← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 116

Sashe 35

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wunin yau gaba
aya aka rasa mai saurara ruma, duk wanda ta yiwa magana sai ya hantareta gaba
aya haushin abin da ta yi suke ji.

"Hmm huzaifa ni fa Allah ne ya taimake ni, da matar cewa ta yi sai ta dakeni, ka ganta kuwa,
atuwace sosai da sosai fa, a kan benci ta zauna, kaga hannun ta a cure da nama, idan ta dakeni ai ji zan kamar an buga mini guduma"
Usman ya ce "Sai na zubar da ha
oranki, ba zaki nutsu ba ko?, ki ke cigaba sa kwatanta yadda take, ina ma Alin ya bar ta ci ubanki, ke ban da rashin kan gado, kawai ki je ki karya 'yar mutane saboda tsabar wauta ta yi miki yawa, sai ka ce wata rainon ga
a-ga
Aliyu ya ce "Kai ba ka san abin takaicin ba ma, har da wani cewa ai aljanunta ne suka tashi, ba a hayyacinta ta daki yarinyar ba, tsabar cin kai"
Mama ta ce "Ba ku ne ku ke zigata ta
auko magana, ku ka ce kun tsaya mata, dole ta yi abin da ta ga dama ai, kuma daga yau duk wasu tashoshi na wrestling a gidan nan sai an sauke mini su, an daina kallon sa a gidan nan, kai kallon ma sai an daina"
Ruma ta waro ido ta ce "Mama, shikenan sai na daina ganin saurayina na wrestling"
Usman ya ce "Au ke har wani saurayi ne da ke a wrestling
in?"
"Eh mana, ba ka san shi bane, Huzaifa ya ma sunan sa,
an tuna mini, idan na ganshi har wani da
i nake ji".

Huzaifa ya ce "Ke ki ka san shi ni ban san shi ba"
Yasir yayi tsaki ya ce "Wallahi Mama mi bamu go ahead, mu yi wa yarinyar nan ru
iyya ni da Huzaifa, mu samo tsumangiya in cu
a mata jikinta in ha
a da ayar Allah wallahi dolen aljanun na ta su magantu"
"Wallahi ni ba ni da aljanu sai raina ya
aci, kuma na sha tabara da ayatul kursiyyu, na fi
arfin aljani da makiri ko tsunburbura na fi
arfinta"
"Ke dalla ware, ai ke kin fi tsunburburar ma rashin ji" suka din ga caccakar ruka kamar zasu daketa.

Ita damuwarta a kan mai sunana Baba ne, hukuncin da zai
auka a kan ta, na abin da ta aikata, sai ta ji bai ce komai ba ma, yayi shiru kamar bai san me aka yi ba.

Tsaye yake a bakin wardrobe
in, yana
arewa kayan ciki kallo kamar ba nasa ba, ya saka hannu da nufin ya
auko kaya, hannunsa a sauka a kan koriyar alkyabbarsa.

Kamar ya na jin tsoron Alkyabbar, ya zarota ya na kallonta.
*Sarki mai koriyar alkyabba a dawo lafiya, ka
anani a kan dokinka ko ka bani kyautar doki*
Shiru ya
an yi ya na tunani, ta yaya zai ji murya
aya a mabanbantan wurare, kuma haryanzu bai kai ga ganin fuskar wacece ba, gashi a duk lokacin da zai ji muryar, sai ta kira shi da sarki!.

Ajiye Alkyabbar ya yi, ya
auko wata dark blue
in suit, ya shirya a cikinsu ya
auki jakarsa ya fita.
aki ya tarar da Ammi tana sallar walaha, ya zauna ya jira ta idar.

Ta idar ta kammala Adduointa, sannan ta kalli Adam ta ce "Barka da wannan lokaci takawa".

Yayi murmushi ya ce "Barkanki Ammi, zan wuce ne"
Cikin tausayawa ta kalleshi ta ce "Ka na ganin babu matsala, zaka iya zuwa aikin?"
"Babu wata matsala in sha Allah"
"To matso na yi maka addu'a" ba musu ya matsa kusa sa Ammi, ya dur
uso mata da kansa, ta
ora hannunta na dama a kan nasa, ta dinga kwararo masa Adduoi.

Wata irin nutsuwa ya din ga ji ta na ratsa shi, ya lumshe idonsa, sai da ta idar, sannan ya ri
e hannun ya sumbaci hannun ya ce "Allah ya ja zamanin giwar Galadima, ya baki yawan rai, Allah ya ji
an Galadima"
Murmushi ta yi, tare da jin maganar har cikin ran ta ta ce "Amin takawa, Ubangiji Allah ya tsare" ya mi
e yana fa
in Amin, ya bar
akin.

Tun da abin nan ya faru, an kai ruwa rana sosai, kan malaman su ruma su yarda ta cigaba da zuwa makarantar, bisa sharu
ai sannan ruma ta cigaba da zuwa makarantar.

Tun baya da aka yi sulhu a police station, duk ranar juma'a sai mama ta aika wani ya tasa ruma a gaba sun je duba Asiya, sun kai wani abu, amma kullum babar Asiya babu godiyar Allah, kullum suka je sai ta yi complain, ita kuma ruma kan su taho, sai ta aikata wani abun da za ta sake tunzarata tayi ta masifa.

A haka duk suka ce sun daina zuwa, yau mama ta ce dan Allah mai sunan Baba ya saka ruma a gaba su je.

