← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 116

Sashe 25

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata irin gigitacciyar dan
a Uamar ya yiwa kunnenta, ta kurma ihu, ya janyota har tsakiyar tsakar gidan, ya dungurar da ita, ya na
e hannun rigarsa cikin tsawa ya ce"Ina ki ka je da aka aike ki?"
Cikin ki
ima da razani, ruma ta wassafa komai, ba ta
oye ba ciki har da zuwa wurin aski da yadda ta
au keke tana tafe tana fa
uwa, duk ta gurje gwiwa, da yadda bayan ta dawo daga aike ta tsaya wurin 'yan bikin da ba ta san suwaye ba ma, tana rawa tana satar ku
in li
Sai a lokacin ta fa
i har fa
a suka yi da yaron dj yana ce mata shegiya
arauniya.

"Yanzu ina ku
in da ki ka
ebo
in?" Yayi maganar yana mi
a mata hannu.

Aikuwa ta zura hannu a rigarta, sai ga ku
i, a
alla idan aka
irga sun kai dubu uku da
oriya.
(SORRY FOR THE LATE UPDATE, AYYUKA SUN YI YAWA NE, INA GODIYA DA TARIN ADDUOI DA
AUNAR DA KU KE WA BOOK
ANWAR MAZA)
Ayshercool
08081012143
[13/07, 9:01 pm] JAKADIYAR AREWA:
ANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing
YouTube channel
@Cool Hausa Novels, domin samun da
an litattafan hausa na sauraro.

Mai sunan Baba ya kalleta a tsanake ya ce "Sata ki ka koma yi kenan ko?"
Ta girgiza kai da sauri ta na zazzare ido.

"Ba zaki bu
e baki ki yi mini magana ba?"
"A'a Yaya wallahi ba sata nake yi ba"
"To idan ba sata ba, me ki ka yi, kin san su masu bikin ne, ko kuma sun sanki, idan ba sata ba baki suka yi, ko nan aka aike ki?" Ta girgiza masa kai.

Ya ce "Good, tashi ki je ki yi alwala ki yi salla, zan gauraya da ke, tashi maza ina jiran ki"
Huzaifa da yake ta huci, ya cika ya batse kamar ya sha yeast ya ce "Wallahi yau sai na lallasaki, za ki gane baki da wayo"
Gwaggo ta ce "Ku dai din ga ha
uri yarinya ce,
uruciya ce kawai take damunta"
Huzaifa ya yi
wafa ya ce "Ba
uriciya da yarinta ba, Allah ya sa
anyar
walwa ce a kan ta da ba ta nuna ba, sai na lallasata na koya mata hankali"
Duk da tana cikin tashin hankalin rashin sanin hukuncin da za ta fuskanta, hakan bai hanata murgu
awa Huzaifa baki ba, tana harararsa, duk da laifin da ta tafka masa.

Daga shiga ban
aki alwala ta tsiri kashi, duk dan ta
ata lokaci kar ayi mata hukunci mai wahala, ta na fitowa, Umar ya ce a tsakar gida za ta yi sallar, dan haka ta
au hijjabi ta tayar da salla.

Ita kanta ba ta san adadin raka'ar da ta yi ba, kawai yin sallar take cike da zullumi, a sujudar
arshe kuwa kai kace neman gafara take ko bacci tayi, amma babu
aya nazari kawai take.

Haka ta idar ta saka addu'a, abin da ba ta saba ba, ko sallar ta yi sai mama ta yi ta fa
a sannan take zaman yin addu'a.

Ganin ta
i sallame addu'a ne ya sanya Umar yi mata wani irin kallon, da babu shiri ta shafa addu'a ta tashi.

Ya ce "Oya, kamun kunne"
Cikin marairaicewa ta ce "Dan girman Allah Yaya.....

"Shut up!

Zaki abin da na ce ko kuwa?"
Jiki a sanyaye, ta dur
usa ta kama kunnenta, nan da nan jikinta ya hau rawa, ta fara gajiya ta saka kuka.

Gwaggo ta ce "Kai ina mace ina wannan goho, kai meyasa ba ka tsoron Allah ne?

Ke tashi dalla wannan wace irin azaba ce?"
Ruma ta ce "A'a Gwaggo, ba zan iya tashi ba sai ya ce dan Allah ku tayani bashi ha
uri"
Mai sunan Baba yayi shiru, ya
i kula Gwaggo, ta dubi mama ta ce "Ke ba zaki saka baki ya ce ta tashi ba, tun da ni ban isa ba?"
Mama ta ce "Ba haka bane Gwaggo, ai gara a din ga hukunta ta idan ba haka ba, sangarta da rashin jin da zata yi sai Allah ruma ba ta ji sam"
arshe mai sunan Baba ya tashi ya bar gidan ma gaba
aya ruma kuma ko da wasa ba ta tashi ba daga kamun kunnen, sai dai ta cika musu gida da koke-koke da magiya.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah mama ki saka baki, na tuba na bi Allah, dan Allah ki bashi ha
uri ya ce in tashi"
"Babu ruwana, ba dai ba kya ji ba, ai na gode Allah da ya bani wa
anda zasu hukunta ki idan ki ka yi ba dai-dai ba, kuma kar ki sake kiran sunana"
"Wayyo Allahna na shiga uku, wallahi mama zan iya rasuwa, kaina da wuyana ciwo suke yi mini, bana son na mutu yanzu, bana nafila karatun Alqur'ani ba kullum nake yi ba, gashi ina yi miki abin da ba kya so, bana son na mutu yanzu ban tuba ba, wallahi mama zan iya rasuwa a wurin nan"
Yasir ya ce "Ba ki jigata bane ba, da ki ke iya wannan surutun"
Gwaggo ta ce"Ji min kafirar yarinya, ba nace ki tashi ba kin
i, ni babu abin da ya
ular da ni, irin wannan goho da ya saki kina 'ya mace, kema da azababben taurin kai na ce ki tashi kin
Ruma ba ta kula Gwaggo ba, sai cigaba da rusa kuka da tayi, tana magiya da neman taimako.

