← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 116

Sashe 111

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Barkanki dai, kuna lafiya?"
"Alhamdilillah, ya kuma mu ka ji da wannan lamari da ya faru?"
Ammi ta amsa da "Alhamdilillah"
"To Allah ya ji
anta da rahama"
"Amin ya rabb"
Mummy ta gyara zamanta ta ce "To, ni dai giwa idan wani abun na yi miki dan Allah ki yafe mini, ban san me na yi miki haka ba, ai ko ban samu shigowa ba, ya kyautu a ce kin aika mini jaririn na gani, nima jiakana ne, amma har su Fauziyya suka zo aka hanasu jaririn, yaran nan ko muna so ko ba ma so tsatsonsu
aya fa, wannan abun babu in da zai kaimu, ni dai ki yafe mini, amma a bani yaron na ganshi"
Ammi ta
an dubi mummy, kamar ba a wurin zaman makoki suka din ga yi da ita a gabanta suna yasar mata da maganganu ba, ta basar ta ce "Bari a kawo shi ki ganshi" tayi maganar ba tare da ta tanka wancan maganganun da ta yi da fari ba.

Iman ce ta
auko sabir, ta kawo wa mummy shi, ta sanya hannu ta kar
e shi, tana wani irin murmushi ta ce "Tubarkallah masha Allah, wannan yayi wayo sosai, sai dai ni kasa gane ma da wa yake kama a tsakanin aishar da takawa"
Ammi kawai ta kalleta ba ta ce komai ba.

"To wane sunan aka saka masa?"
"Mahmud, ana kiransa sabir".

Da sauri Mummy ta kalli Ammi ta ce "Mahmud kuma?

Sunan Mahmud ya ci kenan?"
Ammi ta ce "Eh, sunansa ya mayar masa"
Mummy za ta yi magana, Adam ya fa
akin kamar wanda ya
wato a hannun miyagu.

Tun a falon ya fara
alle rigarsa, saboda wani irin gumi da yake yi,
afafuwansa kamar ba zasu iya
aukarsa ba.

A gigice ammi ta tashi ta bi shi tana kiran sunansa, sai dai bai iya tsayawa ba, Mummy ma tashin ta yi ta bi bayansu, tana tambayar ko lafiya.

Kan gadon ammi ya haye, jikinsa ya fara wannan mazarin, kamar wanda ake bugawa gangi.

A gigice ammi ta ce "Iman,
auko maganinsa maza"
Da hanzari iman ta fita ta bar
akin, ammi Cikin damuwa ta ce "Takawa meyafaru ne?

Meyake damunka?" Bai amsa mata ba, sai runtse idanuwansa da ya yi.

Iman ta dawo da jarkar maganin da ake shafa masa, ta bu
e ta tsiyayo, ta fara
arin shafa masa, amma ya juya kansa ya ce "Kar ki shafa mini, a hayyacina nake, jikina zai daina rawar ne, ku lullu
eni" duk yadda ammi ta so shafa masa
in yarda ya yi, sai lullu
e shi da aka yi.

Bin maganin da kallo Mummy ta din ga yi, sannan ta ce "Wai giwa harzuwa wani lokacin zaki bar yaron nan ya cigaba da rayuwa da wannan larurar ba tare da kin nema masa magani ba?"
"Ina iya
arina, Allah ne bai kawo
arshen abun ba"
"To kina zaune Allah za kawo
arshen lamarin, shi meye wannan
in da ake shafa masa?" Ganin ammi ba ta bata amsa ba ya sanya iman cewa "Magani ne"
o mini na gani" ta yi maganar tana tsare iman da ido, iman ta
auka ta mi
a mata, ta kar
i jarkar ta din ga jujjuyata, tana nazartar meye a ciki, amma ta kasa ganewa, ta ajiye robar ta ce "Shikenan, ga wannan yaron, amma akwai bu
atar ki mi
e tsaye fiye da da, ko kuma ya dauwwama cikin nakasa" kamar dai
azu, a yanzun ma ba ta samu amsa daga ammin ba.

Bashir kuwa tun da ya ga Adam ya
ace masa, ya ha
ura ya koma, dan bashi da tabbacin in da zai nufa ya bi adam
in, kuma ya kira shi bai
aga wayarsa ba.

Rumaisa kuwa zazzage kayanta ta yi da aka bata, na wurin Ammi da na turaki.

Turmi biyar ammi ta bata na atamfar tare da turare mai
amshin gaske.

Turaki kuma ya sanya an cika mata ledoji da kayan dubulan, da uban kilishi fal da soyayyen naman kaza, sai kuma turaruka, ga kuma nono mai kyau kusan galan guda da man shanu.

Ruma ta din ga yashe baki tana murna.

Mama ta ce "Eh dole ki yi murna mana, a dalilinsa kin samu iyayensa sun yi miki sha tara ta arziki ke kuma kina yi wa
an su rashin mutunci"
Ruma a ranta ta ce "Hmm mama ba zaki gane bane ba, baki san girman laifin da mutumin nan yayi mini ba, sai na tabattar masa da abun da na gaya masa ai" mama ta yi ta mita, amma ruma ta yi shiru ba ta ce komai ba, sai ma tunanin gobe in Allah ya kaimu za ta koma makaranta abun da ba ta so.

Sai da ta zo kwanciya barcci, sannan wata irin kewar sabir ta sake kamata, ta rungume fulonta, ta rintse idonta, ta din ga hango fuskarsa yana kallonta yana lumshe idonsa.

