← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 116

Sashe 115

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan har da wanda za'a zarga a kan mutuwar aisha, to ba kowa bane ba face ni mahaifinta, domin ni na
oye ainihin abun da ya faru, adam ba matsafi ba ne, bai kashe aisha ba, kuma bai yi tsafi da gangar jikinta ba, a madadinsa, ina mai baiwa al'umma ha
uri na
oye ha
anin gaskiyar abun da ya faru.

Mummy ta yi jifa da wayar hannun ta, bayan kammala karanta abun da turaki ya sanar da
an jarida, ya wanke adam.

Ayshercool.
*Paid book ne,
500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*
Masifa mummy take kamar ta ari baki, duk
arin da ta yi, amma turaki lokaci
aya ya watsa komai.

Takawa ma mamaki ne ya kama shi, da ganin abun da turaki ya ce, ya wanke shi ya
au laifin, bai jira komai ba ya tafi gidan turaki.

Bayan an yi masa iso ya shiga sun gaisa da turaki, ya dubi turaki ya ce "Allah ya baka yawan rai,
na ga abun da ka gayawa manema labarai, amma ni yakamata na
au wannan laifin na magantu ba kai ba".

Turaki ya murmusa ya ce "A'a mu
in ne dai yakamata, wambai ya zo nan ya nemi mu sanya ka fito duniya ka bayar da ha
uri, a kan abun da ya faru, wai sunan masarauta na neman
aci saboda kai, hakan ya sanya ni na bayar da ha
urin, kar ka ji komai"
"Amma Allah ya taimake ka..."
Turaki ya girgiza wa adam kai ya ce "An rufe wannan babin, ina
a ta?"
Adam ya ce "Wace
ar ta ka?"
Turaki yayi murmushi ya ce "
a ta yarinyar da ta kawo jikana, rumaisa"
Adam ya
an tsuke fuska ya ce "Tana gidansu"
"Allah sarki, duk lokacin da aka ganta, ace muna gaisuwa, Allah ya
ara mata lafiya" turaki yayi maganar yana murmushi, yana tuna lokacin da rumaisa ta zauna a gabansa tana ta zuba shirme son ranta.

Haka adam ya tashi ya tafi, yana ta tunani kala-kala a ran sa.

Idan har turaki zai fito duniya ya kareshi, zai iya fuskantar duniya ya ce duk mai cigaba da zarginsa idan yana da hujja.

Kansa na kashe aisha ya je ya nema mata hakkinta a kotu.

'kar dai shawarar wannan yarinyar mara kan gado zaka
auka, ta kai ka ta baro' wata zuciyar ta garga
e shi, tsaki ya ja ya kawar da wannan tunanin a ransa.

Maganar da turaki ya fito ya yi, ta
ara yamutsa hazo, kowa da abun da yake fa
a, yayin da hakan ya
ara tunzura wambai, turaki ya
ara zubar musu da mutunci ta hanyar kare adam.

Yau kwanaki kusan bakwai rabon rumasa da jaririnta, dan haka ta shiga damuwa ba ka
an ba, tana ta tunani daban-daban a zuciyarta.

Wata irin
ishirwar son ganin yaron ke damunta.

Ta gama shirinta tsaf za ta tafi makaranta, ta fito daga gida har ta nufi hanyar makaranta, ta kalli ku
in makarantarta a hannunta, kawai ta canza hanya, ta nufi titi.

Ta san ku
in hannunta ba zai kai ta gidansu takawa ba, dan haka ta sa
i hanya da
afafuwanta ta dinga tafiya kamar mara hankali.

Tun da sanyin safiya, har rana ta
aga ta fara jin zafinta sosai a jikinta.

Idan ta gaji ta zauna ta huta, idan ta huta ta tashi ta cigaba.

Sai da ta ci fiye da rabin tafiyar sannan ta samu napep ta yi masa magiya ya
auke ta, shi ma in da ya ajiyeta da sauran tafiya, ta sauka ta cigaba.

Sai dai da ta
arasa, tana zuwa
ofar gidan, security suka tare ta.

