← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 116

Sashe 81

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruma ba ta san jikinta babu
wari ba, sai da ta fara tafiyar nan, sannan ta gane ashe a galabaice take, jikinta babu
wari da
arfi kamar yadda take jin ta a da, gaba
aya ta gaji,
ishirwa take ji, ga duhun magariba ya fara yi, kuma babu alamar samun hanya,
afafuwanta tuni suka yi tsami, gashi sai taka abubuwa take yi, kama daga
aya zuwa
ananan duwatsu, amma zuciyarta ta cigaba da bata
warin gwiwar ta tafi, tana jin zata iya fita hanya a kowane lokaci.

Takawa ne yake ta safa da marwa a
akinsa, yana daddana wayar hannunsa, kallo
aya zaka yi masa ka san ya rame, duk yayi wani iri kamar mara lafiya.

Can ya kara wayar a kunnensa, cikin za
uwa ya ce "Ya ake ciki, me ka gano?

Akwai wani labari ne?".

"Easy mana Adam, wacce zan amsa maka cikin tambayoyin naka tukuna?

Ka yi ha
uri wannan bayanin duk ba na waya bane ba, kana da time ka shigo abuja gobe in Allah ya kaimu?".

Adam ya ce "Ni bani da wani time, am so much busy here, abubuwa sun yi mini yawa, koma menene kawai ka gaya mini ta waya, ina jin ka".

"A'a ni babu abun za zan gaya maka ta waya, ka bari ni zan shigo kanon in sha Allah"
Adam ya yakice gumin da yake tsatstsafo masa, ya ce "Bashir, bani da wani isasshen lokaci da zan baka, kawai ka yi abun da na ce, koma menene ka gaya mini, kar aikin da nake yi ya koma baya".

"Na fuskanci a rikice ka ke, idan ka sauko ma yi maganar, gaggawar ba ta da wani amfani " kan adam ya kuma magana, ya kashe wayarsa.

Ya yi jifa da wayar a kan gado, ya san tun da bashir ya ce masa ba zai gaya masa a yau ba ba zai fa
a ba.

"Bashir why, kana
arin mayar mini da aiki baya fa, dole na zo na sameka, ba zan iya jiranka ba".

Ya mi
e hannu ya
au waya
aya, ya sanya a aljihunsa, ya fita ya
au mota ya nufi family house
in su.

A sashen Ammi ya tarar da duk iyalan gidan ahalin marigayi Galadiman kano sun hallara, kama daga kan Mummy zuwa Fauziyya da ru
ayya, duk da ita ru
ayya ba ta fiye zama a gidan ba, tana can gidan yayar Mummy, ga kuma Ammi a zaune da iman da kuma Nusaiba, na gidan auren ne kawai ba sa nan.

Takawa yayi turus yana kallonsu, wambai ya
ure shi da ido, ya
araso cikin falon yana sake tsuke fuska ya
am risuna ya ce "Barka da zuwa"
Wambai ya
i kulashi, shi kuma Adam bai tashi ba.

"Wato wuyanka har yayi kaurin da zan aika maka ka zo, ka yi burus da kirana ko?"
Yayi shiru bai ko motsa ba, sai ma alamun
acin rai da suka baiyyana a fuskar shi.

Da sauri Ammi ta ce "Allah ya taimake ka tuba yake yi, ayyuka ne suka sha masa kai, ga rashin lafiya da.....

"Ya isa binta, dama ke ki ke goya masa baya yake abun da ya ga dama, bai san darajar mutane ba sai zuciya ta banza da ta wofi, tabbas na fara gazgata jita-jitar da ake yi a kansa, na cewar yana shaye-shaye, duba da yanayin abubuwan da yake aikatawa, kalli yadda yake muzurai kamar zai kai mini duka, kalli yadda yake yawo a gari, kamar ba jinin sarauta ba, kalli
ananan kayan da ke jikinsa, duk wani abu da ya shafi al'adar gidan nan nema yake ya watsr da ita, saboda kawai ya raina mutane.

Cikin dakiya Ammi ta sake cewa "Tuba yake, ayi masa afuwa".

Adam a zuciyarsa kuwa ji yake yi tamkar ya tashi yayi tafiyarsa, don cigaba da sauraren wambai, na iya sanya wa ya
ura masa ashar ya huta, saboda takaici.

Wambai ya mayar da idonsa kan Ammi ya ce 'Na san kina sane da maganar da take yawo a cikin masarautar nan, na yayi shaye-shaye yayi yim
urin yi wa waccan yarinya fya
e, yayin da daga wata majiyar muka samu labarin ba fya
e bane ba, wani abu ne a tsakaninsu daban, to dukkaninku ku sani, ko da
an uwana baya raye, ba zan lamuncin mutunci da martabar gidan nan ta lalace ba, a hakan ka ke saka ran sarauta ta shiga hannunka, kana shaye-shaye ga kuma wannan mummunar maganar, ba zan lamunta ba, tun kan maganar nan ta je wurin mai martaba, zan yi wa tufkar hanci, ni na san abun yi.

Ke binta ina mai baki umarni a kan lallai wannan yarinya 'yar tsintuwa, ko dai ki nemi ahalinta ki mayar musu da ita, ko kuma ki nema mata miji ta tattara ta bar cikin gidan nan, na baki nan da abun da bai wuce watanni biyu ba, ta daina amfani da kyawunta tana barazana ga mutuncin gidan nan ba.

Labarai suna zuwar mana, yadda ake ta samun akasin auren 'ya'yan jamila saboda ita, to ki san abun yi tun kan ku kai ni bango ".

