← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 116

Sashe 57

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai tafiyar da nisa sosai, wurin shiru ba kowa sai ragowar abubuwan da aka
ona, da tsirarun bukkoki a can gaba ka
an, wurin kamar an yi wata annoba.

"Ke wace wannan me ki ke yi a wurin nan?" A hankali ta waiwaya taga wani dattijo a tsaye s bayanta, hannunsa ri
e jallon ruwa.

"Sannu baba" ya amsa da yauwwa.

Yana cigaba da
arewa ruma kallo.

"Baba gidan 'yan uwanmu mu ka zo, na hau wani dutse na hango nan shine na ce bari na zo na gani, Allah ya mayar da alkhairi amma kun gayawa 'yan sanda abin da ya faru?"
Kallon ruma yake, yadda take magana fiye da shekarunta.

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Gidan wa ki ka zo a garin nan?"
"Gidan dagaci ne,
an uwan babanmu ne" ya jinjina mata kai ya ce "To mun gode da jajen da ki ka yi mana, amma maza ki tafi kar sauran mutanen rigar nan su ganki".

"To in sun ganni mai zai faru me na yi musu?"
"Kasheki za su yi, dan haka muje na raka ki hanya" babu musu ya saka ruma a gaba har zuwa cikin gari, suna tafe suna hira ruma tana addaba masa da tambayoyinta da ba sa
arewa"
A hanya suka yi sallama, ya koma ita kuma ta
arasa gida.

Gwaggo duk ta tashi hankalinta rashin ganin ruma, ita kuwa ko a jikinta ta ce kallon gari ta fita yi.

Sai dai a tattaunawar ta da dattijon nan ya gaya mata wasu abubuwa da suka sake
aure tunaninta.
****
Hajiya Lubabatu ce ta tsaya a tsakiyar
akinta, tana kallon hoton Galadima mai ci a yanzu, wands ya kasance mijinta da yake can
asar Germany yana jinya, ta
an lan
wasa yatsan hannunta
aya sannan ta furta "Ka yi ha
uri ranka ya da
e, bani da isasshen lokacin da zan cigaba da
atawa a kan ka, goben
ana ita ce a gabana yanzu " ta yi maganar tamkar na cikin hoton yana jinta.

Khalifa ne zaune a kan kujerar da take kallon wadda mahaifinsa yake, mahaifinsa sai murmushi yake sannan ya nisa ya ce "Ina jinka Khalifa".

"Yauwwa daddy, kamar yadda nayi maka bayani, na tsara komai kuma ina da ya
inin komai zai tafi dai-dai da yardar Allah".

"Haka ne, ban
i ta taka ba, na kuma yabawa
arin da kake yi, amma gani nake komai zamu yi wa yaron nan ba zamu huce ba, yanzu haka bayanai sun zo mini yana garin Abuja, sai dai ban san wurin wa yaje ba, idan har ya cigaba da abin nan EFCC zata bincike ni, kuma daga haka ya
ata siyasata, ya ci mutuncina kuma ya
ata gobenka".

Khalifa ya gyara zama ya ce "Daddy, ai shiyasa nake ta
arin aikin nan ya tabatta, ta yadda zan kau da hankalinsa a kan komai, ya tattarashi a wuri
aya, ka harda dani, abin nan zai yiwu daddy, kuma akwai nasara a ciki".

Senator wakili ya yi murmushi ya ce "To shikenan, ina saurarenka, sannan duk abin da kake bu
ata, i will make sure that I provide it".

"To Shikenan Daddy, godiya nake "
Yayi murmushi tare da jinjina masa.

Kwanakin su ruma uku, ta saki jikinta, duk da kullum sai sun yi waya da mama, yawo kuwa kamar ta ci
afar kare, har gona suke zuwa ita da Lawisa, har ta saba da sirikan gwaggo da yaran ma
wabta.

Sai dai gona
aya aka samu aka sayar, a gonakin baban nasu, kuma shima dubu
ari bakwai kawai aka samu, saboda yanayin in da gonar take babu tsaro sosai.

Ana i gobe zasu dawo kano, Gwaggo ta shirya ruma, ta ha
ata da lawisa lawalli ya kai su can wani
auye, gidan wani
anin mahaifinsu, wai su gaishe su.

Aliyu sai mita yake yana tambarat gwaggo yaushe su ruma za su dawo, saboda da sassafe yake son su kama hanya, gwaggo ta ce kar ya damu, gobe da safe zasu dawo.

Har washegari da safe su ruma ba su dawo ba, Aliyu ya ce "Gwaggo, wai haryanzu su ruma ba zasu dawo ba, tafiya fa zamu yi, bana son rana tayi mana".

Gwaggo ta ce "Gadanga, sai dai kayi tafiyarka kai ka
ai, ina sane na tura ruma can, sai za a koma makaranta zan dawo da ita da kaina, yanayi ya nuna mini babu isasshen tsari a jikinta, kuma akwai bu
atar ta zaga ta san dangin mahaifinta suma su santa"
Aliyu ya ce "Amma gwaggo ba mu yi haka da mama ba, dan Allah kar ki yi mini haka".

Gwaggo ta ce "Mhmm, sai kuma ka yi, na gama magana"
Saroro Aliyu ya yi ya ma rasa mai zaice, ya ciro wayarsa ya kira mama a waya.

Yana kira mama ta
aga ta yi sallama.

"Mama, gwaggo fa ta tura ruma wani
auye, wai ba zamu taho tare ba sai an koma makaranta zata da wo da ita".

