← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 116

Sashe 42

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba Uwani da ke 'yan kaye-kaye a falon ta ce "Ayi ha
uri uban gidana, ban san ka da yawan hasala ba, Allah ya huci zuciyar magajin Galadima, ayi ha
uri"
yar Adam ya ha
ura, ya nemi wuri ya zauna, ya na jin yadda zuciyarsa ke tafasa,
shi dama ba ta Mummy yake ba, Mahmud kawai yake son ya yiwa kashedi a kan rayuwarsu.

Nusaiba tsam ta mi
e, ta nufi
akin Iman, ta tarar da Iman
in zaune ta zuba uban tagumi, tana kallon kayan da aka yi amfani da damar bata, aka ci zarafinta, kayan da basu wuce ta yi kyauta da ninkin su ba.

Nusaiba ta dafata ta ce "Masoyiya"
Iman ta kalli Nusaiba ta ce "Na'am Anty Nusyna"
Kallon idon Iman Nusaiba ta yi, idonta ya nuna ta yi kuka sosai.

"Be brave iman, kiyi ha
uri, ban san yadda zan fasalta miki abin da nake ji ba, idan aka cutar da ke ba, muna sonki sosai Iman, kin san yanayin halin da ki ke ciki, dan Allah ki daina damuwa ko
ata ranki"
Iman ta yi murmushi ta ce "Kar ki wani damu, yayata ai na ma riga na saba"
Nusaiba ta zauna sosai ta
ora da cewa "And yakamata ki daina nuna ki na jin tsoron su, musamman yaya Mahmud kamar mara tunani, abin da aka gaya masa kawai da shi yake amfani, ai gara ma yayi ya koma in da yake karatu mu huta masifaffen banza"
Iman ta toshe baki ta ce "Sai na gaya masa abin da ki ka ce, babu ruwana" tayi maganar tana dariya.

Ajiyar zuciya Nusaiba tayi tana murmushi, ganin yadda murmushi ya bayyana a kyakkyawar fuskar Iman.

"Ohh ni rumaisa sai girma nake, mama, ta bakin naki kwanci tashi asarar mai rai, na shiga jss2 fa"
"Aikuwa dai, kina ta girma amma babu nutsuwa ba"
"Kai mama, Allah ya nuna mini lokacin da zaki yabeni, ke kullum bana abin arziki a wurinki mamancy"
Mama ta girgiza kai ta ce "Ai ke gaba
aya abin tsiyarki ya ninka na arzikin yawa"
"Mama"
"Ina jinki"
"To
an kalleni mana"
Mama ba ta kalli ruma ba ta ce "Sai kuma kiyi ai"
"Dan Allah ki sai mini shayi da indomie, kin san bana son tuwon nan "
"Rumaisa ai ni ce ma Indomien, zo ki gutsiri in da ki ke so ki ci, tuwo kuma ban yi miki dole ba, ki barni da kayana"
"Allah ya ji
an matar da ta
iro tuwo idan musulma ce, amma ta cuceni zuciyata tafi raya mini a zamanin tsunburbura ta zo"
Ruma ta
araci soki burutsunta, da gwasalewa mama tuwo, mama ta
i kulata.

Hankalin ruma ne ya tsaya a kan rediyon da mama take ji, wata mata tura wasi
a, tana son a bata maganin da zata sha, tun da tayi yaye
irjinta ya zube kullum mijinta cikin yi mata gori yake.

"Kan uba, amma wallahi maza basu da kai, dan Allah meye ha
insa da kallonta?" Mama ta ja rediyon ta kashe.

"Mama ya zaki kashe, ki bari mu ji mana, nifa bana son harkar watsewa, wallahi ka gaya mini maganar banza sai na tafi gidanmu, wannan ai rashin tarbiyya ne, ya ya zai din ga yi mata kallon
urilla, kuma mama ba kin ce mini
oyewa ake yi ba?

Ita ma har da ita"
Mama dai ta basar, tayi mata shiru, can ta kuma cewa "Hmm kin san Allah mama, nima na gani fa, 'yan ajinmu na islamiyya suka ce, wai idan mace tana tafiya ba ta saka hannu a hijjabinta, maza kallonta suke yi, haka ma idan ta juya bayanta, jiya da na je gidan Asabe ban samo gawayi ba na je titi, daga nan na tsaya sayen mai, kin san riga da skirt na saka, sai mayafin abayat, wani mutum ya tsurawa gurin zamana ido, ai ban sani ba, ina waiwayawa muka ha
a ido, na ce malam kalli gabanka mana, baki ganshi ba babba da shi na saka hannu na kare abina har na zo gida".

Abdallah ya ce "Sannu jikar faisal, duk 'yan matan da suke kaiwa suna komowa a wurin, ba wadda ya kalla sai ke
waila, wani
an abu kamar falanki, saboda asara ke zai tsaya kallo"
"Wallahi ni ba
waila bace ba, kuma ka je ka tambayi kowa na wurin ka ji, kallona yake yi, ni kuwa na saka hannu na rufe"
Mama ta ce "Ya isa haka, kuma saboda tsabar rashin sanin ciwon kai ki tafi har titi da
aramin mayafin da bai fi ayi kallabi da shi ba, duk ranar da Allah ya nuna mini, sai na zane ki.

Kuma zan saka bababana ya je islamiyyar lallai a raba muku aji da wannan yaron, dan sun fi
arfin tunanin ki"
Da sauri ruma ta ce "Ki yiwa Allah da ma'aikinsa, kar ki aika mai sunan Baba, kin san yanzu
iris yake jira yayi mini aure".