Kamar an kunnawa zuciyarta wuta, haka ta din ga jin wata irin
ishirwar son sake ganin sabir, tamkar ta yi tsuntsuwa ta tashi.

Ta sake rintse idonta, tana sake tuna yadda take kwana gata sabir a asibiti, ganinsa da ta yi yau ta sake jin du rintsi duk wuya sai an bata
an ta.

Haka kurum ta hau kuka, tana sake jin tsana da haushin adam a zuciyarta, a ganinta duk shi ya
ulla a
wace sabir a hanata shi.

Cikin ikon Allah, takawa ya farfa
o gaba
aya, ammi ta saka shi a gaba ta din ga tambayarsa a kan meyafaru har ya shiga wannan yanayin.
oye ya
i gayawa ammi dalili, ya ce mata bakomai, kamar kullum ta din ga yi masa nasiha tare da fatan Allah ya bashi lafiya da mafita a kan lamuransa.

Washegari da safe rumaisa kamar ta saka kuka, mai sunan baba ya kafa ya tsare, ya sanya rumaisa a gaba ta shirya cikin uniform
in ta da suka sha guga, kamar ta fashe saboda takaici, ba ta son makarantar nan, ya sakata a gaba ya tafi kaita makaranta.

A ofishin shugaban makarantar ma, sake jajantawa rumaisa abun da ya sameta malamai suka yi, suka yi mata barka da dawowa tare da fatan Allah ya sanya ta nutsu zamanta a hannun
an bindiga ya zame mata darasi.

Gaba daya hankalinta ba ya kansu, tunaninnta kawai yadda za ta ga sabir, mai sunan baba ya gama clearing
in abun da yakamata, aka ce ta tafi aji, amma ajin baya zata koma saboda an riga an yi mata nisa a karatu.

"Kaii repeating aka yi mini, kenan ba zan yi candy da wuri ba, ta
wallahi ba..." Gum ta rufe bakinta ba ta
arasa maganar ba, saboda kallon da mai sunan baba yayi mata, tana ji tana gani aka mayar da ita ajin baya.

A ranta ta ce 'Wallahi ba zan zauna a ajin baya ba, sai a zata ma da
anci ne ya saka aka yi mata repeating"
Da aka fita break,
an ajinsu da suka yi gaba, suka din ga tsalle suna murna, rumaisa ta dawo.

Sam ta
i shiga sabgar kowa, ta
au littafinta ta din ga zana hoton sabir a bayan litattafan ta.

Har aka tashi ba ta san me aka yi ba.

Da ta koma gida mama tana ta murna, tana tambayarta ya aka yi a makarantar?

Rai a
ace ruma ta ce "saboda tsabar tsanar da mai sunan baba yayi mini, ya sa aka yi mini repeating, wallahi ba zan zauna a ajin nan ba, ni ajin yan candy ma zan koma" ganin rumaisa za ta
ata rai, ya sanya ta shareta.

Can rumaisa ta kuma cewa "Mama dan Allah in anjima, ki ce yasir ya rakani gidan su hauwwaliya na duba
afarta"
Mama ta ce "Kuma kin yi tunani mai kyau, kya je ki gaishe su, su ga kin warware sosai, amma sai gobe in Allah ya kaimu"
"Dan Allah mama in je yau"
"Goben in Allah ya kaimu ma sai na ce ba zaki je ba"
"To ki yi ha
uri, Allah ya kaimu goben".

Adam kuwa gaba
aya wunin ranar bai fita ba, ya san dole Jabir zai zo nemasa, ya bar sa
on ko jabir ya zo, a bashi ha
uri ba zai iya ganin kowa ba.

Ya kulle kansa a
aki, ya kunna wayarsa ya hau social media, ya ga yadda labari ya baza ko in, ga tarin kiran waya da sa
onni daga
an jarida, mutane sai comments suke kala-kala.

Ganin wayar na neman caza masa kai, ya sanya yayi jifa da wayar, gaba
aya ya ji ya rasa
warin gwiwar da zai sake fuskantar duniya, da
udurinsa na son kawo
arshen yi wa
asa da harkar tsaro
arna.

Ya ji ya rasa
warin gwiwar bincikar wa
anda suka yi garkuwa da matarsa.

Sai da Ammi ta yi da gaske, sannan ya bu
akinsa, har ya samu ya ci abinci, amma bai gaya mata abun da yake faruwa ba, saboda kar ya sake
aga mata hankali.

Rumaisa yau ji take yi kamar salla, saboda yau zata kuma zuwa ta gano Sabir, dan a yanzu babu abun da yake faranta mata rai sama da haka.

Yau da rumaisa ta je makaranta,
in zama ta yi a ajin da aka kaita, ta tafi ajinsu ta yi zamant, ta ce ba ta ga wanda ya isa yayi mata repeating ba, sai dai a gaji a koreta daga makaranta gaba
aya, wanda da za ayi mata haka da shi ta fi so, dan ita ba
aunar makarantar take yi ba.

Mai martaba a yau da kansa ya dira a gidan su takawa, wanda hakan ya sa gidan ya cika ma
il da hadimai, da jami'an tsaro, masu kaiwa suna komowa, tun daga farkon titin har cikin gidan.

Bai sauka a ko ina ba, sai a sashen Ammi.

Mummy na jin labarin zuwan mai marataba, ta tarkato yaranta ta bazamo sashin ammi, da sunan zuwa kwasar gaisuwa a wurin mai martaba sarki.
afa da
afa ya zo ya yi wa Adam ta'aziyyar mutuwar aisha, sakamakon baya gari lokacin da abun ya faru.
Chapter 111 · 0% Book details