Iman ta yi shiru ta sunkuyar da kai, ta ri
e yatsun Ammi tana wasa da su, tana
an murzawa da
arfi, saboda azabar
acin rai da damuwa.

Haka wambai ya
arewa Ammi cin mutunci ita da yaranta, a gaban Mummy, daga bisani ya sallame su.

Tun kan su gama watsewa daga falon, iman ta fashe da kuka, mussaman da ake ce wai ita ce ke barazana ga mutuncin gidan.

Adam rasa abin da zai ce ya yi, bayan fitar wambai Mummy ta ce "Sai ha
uri fa binta, yaran yau me ka haifesu ba ka haifi halinsu, a zage a bawa yara tarbiyya, kan a samar mana da abun kunyar da zamu gagara kallon duniya, ko mu rasa sarautarmu gaba
aya".

Babu wanda ya tanka mata a cikin su, har Adam da yake zaune yana jin ta.

Bayan fitar Mummy Adam ya ce "Ammi, Allah fa bai ce in bi wan ubana ba, ke da marigayi kune yake wajibina na biku, dan haka babu ni babu wannan tsohon da zuriyarsa har gaban abada, ba zan
ara zuwan kiran da zai yi mini ba, kuma ba zan sake zama a gabansa na yi masa kallon uba ba, ita kuma Mummy haryanzu kin hanani dama a kanta, shikenan idan har zamu cigaba da zuba mata ido, to fa zata cigaba da
arin ganinmu a rana ne.

Ni ban damu ba dama can ni
an iska ne mara mutunci a cikin masarautar nan, amma ba zan cigaba da lamuntar wula
anta iman ba, ko dan saboda ita yakamata ko sau
aya ki kareta" ya
arasa maganar a matu
ar zafafe, ya tashi ya bar falon.

Daga Nusaiba har iman saka Ammi suka yi a gaba suna yi mata kuka, ta rasa abun da zata yi, ta rungumesu duka a jikinta tana ajiyar zuciya.

Tabbas takawa yayi gaskiya, ha
uri da kawaicin da take nunawa a kan abubuwan da ake yi wa iman da ma iya kanta da yaranta, yayi yawa, sai dai ba tana yin hakan da wula
anta iman ko 'ya'yanta ba, sai dan gudun kar ayi
arin rabata da ita.

Ko arzikin ganin tafin hannunta rumaisa ba ta iya yi, saboda duhun da ya mamaye ilahirin dajin, sai kukan abubuwa daban daban da take ji, lokaci zuwa lokaci, wasu lokutan kuma ta ji shiru kamar babu wata halitta da ta wanzu a cikin dajin.

Sai yanzu ta gane a wurin 'yan ta'addam nan a rahama take, ko ba komai tana jin motsin mutane, idan ta gaji kuma tana yi musu kuka ko da zasu hantareta,
wani irin sauro da kuma wasu irin
wari ne suke gasa mata cizo ko ta ko ina.

Ta yi iya
arin ta ta nanna
e jaririn, dan kar
wari su cije shi, sai numfashi yake sama-sama, jikinsa ya
au zafi, ita kanta rumaisan zazza
i ne a jikinta, ga wata irin azababbiyar
ishirwa da kuma yunwa da take ji.

A haka ta jingina a jikin bishiya tana addu'a tana kuka
asa-
asa, ba dan tana tausayin jaririn nan ba, da kuma tsoron wanda ya kashe kansa makomarsa wuta ba, to da babu abun da zai hanata ta kashe kanta.

A hankali take sauke numfashi tana soshe-soshe, babu alamar tana jin bacci a idonta.

Kamar wadda aka tsikara, ta tashi tana laluba hanya, tana tafiya a hankali, hannunta
auke da jariri.

Hayaniya ta fara jiyowa sama-sama ana maganganu.

Dan haka ta din ga nufar in da sautin yake fitowa, tana nufar sautin tana hango hasken wuta yana ci, da alama dai mutane ne a wajen.

A haka har ta cin musu, ta la
e tana le
awa, kusan zata iya cewa wata
aramar masan'anta ce ta sarrafa makamai iri iri, manya da
anana dan wasu ma ba ta san su ba, wasu suna shaye-shaye wasu suna ta shirya makamai, yayin da wasu ke
idaya ku
"Kai har labari ya cika gari artabun da aka yi a dajin nan, mutuwar su sha tara duk ta cika jaridu, kuma haryanzu babu wata
ungiya da ta
au alhakin kai wa su sha tara hari" cewar wani da yake ta murza sigari.

"Kuma ba jami'an tsaro bane ba, a cikin mu ne dai, kuma an kwashe mutanen suka yi garkuwa da su ba" wani ya bashi amsa.

"Haka na ji, daga sama an bada umarnin abi sahunsu, akwai wani jariri da wata mata ta haifa, ana son a tabattar da baya raye, gobe akwai operation, dole a gano suwaye suka kai harin".

"Haka ne, amma yanzu a gama ware kayan nan, su je su rarraba, da safe a bar gari da su, kai yellow, ku zo ku
inke ku
in nan a cikin buhunhuna a kai su a daren nan, mutanen cikin bukkar nan kuwa duk wanda ba a kawo ku
in fansar sa ba, ku
addamar masa kawai".

Hawaye ne suka ziraro a fuskar rumaisa, wato nan ma wata tawagar ce ta daban, atishawa jaririn hannunta yayi, hakan ya janyo hankalinsu in da take.

"Kai anya ba wani naman jejin ne a wurin ba, ku duba mana".
Chapter 81 · 0% Book details