin san 'ya'yan gidan?"
"To meye ala
ata sa su da zan san 'ya'yan gidan, suma 'ya'yan gidan duk a cikin assignment
in suke?"
Ruma ta yi murmushi ta ce "A'a dan Allah in anjima mu je, ina son in ga dokuna"
Haka ruma ta din ga lalla
a Hauwwaliya, suka tafi yakasai, har family house
in su Takawa.

Ruma ta yi mamakin girman gidan, ya fi na Turaki da suka je rannan, suka gama yawonsu suka koma gida.

Yau ma sai magariba sannan Abdallah ya
auketa, suka koma gida, sai dai tun da suka koma gida, ruma take tunanin ta ina za ta ga Takawa, dan ta
udirce a ranta ba zata ha
ura ba.

Sai dai gate
in gidan na su kawai girmansa abin mamaki ne, babu wata 'yar kafa da za ta bi ta shiga, ga masu gadi a zaune a
ofar gidan, da alama shiga gidan ba zai zama abu mai sau
i ba.

Tun da Samha ta koma gida, take tunani a kan abin da Khalifa ya zo mata da shi, dan ba abu ne mai sau
i ba.

Amma duk tunanin da ya kamata ta yi ta yi, shika
ai me mafitar da ya rage mata, dan takawa hankalinsa sam ba ya kanta, idan har ba kawar da ala
ar nan ta yi ba, to ita da Adam sai dai kallo daga nesa, haka zalika sai ta yi
ari wurin takawa su Hajiya Jamila burki a wasu
angarorin dan idan suka nakasta shi, to ita suka yi wa.

Mama ta zauna ta tattauna da yaranta, a
arshe suka amince da a sayar gonar mahaifinsu ta can katsina
a garin
ara, domin yin hidimomin da suke gabansu, masu registration ayi musu, masu exam a biya musu, masu bu
atar jari duk ayi musu.

Sannan still akwai filinsu da aikin gwamnati ya bi ta kai, za a basu diyya.

Sai dai mama ta ce ita tsoron garin nan take ji, kawai ayi waya su sayar
an abin da ya samu da na diyyar a aiko musu, can dangin babansu suka hau mitar cewa mama ta mallake yaran ba ga son su je in da suje,
arshe aka yanke Aliyu zai je.

Yaya Abubakar ya ce "Dan Allah mama idan zai je, ya kai musu ruma, tun da dama exam za su yi, su yi hutu, ko a samu su daina surutun nan da suke yi na rashin zumunci, rabon da aje da ita garin fa tun yaye, rannan da na je baki ga mita da fa
an da suka din ga yi ba, wai kin fiye son 'ya'ya, wayar da muka yi da baba Habu shekaranjiya a kan biyan diyyar nan shi ma ba ki ji fa
an da ya yi ba".

Mama ta ce "Ba
i nake ba, ka san halin rashin jin yarinyar nan shi nake tsoro, ga yanayin garin babu lafiya".

"Mama ai a cikin ido ake tsawurya, in Allah ya yadda babu abin da zai faru sai alkhairi"
Mama ta ce "To, Allah ya sa"
Ruma ta ji dadin batun tafiya da ita garin mahaifinta, amma gefe
aya ta fi son sai ta tafkawa takawa
arna, sannan su tafi yadda zai nemeta ya rasa.

Zaune take a kan kujerar da ke gaban mudubi, tana ta shafe-shafen turare,
amshi duk ya gauraye
akin, sannu a hankali ya tako gabanta yana kallonta.

"Mutum kwalliya sai ka ce aljana" dariya ta yi har sai da dimples
in ta suka lotsa, ta ce "To idan ban kwalliya ba me zan yi?"
Ya saka hannu ya fara jan kumatunta ya ce "Kai na yi missing kumatun nan naki sosai da sosai"
ata fuska ta yi tana sake tura kumatun, shi kuma ya cigaba da ja yana dariya yana fa
in "My Chubby girl".

Tun da aka ce za ayi tafiyar nan da ruma, mama take mata nasiha da ja mata kunne a kan tafiyar da za ayi da ita, a kan nutsuwa da kama kanta, musamman saboda rashin tsaron da yake garin.

Gaba
aya Instagram sun yi banning account
in ruma, dan haka yanzu ba ta hawa Instagram
in sam.

Mama har mamaki take, duk wanda ya ce za shi cikin gari sai ta ce za ta bishi, mama dai ba ta yi magana ba, ta cigaba da zira mata ido, ta gano sintirin me take yi haka a cikin garin nan.

Yau ma haka ta dage sai ta bi Aliyu, Allah ya taimaketa ya tafi da ita.

Bayan sun je, ruma ta faki ido ta fice, ta tafi gidan Galadima, domin aiwatar da abin da ta yi niyya, ta samu napep daga nan mandawari zuwa cikin yakasai.
ofar gidan ta tsaya, tana kallo tana tunanin ta ina za ta shiga?

Cikin dakiya ta tunkari
ofar gidan, masu gadin suka zubo mata ido su ga iya gudun ruwanta.

Gadan-gadan ta nufi shiga, wani
an sanda yayi mata tsawa ya ce "Ke wurin wa ki ka zo?"
an yi jimm sannan ta ce "Wurin wani"
"Waye wanin?".