Gwaggo ta
aga murya ta ce"Eh, ni na ce ba zata dawo yanzu ba, sai na gama nema mata tsarin jiki, sannan kuma ta san dangin mahaifinta, tunda ba zuwa take ba"
Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Aliyu ka taho kawai, idan ka tsaya zai zama abin magana,
yaleta taho"
"Amma mama...

"Kar ka ce komai, in dai ruma ce, da kansu za su tattaro su dawo da ita, ka taho ka barsu".

Ayshercool.
*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Abin da gwaggo ta yi ba
aramin
atawa Aliyu rai yayi ba, da ya san haka ne da ba zai ta
a bari ta saka a kai ruma ko ina ba, daga zuwa ziyara kawai ta ri
e 'ya wai sai wani lokaci.

Ya sake duban gwaggo ya ce "Gwaggo, ruma fa ba zata yarda ta zauna a garin nan ba, rigima za ta yi miki idan ta dawo ta tarar na tafi na barta".

Gwaggo ta ce "Babu komai, na san yadda zan shawo kan kayata, amma a yanzu dai ba in da zata".

Takaici ya ishi Aliyu, ya bi gwaggo da kallo.

"Gadanga ko dukana zaka yi ne?

Na gama yanke hukunci, idan kuma kaima zaka zauna ne ni haka nake so, sai mu zauna idan lokacin yayi sai ku tafi duka".

Tabbas ba dan gobe yana da test mai muhimmanci a makaranta ba zama zai yi, ya saka lawalli a gaba sai ya kai shi ya
auko ruma, amma ba yadda iya ya
auki jakarsa ya fice.
****
Har Adam yayi kwanakinsa uku a birnin tarayya, bai iya aikata komai ba, saboda da ya fita da niyyar zuwa wani wuri, sai jiki ya hau rawa kai ya hau ciwo, ga ruma da ta addabawa rayuwarsa ya kasa mantawa da ita, komai yake yi sai ya din ga ganinta.

Bayan ya cika kwanaki hu
u, ya kira Ammi yayi mata
aryar bai gama abin da yake yi bane, sai dai tattaunawar haka aka yi ta babu shi, duk da halartarsa tattaunawar na da matu
ar muhimmanci.

A kwana na biyar ya kira direbansa a waya, ya ce ya zo da mota ya same shi a hotel
in da yake.
arfe biyu direban ya sameshi, sai dai a wannan karon cikin ikon Allah tun da ya fito sau
aya kan ya sara, jiri ya
ebe shi, amma
ya tattara nutsuwartsa, yana addu'a, ya nufi motar.

Suka gaisa da direban nasa, yayi masa ya hanya, daga nan ya ce ya gaya masa in da zai kai shi.

Mintuna ashirin ce ta kaisu, a harabar wata plaza suka yi parking, Adam ya bu
e motar ya fita.

Wani matashi ne zaune wanda zai yi sa'an Adam, yana danna computer, yana ganin Adam ya mi
e cikin girmamawa yana murmushi ya ce "Barka da zuwa"
Adam ya
arasa yana murmushi, ya mi
a masa hannu suka gaisa, sannan ya zauna.

Matashin ya kalli Adam ya ce "Adam, ya aka yi an shirya zama da kai, amma ba ka yi attending ba?, na din ga kiran wayarka ba ka
agawa, har wayar ma ta daina shiga gaba
aya?"
Adam ya
an taune lips
insa na
asa ya ce "Am sorry Habib, wata matsala aka samu, amma komai normal yanzu in sha Allah".

Cikin kulawa Habib ya ce "Are you safe?"
Adam ya jinjina kai sannan ya ce "Me aka tattauna, wace matsaya aka cimma?"
Habib ya
an rausayar da kai ya ce "To, mun tattauna yadda yakamata, amma dai kamar yadda na yi maka bayani da farko, ko da ka fito
arara ka bayyana lamarin nan, ko an je kotu za a sake su, saboda haryanzu baka da wata cikakkiyar hujja ta zahiri da zaka kafa, yanzu ko kun yi wani abu a kai, ya riga ya gama shiri, da tattaunawa da lawyoyinsa, ya shirya tsaf da ka yi attacking zai yi depending, yanzu abin da yafi shine ka sake mayar da hankali sosai da kai da abokan aikinka, ku samo hujja ta gaske, ta zahiri da za ayi amfani da ita, nima zan shirya tsaf domin cimma nasara ni da tawagarmu"
Adam yayi ajiyar zuciya tare da dafe goshinsa, ya sake
agowa ya kalli Habib ya ce "Duk wata hanya da zan bi domin neman hujjar kama mutumin nan an tosheta, kuma kullum kallon mutunci ake masa, ana sake bashi girma tare da shigar da shi cikin al'amuran
asar nan, bayan su ne babbar matsalar mu"
"Adam, tun da ka ga haka, ba shi ka
ai bane, ko dai an san me yake yi ake rufa masa asiri, ko kuma akwai wasu manyan da suke aikin tare "
"Haka ne, abin da nake tunani kenan nima, amma babu komai in sha Allah zamu yi nasara, zan cigaba da
ari, ina son magana da saifu ma, zan zauna a garin nan sai Allah ya kaimu monday zan koma kano".

Habib ya ce "To shikenan, Allah ya yi jagora, gashi ko shayi ban baka ba"
Adam ya girgiza kai ya ce "Kar ka damu"
Daga haka Adam ya tashi ya fita, ya saka direbansa ya mayar da shi masauki.
Chapter 57 · 0% Book details