← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 116

Sashe 23

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruma ta ce "Mama....."
Mama ta katseta ta hanyar cewa "Rufe mini baki, kar ki sake ki yi mini shirme, kuma ki tashi ki yi sallar da ki ka ce baki yi ba dan ubanki"
"To mama ai idan ana bi
i ba a salla"
in ubanki, ke kin san meye bi
in ne?"
"To meye bi
in?"
"Ba zaki tashi ki yi sallar ba, sai na zane ki da bulugarin nan?"
Ta kalli Gwaggo ta ce "To ke gaya mini"
Kamar wadda ta tambayi meye wani babban zunubi Gwaggo ta ce "A'a ni babu ruwana, ga uwarki nan ta baki amsa ni zaki tambaya wannan babban al'amari ba a bakina ba, 'ya'yan binki wayewar ku ta yi yawa".

"Ohh ni ruma, komai na yi laifi ne, ai shikenan"
Tun daga lokacin ba ta kuma kula kowa ba, ta koma tayi shiru wai ita ta ji haushi.

Har zuwa sallar magariba, ba ta sake kula kowa ba, Gwaggo ma ta gaji da yi mata hirar, amma Ruma ta
i saurarata.

Yaya Sadik ne yayi gyaran murya ya ce "Ruma, wai ni kuwa idan kin girma me ki ke son ki zama ne?

Da na je taron PTA
in ku an ce da kun shiga primary 6, za'a fara shirin common entrance, shi ne na ce idan kin shiga Sakandire me ki ke sha'awa Art zaki yi ko science?"
Ta kalle shi ta ce"Wai in din ga drawing?"
"Wane irin drawing kuma?"
"To ai ji na yi ka ce Art, Art ba drawing ba kenan?"
"A'a ba wannan ba"
"Ni dai kawai sana'ar da zan samu ku
i nake so, ko kuma in zama 'yar sanda, in dinga tsayawa a titi ina bada hannu masu mota suna bani ku
i, ko kuma a bu
e mini kanti, ko na zama mawa
iya ko 'yar film!"
Ayshercool
08081012143
A TAIMAKA AYI SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL
INA NA COOL HAUSA NOVELS, KO IN KOMA POSTING SAU
AYA A SATI
[11/07, 4:25 pm] JAKADIYAR AREWA:
ANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing
YouTube channel
@Cool Hausa Novels, domin samun da
an litattafan hausa na sauraro.

Girgiza kai kawai Abubakar ya yi, ya ja bakinsa ya tsuke.

"Yaya ya na ji kuma kayi shiru?"
"To ruma ba dole na yi shiru ba, kowa yana nemawa kansa mafita a rayuwa, amma ke in da ki ka dosa daban?"
"To wai me na fa
a ba dai-dai ba?"
"Yanzu ke tsakanin ki da Allah, kin ta
a ganin mace a titi tana bada hannu a
asar hausa?"
an yi shiru sannan ta girgiza masa kai ta ce "A'a, to mawa
iya fa ko film?"
Abubakar ya ce "Ba kushe sana'ar wani zan yi ba, amma ki yi tunanin wani abun daban"
"To ba sai a bu
e mini kanti ba"
"Yanzu a unguwar nan gaya mini shagunan da ki ka ga mata ne a ciki suke sayar da abu?"
Ta yi farat ta ce "Ga maman Olu beyerabiya"
"To ke bayerabiya ce?"
"A'a amma dai....."
"Kin ga, ya isa haka, dama ni a kan career ki nake magana, tun da baki gane me nake nufi ba shikenan" ita sam ba ta ga aibun abin da ta ce tana so ba, dan haka ko a jikinta ta share.

Gwaggo ta fara shirin tafiya, su Yasir suna ta murna, dan dama duk ta ishe su da fa
a da azabar saka ido.

Shi kansa mai sunan Baba murna yake ta tattara ta tafi ta bar musu gida su huta, dan ta saka shi a gaba da yawa, dan ma Allah ya taimaki Abubakar bai fi sati ba ya koma makaranta.

Amma kullum cikin surutu takewa mama "Hauwwa wannan zagada zagadan yaran naki, duk sun isa aure amma kin tare su a gaba kina ado da su a gida, ga
auye can muna da mata burjik, amma dan mugunta kin tare su kin hana su motsi'
Mama ta ce "Haba Gwaggo, guda nawa yaran suke, haryanzu su Baba basu ha
a talatin ba fa, duk girman jiki ne, kuma kina ganin irin rayuwar da ake sai godiyar Allah, babu mai
warar sana'a sai
arfin hali, idan suka
auko aure da yaya za su ri
"Ba wani nan, idan mutum yayi aure Allah zai warware, amma kallesu dan Allah tuma-tuman gwauraye ki na ado da su a gida, babu mai mata, kalli dai wannan zagaren, sai dai ya shigo fuska kamar bajimin sa, ya zo ya
au abinci ya fita yana zazzare ido kamar wani zaki, ko fara'a ba ya yi, kai haka zaka yi wa matar ma idan an aureka?, ko da yake ma wace macence za ta auri mutum ba fara'a ba komai fuska kamar kunun kanwa ba rahama"
Lomar Abincinsa kawai yake kawai, ko motsi bai yi ba, balle ya nuna ya san da shi take, yana jin ta ya share ta.

Ruma kamar ta kwashe da dariya, jin an ce fuskar yaya Umar kamar kunun kanwa, amma sanin ruwa ba sa'an kwandon ba ne ya sanya ta ja bakinta ta tsuke.

"Umaru da kai fa nake" A hankali ya
ago idanunsa ya yi mata wani irin kallo, ya mayar da kan sa ya cigaba da cin abinci.