"Aikuwa ina daf da gaya masan, idan har baki nutsu ba, kin daina wannan rashin kan gadon ba, gara ya aurar da ke na huta"
Ruma ta saka hannu ta kama la
anta ta ce "Na daina da yardar Allah"
"Takawa, wai yaushe zaka je ka
auko yarinyar nan ne?"
an lumshe idonsa ya bu
e sannan ya ce "Zan
aukota ne, gara ta
an huta ta nutsu tukuna, visarta har yanzu da saura"
Ammi ta ce "To shikenan, yauwwa ya maganar tafiyar da na ji Jabir ya ce zaka yi?

Meye gaskiyar maganar?"
"Ammi ki manta da shi kawai,
an rainin hankali ne a wurin aiki ne za a tura mu wani bincike".

Ammi ta numfasa sannan ta ce "To, Allah ya yi jagora, amma dai duk da haka kamar yadda ya ce ka din ga kula takawa, ka san currently a
adamin da kake, kar ka janyo mana wata wahalar wadda muke ciki ba ta
are ba, dan Allah ka dinga komai a sannu, sannan ka ri
e addu'a kamar yadda nake jaddada maka"
"In sha Allah Ammi, kar ki damu ina iya
arina wurin yin Addu'a".

"Haka ake so, Allah ya yi maka jagora"
"Amin Ammi".

Daga haka ya
auko wayarsa yana duddubawa, yana tsaka da duba wayar, Ammi ta kuma cewa "Ko yaushe Mahmud zai koma makaranta, na ga kamar lokacin komawarsa yayi, kuma ance mini haryanzu ana ganin gilmawarsa a gidan nan"
Takawa ya sauke wayar, ya dubi Ammi ya ce "Ammi, ba babarsa tana kallo bai koma
in ba ta zira masa ido, dan Allah ki daina damuwa da abin da ya shafe su, ki din ga
agawa kan ki hankali".

Ammi ta girgiza kai ta ce "Da kai da su ni duk abu
aya ne a wurina, ba zan so rayuwar wani daga cikinku ta samu tangar
a ba".

"To Ammi tun da ba sa yi da ke, ai mu mun isheki rayuwa, dan Allah ki manta da su"
Ajiyar zuciya Ammi ta yi, ba ta sake cewa komai ba.

Yau kamar korarriya haka ruma ta shigo gida, sai cika take tana batsewa, ba ta kula kowa ba ta cire uniform ta yi wanka, ta zubo abincin ta ta fara ci.

Kamar wadda aka tsikara ta ce "Yaya Aliyu, wai ina ce makarantar 'ya'yan gwamna ne?"
Yayi murmushi ya ce "Mai yafaru?"
"A'a tambaya kawai nake yi"
"A manyan makarantu suke, wasu a turai ma"
"Suna zama a
asa, ajinsu babu abin zama?"
Yayi dariya ya ce "Amma kin ci kai, 'ya'yan gwamna ne zasu zauna a
asa?

Zama a
asa a makaranta wannan ai sai
an talaka"
"To meye banbancin mu da su?

Dukkanin mu ba mutane bane, kuma muma ba 'ya'ya bane?"
"Kuna da bambanci mai tazarar gaske, dukkaninku mutane ne, kuma 'ya'ya ne, amma iyayensu ke ri
e da madafun iko, abin da zaku yi ku taimaki kanku a matsayin yaran talakawa shi ne, kuyi karatu komai wahala, idan ba haka ba kuwa ku
are a bayinsu da 'ya'yansu"
Tamkar ruma zata fashe da kuka ta ce "To wallahi zan yi Allah ya isa, aka ce duk 'yan
asa
aya muke, bencinmu ya karye, dama wasu a
asa suke zama, kullum sai kayana sun yi datti, uniform
ina duk sun fara ko
ewa.

Ga malaman namu ma sai a hankali, wallahi malamin English
in mu bai iya turanci ba kame-kame yake yi, malamin math
in mu kuma Arabic yayi ba uwar da muke ganewa, ga ajinmu azababben zafi window
aya ce, bana gane komai a makarantar kamar na daina karatun.

Kuma jiya nake ji a radion mama uban ku
in da ake saiwa
wasu manyan motoci sai ka ce motar aljanna, ko meye sunansu oho na manta, to wallahi duk wanda aka raba da ha
ina ya cinye ban yafe ba, zama a
asan da nake a matsayina na 'yar
asa"
Mama ta ce "Ruma wa ki ke yi wa Allah ya isa, ban hanaki wannan
abi'ar ba ruma?"
"Mama ba zaki gane halin da muke ciki ba, ga rashin abin zama, ga zafi ga rashin malamai ga duka kamar an samu jakai, har noma ake sakamu fatanya a makaranta, gaba
aya makarantar mu 'ya'yan talakawa ne, shikenan mu ba mutane bane".

Ruma kenan, gaba
aya tunaninta da maganganunta sun shallake shekarunta, wata
ila hakan yana da ala
a da yawan jin radion da mama take yi, da yawan tattauna matsalolin da
asa ke ciki da yayyenta suke yi.

Babu wanda ya kuma tanka mata, tayi bambaminta ta gama, dan ta wani fannin tabbas Ruma tana da gaskiya, amma babu yadda za ayi a gaya mata tana da tazarar da wa
anda take hange take kamanta kanta da su ta gane.

Haka ta
are cin abincin tana mita, kuma bil ha
i har cikin ranta, take fa
ar yadda abin yake yi mata ciwo.

Kasancewar yau Alhamis babu makarantar islamiyya, Huzaifa da Yasir duk suna gida.

Huzaifa ya nutsu yana ta kallon tiktok a wayarsa, ruma ta lalla
a ta zira kanta tana kallo.
Chapter 42 · 0% Book details