← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 116

Sashe 75

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana zuwa ta tarar da Aisha a zaune, idonta
aya ya tara jini, fuskarta duk a kumbure, zaninta kuma na farin leshi, ya rine da jini, sai haki take yi.

"Anty Aisha menene?

Me suka yi miki?" Ruma ta yi maganar da
yar.

Alama ta yi wa ruma da ta
araso kusa da ita, ruma ta
arasa a hankali ta zauna a kusa da ita.

Aisha ta mi
a hannu ta ri
o na ruma, ta
ora a kan cikinta sannan ta ce "Rumaisa, takani suka yi a cikina, kin ji babyna ba ya motsi" tayi maganar tana fashewa da kuka.

Kuka ruma ta saka ta ce "Suwaye su?

Me ki ka yi musu?"
"Ban sani ba, sun ce ba dan su kar
i ku
in fansa suka
aukoni ba, dan su tozarta ni ne, ki yi mini Addu'a dan Allah, Allah ya sa babyna yana raye, na fara jin jiri, na zubar da jini da yawa".

Ruma ta rasa abun yi, ta rungume Aisha suna kuka.

"Zaki iya tashi a rakaki wurin da zaki wanke jikinki?"
Barde yayi maganar yana kallon Aisha.

Ruma ta ce "Ba ta so, mugwaye azzalumai, marasa imani, me ta yi muku?"
Barde ya ce "ke!

Ki daina ganin ina
aga miki
afa, wannan matar ba an
aukota ne dan ayi garkuwa da ita ba, mutanen da suka zo
azu su suka yi garkuwa da ita".

"Wallahi ba zata je ba, ba ta so salon ku kuma yi mata wani abun"
"Shikenan, kun huta".

Aisha ta ce "Rumaisa ki yi sallolin da suka wuce ki, sai ki sakamu a addu'a"
Ruma tayi taimama, ta mi
e ta kabarta salla, dan Anty Aisha ce ta koya mata yadda ake yin taimama, farillanta, da sunnoninta.

Da ta idar da sallar ma kusa da Aisha ta koma ta zauna, tana ta jera mata sannu.
****
Ammi na zaune a kan sallaya tana lazumi, Baba uwani ta fa
o dakinta a hargitse, da har sai da Ammi ta tsorata.

"Tuba nake ranki ya da
e, Allah ya
ara miki lafiya da nisan kwana, tuba nake ki yafe ni, na fa
o miki
aki babu neman iso, wani abu na jiyo da ya girgiza ni, na ga bai kamata na rufe miki ba".

Cikin mamaki Ammi ta ce "Ke kuwa menene haka?"
"Allah ya baki yawan rai, kin san zance a cikin masarauta ba ya rufuwa, ban sani ba ko a hadiman sashin nan ne da basu san meke faruwa ba, ni kin san tun yaranki na
anana muke tare da ke, wani zance na ji yo da ya
aga mini hankali na ce dole na sanar miki".

"Ina jinki, meyafaru?"
"Kin San rashin lafiyar nan ta takawa ba kowa ya san yana fama da ita ba, to jita-jita ta ya
a gari wai shaye-shaye yake yi, yayi mankas yayi yin
urin yi wa iman fya
Ras!

Zuciyar Ammi ta yi wata irin mummunar bugawa, shaye-shaye ga kuma kalmar fya
e da aka jinginawa yaranta.

A ki
ime ta ce "Uwani, a ina ki ka jiyo wannan mummunan zancen?"
"Hadiman gidan turaki na ji suna fa
a, ammma suma wai-wai suke yi ".

"Kenan Samha ce ta je ta fa
i wannan maganar?"
Cikin inda-inda uwani ta ce "Amm...a..a'a ba na tunanin hakan, ban dai san yadda a kai zancen ya fasu a haka ba" Ammi ta ja wani irin numfashi ta ce "Shine, jeki kawai" daga haka ta kasa tofa komai, saboda tsananin tashin hankali.
an barcin da ya saci mama tana daga zaune, ta ji da
insa sosai, dan dama ba iya baccin take yi ba.

Aliyu yana zaune ya na yi mata ninkin kaya, mai sunan Baba kuma yana gyara socket
akin.

A gigice mama ta farka daga baccin, ta mi
e tsaye zata fita, cikin zafin nama mai sunan baba ya tashi ya ri
ota yana fa
in "Ina zaki je ne?"
"Rumaisa ce a waje tana
wasa
ofa zan je na bu
e mata ne".

"Haba, amma ya aka yi mu bamu ji bugun ba, ba kowa fa".

"Kai umar ka sakeni, tana
ofar gida tana bugawa, sai kuka take ni na ganta, kuma na ji bugun".

Umar zai iya
irga sau nawa mama ta kira sunansa da wayonsa.

Ya kwantar da murya ya ce "Mama, yau kuma umar ba baba ko mai sunan baba ba?

