← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 116

Sashe 62

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutanen da ba imani ne da su ba, 'ya mace ce fa, Allah ka
ai ya san me zasu yi mata, gara ace mutuwa ta yi ga gawarta da wannan tashin hankalin, wa zai kula da ita?".

Aliyu da tasa zuciyar ma ke daf da karyewa ya ce "Na sani, amma addu'a ba ta bar komai ba Usman ita zamu dagewa, kayi ha
uri tashi ka daina kuka kar mama ta zo ta samemu" haka yayi ta rarrashin Usman.

Mai sunan baba kuwa ji yayi duniyar ta yi masa zafi, ina ma shi aka
auka aka bar ruma.

Yaya mama za ta ji idan ta samu labarin an yi garkuwa da rumaisa?.

Zuciyarsa ta din ga zafi yana jin da zai ga gwaggo sai yayi mata rashin mutuncin da bata ta
a tunani ba, dan yana jin zai iya mangareta dan duk ita ta janyo wannan masifar, duk da tana
anwar mahaifinsu, cewar da aka yi tana gadon asibiti jininta ya hau bai dameshi ba, dan da jinin tasa uwar ya hau ko wani abu ya samu ruma, gara duk abin da zai faru ya faru.

Zuwan takawa a Abuja a wannan karon ya sanya ya samu abubuwa masu muhimmanci da bincikensa bai kai masa ba a baya, sai dai zuciyarsa na ta azalzalarsa a kan lallai ya koma gida, jinsa yake tamkar a kan wuta, idan bai bar garin ba kamar wani mummunan abu zai faru da shi, dan haka babu shiri, ya tattara kayansa ya taho Kano, dama ga Ammi na ta waya dan duk a tsorace take, saboda yanayin jikinsa, Jabir ma duk ya addabeshi a kan nan kano ma akwai aiki, dan haka ya ha
a kayansa ya koma kano.

Sai ka ce a wannan karon ya fara tafiye-tafiye, Ammi sai hamdala take a kan dawowarsa gida lafiya, dan ba
aramin tashin hankali ta shiga ba, da yayi tafiyar nan dan sam ji ta yi ba ta son tafiyar ta sa.

A gidan Turaki suka ha
u, da takawa, da Jabir da kuma Jamil da ya kasance wa ga Samha kuma cousin
in sa.

Hira suke yi sosai, suna tattaunawa a kan rayuwa.

Jamil ya zunguri Takawa ya ce "Kai, wai me kake nufi da ni ne, ba fa ka taka gidana ba, ranar da na tare ma ko rakiya ba ka yi mini ba, kuma ba ka zo ba sai harkokinka kawai kake"
an shiru Adam yayi, tun daga lokacin da ya ji muryar ruma a ranar ya rasa nutsuwarsa, kilisar ma da
yar aka
arasata da shi, tunani ya fara yi ko zuwa unguwar su zai yi.

'Ka je ka yi mata me?' wata zuciyar ta tambayeshi.

Tsaki yayi wanda ya fito fili bai sani ba.

"Tsakin me kake kuma?" Adam ya tambaye shi.

Girgiza kai yayi bai ce komai ba.

Jabir ya ce "Yauwwa Takawa, ina mutuniyarka kuwa wannan yarinyar?"
e rai Adam yayi tare da basarwa, Jamil ya ce "Wace yarinyar, budurwa yayi ne?

Kai ka isa ka yi wa
anwata kishiya?"
Jabir ya ce "To bana ce ba, wata 'yar figigiyar yarinya ce mai kama da bainu, ban ta
a ganin yarinya mara mutunci da rashin tsoro irinta ba".

Adam a ransa ya ce "Ai ba ka san mara mutunci ba, sai ka ga wasi
ar da ta rubuta mini' amma a zahiri yayi shiru kamar ba da shi suke hirar ba.

"Ina sonka Adam, so bana wasa ba, so mai tsananin gaske son da nake jin zan iya komai domin na mallake ka, duk da na rasa dalilin da ya sanya bana gabanka, ko da yake ba rasa dalili na yi ba, nafi kowa sanin dalilin da yasa bana gabanka, kuma ina daf da magance komai domin in samu mi
iyar hanya
ar ta cimma muradina na rayuwa da kai, ko baka aureni ba ina son kasancewa da kai na rayu
ashin kulawarka.

Ban sani ba ko zuwa nan gaba asirina ya tonu duk da bana tunanin faruwar hakan, amma idan ma ya farun ka yi mini uzuri soyayyar ka ce ta janyo mini hakan" tamkar ta
iya haka samha ta saka hoton Adam a gaba ta na surutu, hoton yana sanye da kaya ne na sarauta, ya
an sauke rawaninsa yana murmushi, wanda aka
auka da hawan wata salla.

Sai da ta gama soki burutsunta, ta mayar da hoton ma'ajiyarsa, ta tashi ta
arasa shirinta ta fice.

Mummy ce tare da aminiyarta zaune a
uryar
akin Mummy suna tattaunawa.

"Wai hajiya Lubabatu babu wani zazzafan malami ne, abubuwa kamar sun tsaya mini, sun
i cigaba kamar yadda nake so".

"Haba Jamila, ke kin san an da
e muna ha
a rijiya, rijiyar da muke saka ran samun ruwa a kowane lokaci, mun shirin da idan balli ya tashi akwai rikici, ke dai mu cigaba da ha
uri".

Mummy ta girgiza kai ta ce "Ya ci ace burina ya gama cika, nifa da dai da mintuna biyar bana son ruhin Binta ya kasance cikin kwanciyar hankali da farinciki, so nake ta dauwwama a ba
in ciki har
arshen rayuwarta".

