← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 116

Sashe 114

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wai yanzu rahoton cikin gidana shine labarin ya
awa a media dan a
ata mini suna"
Jamil ya ce "Ni kaina abun ya girgiza ni, na rasa yadda aka yi maganar nan ta fita a haka, tun
azu ni da Jabir abun da muke tattaunawa kenan, yadda za a shawo kan matsalar nan, amma ya kake gani, me ka shirya gayawa duniya domin wanke kanka?"
"Ba ni da isasshen lokacin da zan
ata wurin
arin wanke kaina a idon duniya, ina da abubuwan yi da yawa a gabana, kuma ba za a kawar da hankalina a kan abubuwan da na sanya a gaba ba, duk wanda yake ganin yana da wani
orafi, ko son tuhumata a kan mutuwar matata, idan yana da shaida ya kaini kotu" yayi maganar yana jin kamar za ayi masa kallon wawa abun da ya fa
Jabir ya waro ido ya ce "Yanzu kana nufin haka zaka zuba ido a cigaba da
ata maka suna?"
"Idan sun gaji zasu daina, idan kuma basu gaji ba zasu cigaba, idan na cigaba da
arin wanke kaina, za su cigaba da
arin kaini
asa, idan na tsaya a kan
afata na cigaba da kar
ar duk abun da za'a ce kaina, wataran gaskiya zata yi halinta"
Jamil ya ce "Amma kana ganin hakan mafita ce adam?

Duk abun da ya shafeka ya shafi masarautar garin nan ne fa kai tsaye"
Adam ya ce "In da nake godewa Allah kenan, atleast masarautar nan wani immunity ne a gareni"
Su da suka san Adam da saka abu a rai, da shiga damuwa sun yi mamakin yadda yau ya nuna halin ko in kula da wannan lamarin.

Jabir ya ce "To, bari mu ga zuwa yaus
he wannan mafitar taka za ta kawo sauyi ga lamarin nan, amma a ganina kamar kasada ce hakan, Allah ya yi mana jagora"
Adam ya amsa da Amin, ya mi
e ya ce "Bari zan shiga gari na ga Bashir, gobe in Allah ya kaimu zai bar gari, ina da muhimman abubuwan da zamu tattauna".

Jamil ma tashi yayi ya ce "bari nima na gangara gida, na gaida Alhaji, sannan na wuce gida sai sa safenku".

Jabir ya ce "To Allah ya bamu alkhairi"
Kamar yadda Jamil ya fa
a, gida ya wuce ya je ha gaida mama da turaki, sannan yayi aniyar tafiya gidansa, Samha ce ta bi yo shi, tana kiran sunansa.

Ya tsaya yana jiran isowarta, ko sa ta
araso, hannunsa ta ja ta ce "Mu je motarka mu yi magana" bai musa mata ba suka wuce motarsa, suka shiga.

Shiru ne ya
an ratsa, daga bisani ya
an numfasa ya ce "Ina jinki"
Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "A duniya bayan mama bani da wani kamarka yaya jamil, mama ta kasa fahimta ta, ban sani ba ko kai zaka fahimceni, domin kuwa kaine dai-dai da zamanin da muke ciki"
Jamil ya ce "Haka ne, ina saurarenki".

"Yaya jamil game da takawa ne"
Ya dubeta ya ce "Takawa again, me kuma ya faru?".

"Maganar nan ce dai ta shekarun baya, tun da Aisha ta mutu ina son maye gurbinta, na so na je wurin baba da kaina, amma sai na ga rashin dacewar hakan, ka taimaka yaya kai ka
ai zaka fahimci halin da nake ciki"
"Wai ke samha ba zaki
yal adam ba kamar baki da zuciya?

Duk cikin tarin samarinki babu wanda zaki fitar ki aura sai shi dai?"
Kamar ta fashe da kuka ta ce "Da zan iya cire shi daga zuciyata da tuni na yi, dan Allah ka taimakeni yaya jamil"
Jamil ya
an yi shiru sannan ya ce "Zan fara yi wa adam
in maganar na ji mai zace"
Da sauri ta ce 'A'a dan Allah kar ka gaya masa yanzu, turaki zaka fara yi wa zancen"
"To amma kin san magana yanzu ba zata yiwu ba, tun da haryanzu ana cikin alhinin mutuwar nan"
"Ohhj God, to sai zuwa yaushe kenan?"
'dole ki yi ha
uri, lokaci ya
an tura ka
"To shikenan na gode, ina saurarenka ka gaida gida " ya jinjina mata kai, ita kuma ta bu
e motar ta fita, tana jin a jikinta kamar a wannan karon za ayi nasara.

Kamar wutar daji, haka Zancen mutuwar aisha, ya cigaba da zaga gidan jaridu, da kuma kafafen watsa labarai, yayin da ta
angarensa ya
i cewa kowa komai, kuma ya
i magana da kowane
an jarida.

A yau babu tsammani, mai girma turaki ya kar
i ba
uncin wambai da misalin
arfe tara na dare.

Turaki yayi mamakin ganin
an uwan nasa a wannan lokacin, amma ya
oye mamakinsa, ya kar
e shi.