Tun da Allah ya sa babar Asiya ta yi arba da fuskar mai sunan baba, ta shiga hankalinta, ko maganar kirki ta kasa sai kame-kame.

Tun da suka gaisa, ya bata abin da zai bata, ya ce ruma ta tashi su tafi, ko yaya mai jiki bai ce ba balle ya ce Allah ya kyauta.
suka taho hanya, ruma a nutse take babu tsokana da hauma-hauma, saboda kura ta san gidan mai babban sanda.
da suka zo bakin layin su, cikin girmamawa ruma ta kalli mai sunan Baba ta ce "Mai sunan Baba, mama ta ce na taho mata da kayan miya a wurin Hudu"
Ya kalleta ya ce "Idan kin ga dama, ki tsaya hauma-hauma da neman magana a hanya, zaki zo ki sameni".

"In sha Allah ba zan yi ba"
Ganin da mutane a wurin Hudu, ya sanya ruma ta tsaya ta na jira, sai dai kan ya kawo kanta, ta
au wu
a ta din ga daddatsa masa kabewa bai sani ba.

Da ta gaji ta ce "Malam hudu ka sallameni mana"
Ya ce "Yi ha
uri na fara sallamar matan aure, su da zasu
ora girki"
Ruma ta yamutsa fuska ta ce "To da me matan auren suka fini?

Nima fa watarana matar auren nan ce"
Yayi murmushi ya ce "Eh, amma dai yanzu
waila ce, Allah ya nuna mana kin zama matar aure ruma"
Ta ha
e rai ta ce "Gaskiya malam Hudu ka daina gaya mini wannan kalmar ta watsewa,
waila fa iskanci ne"
an bu
e baki yayi ya na kallonta, sai kuma ya ce "To Allah ya baki ha
uri" sai da ta bawa mutanen wurin dariya.

Can ta kalli Hudu, ta kalli lafcecen billensa kamar an yi masa da gatari ta ce
"Malam Hudu, na da
e da tambayar nan a zuciyata wai meyasa aka yi maka bille?"
Yayi murmushi ya ce "Delu billen mahauta ne"
"To amma dai da wu
a aka yi maka ko?"
Ya ce "A'a, aska ce, billen gado ne na mahauta"
"To kai baka gaji ku
i ba sai bille, da babanku ya mutu sai aka raba muku billen?"
"Ke na gaji da wannan wula
ancin naki, mai zan baki?" Ruma ta mi
a masa ku
i, ta yi masa bayanin abun da zai bata, ya sallameta ta tafi gida.

Da ta je gida, ta ha
a kayan miyan, ta gyara su ta tafi kai marka
****
Tsaye take a harabar Hotel, tana sanye da doguwar riga ja, ta na
e kanta da jan mayafi, fuskarta sanye da tabarau da kuma takunkumin fuska, dan haka idan ba wanda yayi mata cikakken sani ba, ba yadda za ayi ka ganeta.

Wayarta ta
auko ta kira wata lamba, ta kara a kunnenta, a
an hasake ta ce "Gani nazo ka na ina?"
"Room A7, Vip" ta ajiye wayara, ta shiga cikin hotel
in, babu wanda ta tambaya da kanta ta gano
akin, ta tsaya a bakin
ofa, ta kuma kiran wayar "Gani a
ofar
akin" ta fa
a a ta
aice.

Wani mutum ne ya bu
ofar
akin ya le
o ya ce "Ke ce ba
uwar yalla
ai?"
"Kai ka san wani Yalla
ai, ka je ka gaya masa gani na zo"
"Ok, to dama cewa ya yi a shigo da ke"
"Ba zan shigo ba, idan ya matsu ya fito idan kuma ba a matse yake ba zan yi tafiyata, bana son jira".
an yi jimm ya ce "Amma kamar maganar ki ta yi tsauri"
A fusace ta ce "Kai ka san wacece ni kuwa?

Na yi mai wuyar ai da na zo nan, idan ba zai fito ba zan tafi"
Juyawa mutumin ya yi ya koma cikin
akin, babu da
ewa sai ga wani mutumin ya fito, shi ma fuskarsa rufe da takunkumi.

"Ki shigo mana, zuwa bai yi miki wahala ba sai shigowa?"
"Ba zan shigo ba, ka gaya mini koma menene a nan ina jin ka"
Ya ce "Well, mu je
asa to, sai mu yi magana"
Tare suka sauka
asa, suka samu wuri suka zauna, ya dubeta ya ce "To sauke takunkumin mana"
"Ba zan sauke ba, wai tukuna kai wayene naga kamar ka na
arin raina mini hankali"
Murmushi ya yi, ya sauke takunkumin fuskarsa ya ce "Khalifa senator usman, na san kin sanni kuma kina jin sunana, kuma kin san me nake nema"
Ajiyar zuciya ta yi, ta sauke na ta takunkumin ta ce "Dama kai ne?

To Meyasa ka ke nema na?"
"Samha kenan, kin san ita kasuwar muradi babu in da ba ta kai mutum, ba wani abu ne ya sa nake neman ki ba, sai dan mu ha
a hannu na taimake ki, ki taimake ni.

Ban sani ba ko baki sani ba, amma na san kin san Adam, Adam ya na barazana ga mutunci da rayuwar mahaifina, da kuma ni kaina da career ta, dan haka nake son ki taimakeni na kai shi
asa, zan baki ku
i ko nawa ki ke bukata" yayi maganar yana tsareta da ido.
Chapter 35 · 0% Book details