Dariya Hajiya Lubabatu ta yi ta ce "Haba Jamila, ai ko a haka kika barta wallahi ta yabawa aya za
inta, kuma ta
ana ku
arta, amma ki cigaba da ha
uri ai mun
ana tarko daban-daban".

Mummy ta jinjina kai ta ce "Shikenan, bari mu ga zuwa yaushe, na cigaba da sanya musu ido, duk wani motsinsu uwani na gaya mini, kuma na ce lallai ta kawo mini maganin da waccan 'yar tsintuwar ke shafa masa".

"To shikenan, to bari mu ga yadda abubuwa zasu kaya".

Har azahar babu wanda ya kula su ruma, masu kuka na yi masu addu'a na yi, ga yunwa ta addabeta a gida wataran
arfe bakwai ta karya, amma har bayan azahar babu wanda ya kulasu balle ya basu wani abu.

Tashi ruma ta yi ta samu
aya daga cikin 'yan bindigar ta ce "Bawan Allah yunwa nake ji, ku bani abinci na ci"
Wani mugun kallo ya yi wa ruma ya ce "Zo ki cinyeni, an gaya miki nan wurin hutu ne da jin da
i?".

"Ai ni ba mayya bace da zan cinyeka, idan ma cin ne ban ga abin ci a nan ba, idan ba za a bamu abinci ba meyasa zaku kawo mu nan?" Ta na rufe baki yana hanka
eta sai dai fa
asa ya saita ta da bindiga "Idan ki ka yi mini hauka, yanzu na lahira zasu yi maraba da ke".

Ruma ta kalli yadda ta fa
asa, wata irin zuciya ta harzi
ota ta mi
e tsaye ta sake kallonsa ta ce "Na fa
a a bani abinci yunwa nake ji, ai da
inta idan ka kasheni ba a wuta zaka sakani ko aljanna ba, hisabi na Allah ne, to na fa
a a bani abinci yunwa nake ji, harbeni maza kai kuma a
ara maka kwanakinka a duniya"
Babu alamar tsoro ko shakka a tare da ruma, kowa sai da ya Zubo mata ido, saboda
arfin halinta.

A fusace ya tashi yayi kan ruma, amma wani ya ri
e shi, ya ce kar ka kuskura,
yaleta idan ka yi mata wani abun za'a iya samun matsala, ka bari oga ya zo ya fa
i ya za ayi".

Huci ya din ga yi yaso ya tattaka ruma, ko ya keta mata haddi a gaban mutanen wurin, ya kawo
arshen harshenta.

"Ni baka kyauta mini ba da baka bari ya kasheni na huta ba"
"Wato ke dai bakinki ba zai mutu ba ko?"
"Idan har so ku ke na yi shiru, to ku kasheni ko ku mayar da ni gidanmu, wannan ai zalunci ne ni yunwa nake ji" tayi maganar tana share hawaye.

Dattijon nan ne dai na jiya ya ce "Yarinya ki yi shiru da bakinki, kar su citar da ke, wannan mutanen ba ayi musu haka".

"To ni yunwa nake ji" tayi maganar har cikin zuciyarta.

Duk wani kurari da zare ido ruma ta
i yin shiru, kamar ma da gayya take yi dan ta tunzurasu su yi mata abin da za su yi mata.

Har dare mama ba ta san abin da ya faru ba, kuma an rasa wanda zai gaya mata, sai mita take musu cewar ita fa ta kasa ha
uri ta kira gwaggo idan an dawo da ruma ta ha
ata da ita, amma wayar gwaggon ba ta shiga.

Sun yi mamaki da duk jin rediyon mama ba ta ji batun kai harin ba.

Ganin tana ta surutu ita ka
ai ba wanda ya tanka mata, ya sanya ta magantu "Wai ba zaku gaya mini meke faruwa ba ne?

Duk cikinku fa yau babu wanda ya ci abinci, kun
i walwala kun
i magana, kuma kun
i gaya mini menene?"
Usman ne ya tashi ya ce "Mama sai da safe, ni dai bana jin da
i ne".

Babu wanda ya bawa mama amsa, a hankali duk suka watse daga tsakar gidan, mama ta sha jinin jikinta ta fara tunanin menene ya faru haka, da basa son gaya mata?.

Babu wanda ya saurari su ruma sai bayan la'asar, aka zo da wasu kuloli a kan babur, aka rarraba musu wata busashshiyar gurasa, gaya guda
ai, sai pure water
aya tamkar mabarata.

Ruma ta kalli gurasar nan, duk uwar yunwar da take ji, amma a rasa me za a bata sai wannan takurarriyar abar a bushe, babu mai babu komai a jiki.

Gashi duk ta bushe kamar
anzo.

Ruma ta gasta ta fara
arin ha
iya, amma ta kasa ha
iyewa, da
yar ta dannata da ruwa, daga gutsura
ayar nan ba ta
ara ba ta shanye ruwanta ta yar da ledar, sauran kuwa tuni kowa ya kama gurasar nan suka cinye.

Duk wata tattaunawa su Usman da sauran 'yan uwansa sun yi, amma sun rasa ta ina zasu
ullowa lamarin, duk in da zasu buga sun yi, amma babu wani labari game da in da su ruma suke, gashi da wani ya ce zai je katsinan mama za ta gano akwai abin da yake faruwa, dan a yanzu haka ma duk ta tsargu, mussaman yadda suka daina walwala ga kuma ta fara shiga damuwa rashin shigar wayar gwaggo.
Chapter 62 · 0% Book details