Cike da
uluwa Yaya Aliyu ya ce"Ki yi mana shiru dan ubanki, tun da ba wani ne ya aike ki ki aikata abin da ki ka yi ba" haka ruma ta ja bakinta ta tsuke, tana kuka
asa-
asa dan wasu lokutan yaya Aliyu ma ba daga nan ba wuri8iya tsare gida da hukunci, dan daga yaya Umar sai shi a zafi.

Har mai sunan Baba ya dawo ruma tana nan tana aikin kamun kunne, tana yi tana fa
uwa tana tashi.

Sai da ya dawo sannan ya ce ta tashi, kuma ya ce mata washegari za su gauraya.

Tana mi
ewa tsaye jiri ya kwasheta sai amai, Gwaggo ta fito da sauri ta kama ruma, kanta sai juyawa yake saboda azabar wahala.

A zaune ta yi alwala tayi sallar isha'i, ko abinci ba ta nema ba, ta kwanta saboda galabaita, cinyoyinta sai azabar ciwo suke yi mata, dama da fari suna ciwo saboda hawan keke, gwiwoyinta na ra
i saboda duk ta
uje su saboda keke, yanzu kuma ga kamun kunne, jikinta kamar an mata duka haka take jin ta, a take wani irin wahalallen bacci ya kwasheta.

Sai dai kwana ta yi da wani irin zazzafan zazza
i, wanda ita kanta ba ta san ya hau ta ba, jin surutan ta ya yi yawa a baccin ne ya sanya mama zuwa ta ta
a jikinta, ta ji da zafi sosai.

Duk da mama a
ule take da ruma, haka ta fita ta
ebo ruwa ta sanya
aramin towel, ta din ga shafawa ruma ruwa a jikinta.

Tun asubar fari kuwa, ruma amai ne ya tasheta, saboda har a lokacin jiri take yi.

Yanzu ma a zaune ta yi sallar asuba, ta nemi wuri ta kwanta.

Tun mama na basar da ita, har kuma ta fara damuwa, Gwaggo kuwa ta samu wuri
aya ta zauna sai mita take na masifa a kan mama tana gani aka bawa ruma gwale-gwale amma ba ta ce komai ba.

Bayan gari ya gama wayewa, Gwaggo ta karya ta yi haramar tafiya, sai dai a lokacin ruma ta samu bacci, dan a galabaice take.

Gwaggo ta ce kar a tasheta, Abdallah ya tafi rakata tasha, suna ta murna zasu huta, dan dama Gwaggon ta ishe su,
ruma ce kawai take son zamanta a gidan.

Mama ta tashi ruma, ta matsa mata a kan lallai ta ci Abinci, ta na ci tana kuka ta
an sha tea ka
an ta kuma kwanciya, sai dai ko mintuna goma ba ayi da cin Abincin na ta ba, ta tashi ta cigaba da amai.

Ba shiri mama ta ce Aliyu ya zo ya kai ruma chemist a dubata.
yar take iya tafiya, suna tafe tana kuka, har sai da ran Aliyu ya fara
aci, amma ya shareta suka cigaba da tafiya a hankali.

Cikin sa'a kuwa suka tarar ya fito, kasancewar asabar ce, ranar ba ya zuwa aiki.

Ya na ganinsu cikin kulawa ya ce "Subhanallah, 'yar gidan mama yau ke ce ba lafiya?" Ita dai ba ta iya magana ba ta nemi wuri ta zauna.

Aliyu ya zauna ya rungumeta, saboda
arin fa
uwa take yi.

"Meya sameta haka?"
Aliyu ya ce "Ina ga zazza
i ne dai, da amai ta fara jiya"
Bakinta bai mutu ba, ta ce "Kamun kunne aka sakani, kusan awa goma shine ya sani rashin lafiya"
"Subhanallah, waye ya saki kamun kunne kuma?"
"Mai sunan Baba ne"
"To ki yi ha
uri, yanzu dai zan
ibi jininki na yi miki gwaji, in duba meye ya haddasa zazza
iban jinin da za'a yiwa ruma, tamkar za a cire mata ido, ta dinga kurma ihu, tana fizge-fizge, ga ta da shegen
arfi, da
yar Aliyu ya ri
eta aka
ebi jinin nan.

Kuka har da majina, Aliyu ya dinga dungure mata kai yana zaginta.

Ya gama gwaje-gwajen da zai yi mata, ya ce "Malaria ce ke damunta, dan haka akwai bu
atar ayi mata allurai, da kuma magunguna"
Ruma ta yi masa zuru da ido, tana jiran ta ga a ina za ayi allaurar.

Ya ha
a alluransa ya nufo ta, ta mi
e tsaye.

"Ke malama ki tsaya, dan ba zaki sake wahalar da ni ba"
"To a ina za ayi mini allurar?"
Mai chemist ya ce "Ai a baya ake yin ta"
"Wai bayana" tayi maganar tana nuna bayanta.

Nasiru mai chemist ta ce "A'a a mazaunai"
"Suwaye mazaunan?"
Aliyu ya ha
e rai ya ce "Ke juya ki tsaya ayi miki allurar nan mu tafi, kin san sarai a in da za ayi".
Chapter 25 · 0% Book details