"Sunanshi Adamu"
Wado ido suka yi gaba
aya suna kallon ruma "Ke!

Baki da hankali?" Saroro ta yi tana tunanin me ta yi kuma?

"Ke haka ki ka ji ana kiransa da shi, zaki zo ki fa
i wannan sunan haka?

Zaki bar wurin nan ko sai mun saka dogarai sun zane miki jikinki"
"Ai ni ban san me ake ce masa ba, dan Allah ku barni na shiga"
"Ke, ba a zuwa gidan nan sai da izini, wuce ki bar nan ko ki jira idan kin nemi izini sai ki shiga".

"To a wurin wa zan nemi iznin?"
aya daga cikin su ya ce "Ke bar nan ko na yi miki duka a wurin nan, ji mini shegiyar 'ya da baki fil-fil kamar robot"
Ta kalleshi ta ce "Ni ba shegiya bace ba, ka daina zagina" tayi maganar idonta
yar a cikin nasa.

Girgiza kai kawai yayi, dan idan ya tunzura sai ya ji
awa yarinyar nan jikinta.

Ta samu wani
an tudu ta zauna, tana kallon hanya.

Suka kunna sigari suna sha, ruma ta kallesu ta ta
e baki a hankali ta ce "An yi asara"
"Ke ki ka kuma hararata sai na miki duka, ki tashi ki tafi ko?"
"Ni dai ba a kanku nake ba, ku
yaleni mana" ta yi maganar tana kawar da kai, tana ji a jikinta ko zata wuni a nan, sai ta ga abin da ya turewa buzu na
Wata dattijiuwa ce ta nufo gidan, suna gainta da fara'arsu suka fara mata magana "Baba Sabuwa, kin dawo?"
"Wallahi kuwa, kun ganni sai yanzu ya aiki?"
Suka amsa mata da Alhamdilillah.

Ruma ce ta taso da sauri tana fa
in "Baba" baba sabuwa ta tsaya ta kalli ruma ta ce "Yarinya ya aka yi?"
"Dan Allah gidan nan zaki shiga?"
Ta ce "Eh, a gidan nake aiki"
"Kin san wani Adamu a cikin gidan?" Hangame baki baba Sabuwa ta yi, tana waige-waige da fatan Allah ya sa wani bai ji ba.

"Ke 'ya ta ai ba a fa
ar wannan sunan a gidajen sarautar kano, takawa ake ce masa, eh na san shi"
Ruma ta yi
asa da muryarta ta ce "Dan Allah abu zan baki, ki kai masa, so nake na ganshi an hanani shiga, amma dan Allah ki bashi wannan takardar hannu da hannu babata"
Baba uwani ta ce "To shikenan, amma in ji wa zan ce masa?"
"Idan ya ga takardar shi zai gane, dan Allah ki bashi "
Baba sabuwa ta ce "to shikenan, zan bashi in Allah ya yarda".

"Ku kuma da baku barni na shiga ba kwa ci kanku"
"Zo mu baki sigari "
ayan ya fa
a cikin iya shege.

"Sai dai uwar sigari" ta fa
a a hankali.

Tutsiye Baba sabuwa suka yi, a kan lallai ta basu takardar nan su duba, kar a shiga da wani mugun abu gidan, amma ta ce ba zata bayar ba.

Baba sabuwa, hadima ce a cikin gidan ita ma, ita ce shugabar hadimai a
angaren Mummy, kuma tana
aya daga cikin masu bata rahotanni a kan abubuwan da suke wakana a gidan.

Tun da baba sabuwa ta shiga gidan, take tunani ta kai wa uwar
akinta takardar su fara dubawa ko kuwa?

Sai dai mummy ba ta nan, dan haka ta sanya takardar a
an tofinta, ta cigaba da ayyukanta.

Ruma kuwa jinta take wasai, kamar an yaye mata wata damuwa da take damunta, tana komawa maman su Hauwwaliya da yaya Aliyu suka rufeta da fa
a, dan babu wanda ya san ta fita, ko a jikinta kasancewar yau tana lissafin sa
onta zai je in da take so, sai Addu'a take Allah ya sa baba Sabuwa ta bayar da sa
onta.

Aliyu ya tasa ta a gaba zuwa gida, suna tafe yana
are mata zagi.

Wajen
arfe biyar takawa ya tashi daga aiki, a gaggauce ya nufo gida, dan yau bai samu zuwa gidan ba sai yanzu.

A gate jami'an tsaro suka sanar sa shi zuwan wata yarinya, da take son ganinsa amma suka hanata shiga gidan, suka sanar masa da ta ba wa sabuwa takarda ta ajiye masa.

Bai kawo komai a ransa ba ya shiga gidan, yana tunanin wacce yarinyar ce haka?.

Yana yin parking ya wuce sashin Mummy, ko da ya shiga falon, Fauziyya ya tarar, jiki na rawa ta yi masa sannu da zuwa.

Bai amsa ba ya ce "Kira mini Baba sabuwa" ta mi
e tana tunanin me yasa yake neman Baba sabuwa a yammacin nan?.

Baba sabuwa ta risuna tana gaishe shi, ya mi
a mata hannu ya ce "Bani sa
ona" babu musu ta fito da takarda ta mi
a masa.

Ya juya ya fice.
Chapter 50 · 0% Book details