Wambai ya ce "Na san zaka yi mamakin ganina a wannan lokaci, sai da ba komai ne ya kawoni ba, illa zuwa in sake tabattar da abun da kunnuwana suke jiye mini, kuma ka yi burus, ba ka ce da ni komai ba"
Cikin rashin fahimta, turaki ya ce "Meke nan kake nufi?"
"Maganar rasuwar
ar wurinka aisha mana, ko kai ba ka jin jita-jitar da ke ta yawo a kan mutuwarta?"
Turaki yayi murmushi ya ce "Alhamdilillah, da kai da kanka ka ce jita-jita ne, nima haka nan na tsinci zancen"
"Turaki na zuwa na yi domin mu yi wasan barkwanci ba, gaskiyar lamari zaka sanar mini, gaba
aya mutuncin masarauta na nema ya zube, martaba da kimar gidanmu adam na ta cigaba da rusata sa shi da uwarsa, wannan wane irin abu ne?"
Turaki ya girgiza kai ya ce "Na san mai
akina ce ta je ta gaya maka wasu abubuwan, maganar da ke yawo a gari, tabbas aisha ta mutu a hannun 'yan bindiga, amma ba adam ne sila ba, ko ya kasheta ya sha jininta ba kamar yadda ma
iya ke ta kwarmato, kuma yarinyar da aka tsaresu tare ta zo da yaron wurin aisha".

"Turaki kana nufin goya masa baya wurin
oye laifinsa, dan me za a ce a
asar waje ta mutu a
oye gaskiya, wannan banzan aikin da yake yi na shishshigi ga manyan
asar nan da kawo
arshensu, ai gashi shi zasu kawo
arshensa, ko iya wannan labarin an yi mana mummunan tambari, a ce an samu babbar zuriya kamar ta mu da
arya.

Dan haka dole a hukunta adam, sai ya yi wa duniya bayanin yadda matarsa ta mutu domin wanke ahalinmu daga mummunan zargin tsafi da kisan kai, ga uwa uba ayar tambaya a kan yaron da ake ce nasa ne, na baku awanni arba'in da takwas, idan har bai yi abun da na ce ba, matakin da zan
auka a kan sa ba zai yi muku da
i ba.

Kai banda tsabar rashin sanin ciwon kai, kamar ba
arka ba wane irin abu ne haka?"
Turaki ya ce "Da Adam da A'isha, duk tsatso
aya ne, kuma
anmu ne, dukkansu.....

Bai
arasa ba, wambai ya
aga masa hannu tare da fa
in.

"Ba nasiha nake bu
ata ko tunatarwa ba, martabar ahalinmu da sarautarmu nake
arin karewa, dan haka ayi abun da muka umarta, ko a ga ba dai-dai ba"
Turaki yayi ajiyar zuciya, ya bi wambai da kallo, da ya tashi fuuuu ya fice.

Yayi ajiyar zuciya yana jin wani irin matsanancin tausayin Adam.

Duk wannan kumfar bakin da wambai yayi, ya biyo bayan ziga da kuma famfon da Mummy ta je har gida ta yi masa tare da taimakon hajiya sauda, shi kuma kamar kullum ya hau kai ya zauna ba tare da bincike ba.

Rumaisa har islamiyya ta koma, in da malamai da
alibai suka din ga yi mata barka da arziki na ku
utowa daga hannun
an bindiga, sai dai a wannan karon ma, duk yadda
an bugun ciki, suka so ta basu labarin abun da ya faru da ita
i ta yi, wasu har suna cewa rumaisa ta koma saliha.

Bayan tashi daga islamiyya, ta wuce gidansu habiba, dan tun da ta dawo ba ta je gidan su habiba, suka rungume juna suna tsalle a tsakar gida.

Daga bisani suka zauna suka hau hira, mamansu habiba ta zubo musu
an wake, suka kewaye suna ci suna hira.

"Ruma ina yaya Aliyu ne?"
Ruma ta kalleta ta ce "Meyasa ki ke nemansa?".

"A'a, tun a asibitin nan ban kuma ganinsa ba"
"To meye ha
inki da shi, to idan son sa ki ke yi, zaki dinga sai mini kayan da
i kina bani"
Waro ido habiba ta yi ta ce "Astagfirullah, dan Allah ruma ki daina yi mini haka, baki san kirkin da ya yi mini ba lokacin da nake zuwa gidanku da ki ka
ata, mai sunan baba yayi ta hararata, shi yake rarrshina ya dawo da ni gida".

Ruma ta kwashe da dariya, ta ce "Allah sarki habibata, kamar ba nan muke kwasar dambe da ke ba, ke ni shawara zaki bani ma"
"Shawarar me" habiba ta yi maganar tana su
e hannunta.

"Mutumin nan da ya
wace mini jaririna, wai ya zan yi da shi ne in kar
ana?"
"Wai
wace jaririn suka yi gaba
aya to saboda me?"
"Saboda wula
anci mana, kullum da tunanin yaron nan nake kwana nake tashi, babarsa fa cewa ta yi ta bar mini shi, amma ya
wace mini shi.

Habiba kin san in da kotu take?
ararsa zan je na kai, ba dama an ce zulai ta kai
ara kotu al
ali ya bata
an ta ba, to nima kotu zan kai shi".

Habiba ta
an yi shiru ta ce "Tsoro nake ji ruma, kin san ba a wasa a kotu"
"Na sani, ai ba wasa zamu je ba,
ara zamu kai".

Habiba ta ce "To, a unguwar su babanmu akwai kotu, dama za ayi sauka a gidan, sai ki zo mu je".

Ruma ta yi murmushi ta ce"Amma na ji da
i habiba, Allah ya kaimu in sha Allah sai an bani
a na, bari na tafi gida" ta mi
e suka fita tsakar gida suka wanke hannu, ta yi wa maman Habiba sallama sannan ta tafi gida.
Chapter 114 · 0% Book details