"To Allah ya kyauta, ka ma dai mayar da ni mahaukaciya, ka je ka
arata, tattara kayana ma zan yi na bar muku gidan ku, gobe goben nan zan bar garin nan.

A hankali yasir ya ce "Alhamdilillah, Allah ya raka taki gona"
A rikice ruma ta ce "Haba Gwaggo, ni bana son ki tafi, dan Allah ki zauna bamu gaji da ganinki ba".

Huzaifa ya yi
asa da murya ya cewa Abdallah"Ji munafukar 'yar nan, ko a gidan uban waye bamu gaji da ganin na ta ba, mata duk ta addabi mutane?"
Abdallah ya ce "Ashe ka manta wacece ruma, ai wannan yarinyar tsaf sai ta ha
a ya
in duniya na uku, duk abin da ta san za ta aikata wanda ba a so shi take yi"'
Kamar wasa ruma har da kuka, wai kar Gwaggo ta tafi, ji suka yi kamar su yi wa ruma taron dangi su zaneta.

Ganin ruma na kuka, ya sanya Gwaggo ta ce ba zata tafi yanzu ba, saboda ruma.
*****
Sauri-sauri take yi, tana tafe tana duba agogon hannunta, tana daf da makara zuwa wurin da zata.

Tana
arasawa harabar gidan ta
aga murya ta ce "Gali, gani na fito zo mu je na makara"
Cikin girmamawa da murmushi Gali ya taso ya ce "Allah ya taimaki 'yar gaban goshi, Allah ya
ara miki lafiya uwar
akina, ai tun
azu ke nake jira, tun da tun hu
u ki ka ce mini"
"Kai dai bari, na tsaya na yiwa Ammi girkin dare, kar na je ban dawo da wuri ba ka san ba komai take ci ba"
Ya ce "Haka ne, bari na fito da motar" ya yi gaba ita kuma ta tsaya.

'yan mata ne su hu
u, suka fito ta
ofar wani sashi na cikin gidan, suka tunkaro in da take wajen harabar gidan, hakan ya yi dai-dai da fito da motar da Gali ya yi.

Kai tsaye suka tinkari motar ba tare da sun kulata ba, suna
arin bu
ewa su shiga.

Da sauri Iman ta ce "Kai, fita fa zan yi, zai kai ni unguwa ne"
aya daga cikin su ta kalleta ta ce "Saboda ta ki fitar zamu fasa tamu ne?"
Iman ta ce "A'a ba haka nake nufi ba, na ga kun iya driving, kuma ga wasu motocin, ni Ammi ta hanani tu
i ne, kuma na yi magana da Gali tuntuni a kan zai kai ni unguwa"
Cikin tsawa
aya daga cikin su ta ce "Shut up!

Mu ki ke kallo ki ke gayawa haka, kin manta a tuna miki ne?"
"Me ku ke yi haka a tsatstsaye?" Gaba
aya suka waiwaya suka kalli mai maganar.

Jikin Iman ne ya yi sanyi, tare da shiga wani yanayi mai wuyar fassara, bayan sanya idanuwanta a cikin nasa.

Fauziyya ta cire glass
in fuskarta ta ce "Bro, wannan
anwar ta ka ce take yiwa mutane rashin kunya, duk motocin gidan nan ta rasa wadda za ta hau, sai da muka zo muka ce a kai mu unguwa, wai ita ma tilas ita zata hau a fita da ita"
Ya tsuke fuska ya kalli Iman ya ce "Wato ke tsagerancin naki har ya kai ki din ga yiwa na gaba da ke rashin kunya ko?

Sa'anninki ne su?"
Jiki a sanyaye ta kallesu, sannan ta mayar da idonta kan sa, sai dai ta kasa magana, sai hawaye da suka cika mata ido.

"Ina magana zaki yi mini kuka, get out from my sight, stupid girl"
Gaba
aya ta rasa meya kamata ta yi, jiki a sanyaye ta nufi hanyar fita daga gidan.

"Ke zo nan" ta ji muryarsa ba tare da ta yi tsammanin hakan ba.

Ta juyo ta dawo in da yake tsaye.

"Ina zaki?"
"Napep zan je na hau"
"Wuce ki koma, ba zaki fita ba" yayi maganar cikin bayar da umarni.

Ta kalli yadda motar da su Fauziyya suka shiga ta bar gidan.

Ba ta ce masa
ala ba, ta koma sashin su, sai dai duk yadda ta so ta ri
e hawayenta abin ya faskara, tuni hawayen suka wanke mata fuska.

"Subhanallah, abar
aunata ya haka?

Meyafaru? ya baki tafi ba?" Ammi ta yi mata tambayoyin a jejjare cikin ru
ewa bayan ganinta ta na kuka.

Iman ta share hawayenta ta ce "Bakomai Ammi, kawai fasawa na yi"
No ban yarda ba, gaya mini"
"Ammi su Fauziyya ne da Yaya Mahmud".

Nan da nan Annurin fuskar Ammi ya
auke gaba
aya ta ce "Mahmud again?

Tura fa ta fara kaiwa bango, meya yi miki?"
Iman ta share hawayenta ta ce "Ammi dan Allah ki bar maganar, kar ranki ya
aci, bana son ki damu"
Ammi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Na ji, amma me suka yi miki?"
"Dan Allah kar ki damu Ammi, bakomai ki yi ha
uri"
Jinjina kai Ammi ta yi sannan ta ce "Yanzu shikenan, kin fasa fitar kenan?"
Iman ta
aga mata kai alamar eh.
Chapter 23 · 0% Book details