Cewa fa ki ka yi kin ganta a waje tana kuka?

Ta yaya ki ka ganta? bacci fa ki ke yi mafarki ne ba gaske ba?"
Sai kuma jikin mama yayi sanyi ta fashe da kuka ta ce "yi ha
uri babana, na zaci gaske ne, yi ha
uri na yi maka tsawa".

Aliyu ya ce
"Mama, tun da ki ka fara mafarkin ruma a
ofar gida tana buga gida, in sha Allah ta kusa dawowa, ina jin hakan a jikina, baki ga Adduoin fa da ake yi mata ba".

Mama tayi murmushi ta ce "Ashe kai ma kana jin za ta dawo, na zaci nika
ai nake ji, dan dai ka
r in dameku ne, ina ma san ranar da zata dawo".

Mai sunan Baba ya girgiza kai ya ce "Shikenan, dama lokacin shan maganinki yayi, zauna in baki ki sha ki kwanta ki huta, Allah ya dawo mana da ita lafiya, ya tsare mana ita a duk in da take".

Kamar
aranar yarinya mama ta ce "Kai ma kana kewarta ko babana?"
"Mama
anwata ce fa, duk halinta jininmu
aya ina kewarta, zauna to" haka ya zaunar da mama da
yar, ya bata magani, dan mama har likitan
walwa liktanta ya bada shawar ta gani, saboda depression na neman kamata.

Tamkar ciwo jira yake dare yayi, ciwo ya tayar wa Aisha, sai dai ta daure ta
i nunawa saboda kar ruma ta tayar da hankalinta.

Ruma da hannunta ke kan cikin Aisha, ita kuma ta ri
e hannun ruma, ruma na kwance lamo ba bacci take ba, can ruma ta ce "Laaa, Anty Aisha wallahi jaririnki ya motsa, baki ji ba?"
yar ta yi murmushi ta ce "Na ji ruma, yana raye Allah ya sa ina da rabon ganinsa".

"Amin, bari in yi musu magana su kai ki asibiti "
Ta ri
e ruma ta ce "
yalesu, ba zasu kai ni ba, na ji sau
i ki zauna mu yi hira"
Ruma ta ce "Ni bana son hirar, so nake na ga kin koma kamar da"
Cikin dakiya ta din ga yi wa ruma hira, tana sakata dariya, amma a
asanta kuwa jini ne yake zuba sosai.

Jin tana cigaba da numfashi da
yar, ya sanya ruma ta tashi, ta tafi wurin 'yan bindigar nan ta ce "Dan Allah sha tara ku kai ta Asibiti, bata da lafiya sosai wallahi"
Duk da duhu ne, ya kunna fitila ya haske in da Aisha take, sai jujjuya kai take, zaninta yayi sharkaf da jini.

A aljihunsa ya sanya hannu, ya ciro wayarsa, ya kira wata lamba.

"Oga, matar nan fa kar ta mace mana, ya ake ciki azo a fita da ita ko zuwa wayewar gari ne"
Ruma ta kasa kunne, sai dai ba ta jiyo me na cikin wayar yake cewa ba.

Sha tara ya kashe wayar ya ce "Da safe za a kaita asibitin, tafi ki kwanta"
Ruma ta tashi ta koma wurin Aisha, tana gaya mata ai da safe zaa kaita asibiti.

Aisha ta jinjina kai, ruma ta ce "Anty Aisha, wai daga ina jinin nan yake fitowa, ko fitsarinsa ki ke yi ne?"
"A'a ruma, amma dan Allah matso in din ga jinki a kusa da ni, jiri nake ji".

Ruma ta matsa ba tare da
yamar jinin ba, ta rungume Aisha.

"Rumaisa ina
an kwalina da na baki?"
"Yana
unguna na
aure shi, na baki ne?"
Ta ce "Yauwwa sannunki baby rumaisa, ina
aunarki sosai"
Ruma da kuka take ta ce "Nima ina sonki sosai Anty Aisha".

"Idan na haifi mace sunanki zan saka mata, idan namiji ne kuma sunan wannan abokin naki da ya ta
a miki
irji, ya ma ki ka ce sunansa?" Ta yi maganar cike da zolaya, da son kunna ruma.

Aikuwa ruma ta ce "Wallahi ba za'a saka masa sunansa ba, ke me yayi miki zafi, zaki saka sunan
an iska, ba gara a saka sunan Barde ba, tun da dai yana bamu abinci"
Ta yi dariya ta ce "To a saka mai sunan Baba"
Ruma ta ce "Kaii, ban baki wannan shawarar ba, fa
ansa ka
ai ya isheki".

Aisha tayi wa ruma wani irin ri
o tana nishi, sannan ta ce "Kawo kunnenki ki ji wata magana".

AYSHERCOOL.
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR
DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO.

SHIN
URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION?

KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE
I KINA HASKAWA?
Chapter 75 · 0% Book details