Ta kalli wanda ya sha gabanta ta ce "Wucewa zan yi"
"Ki je ina?" Ya tambayeta.

"Ciki mana wurin
ana, ko ba ka gane ni ba ne?".

Ya ce "Na gane ki, sai dai an ce kar mu sake barinki ki shiga idan ki ka zo?"
Cikin mamaki ta kalli securityn ta ce "Waye ya ce kar a sake barina na shiga?"
"Takawa, shi ya ce kar ki sake shiga idan kin zo in ba shi ya ce ba"
"Kam bala'i, wai wannan wane irin mutum ne, shi wane irin azzalumi ne, idan har ba zan din ga shiga ba, ya bani
ana mana, ai dai ya san ba maula ce take kawo ni ba ko?"
"Ke da shi ne wannan, matsa daga nan"
Wata irin zuciya ta turnu
o rumaisa ta ce "Wallahi ba in da zani sai an bani
a na, wallahi yau sai na shiga gidan nan, wane irin mugun mutum ne shi, ba shi da imani ba shi da tausayi, wallahi sai na shiga sai dai ku kasheni" ta yi maganar tana tunkarar gate
Tare gate
aya yayi, cikin tsawa wani ya ce mata "Ki ka motsa daga nan sai na harbeki"
"To ka harbenin mana, sai me?

Allah sai na shiga"
Gaba
aya ta rasa abun da za ta yi, ta fashe da kuka, saboda uwar wahalar da ta shawo, kan ta samu ta zo, amma ta tarar wai an hanata shiga.

Ta fi mintuna talatin a tsaye a rana tana kuka,
aya daga cikin masu gadin ya ce "Wannan wace irin jarababbiyar yarinya ce haka?"
"Kai ne baka santa ba, kwanakin baya ta ta
a zuwa gidan nan, zata aikata fiye da abun da ta yi yanzu"
Kamar daga sama, ta hango shi yana tunkaro
ofar gidan, sanye da
anan kaya, kunnensa
aya da Bluetooth, fuskar nan tasa fayau ya yi
iba abunsa, kan ya
arasa gate
in rumaisa ta tashi da gudu, ta je ta ri
e rigarsa tana kuka.

Sororo yayi yana kallonta, "Shi ne kace idan na zo kar a sake barina na shiga, ka san da haka ka kar
e mini yarona?

To ka shiga ka
auko mini sabir ba zan sake zuwar muku gida ba"
aya daga cikin security zai yi magana, ya
aga masa hannu ya dakatar da shi, ya kalli rumaisa ya ce "Wane jaririn ki ke magana a kai?"
Waro ido rumaisa ta yi ta ce "Ni zaka rainawa hankali ka mayar mahaukaciya, wato ma baka san wane jaririn nake magana a kai ba, wallahi sai na
ebo maka
an sanda, ko kuma tun da kai ma
an sanda ne, na san ha
a baki zaku yi, al
ali zam je na gaya wa, kuma ka bani
ana ba zan sake zuwar muku gida ba"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, mu shiga ki ga
an na ki, sakar mini rigata".

"Wallahi ba zan cika ka ba, ka gudu su hanani shiga" ta
ara ri
e masa riga, suka nufi gate
"Ranka ya da
e, Yalla
ai ya ce kar a sake bari ta shiga".

"Ni kuma na ce sai ta shiga, ko nima an hana ni shiga ne?"
Ya girgiza kai, suka bu
e gate
in, suka shiga, sai da suka zo
ofar shiga sashen ammi, sannan ta saki rigarsa ta shiga ciki da sauri.

Sai dai tana shiga babban falon ammi, abun da ta gani ya razanata.

Turus!

Ta yi ta tsaya, Adam ta gani a zaune sanye cikin suit farare, da shi da ammi a falon, sabir a kan kujera yana barci.

Ta waiwaya ta kalli hanyar da ta shigo, sannan ta kalli in da Adam yake.

Ammi ta ce "Rumaisa daga ina haka?"
arasa ta zauna, safarta tayi futu-futu saboda tafiyar
afa, ta zauna ta ce "Tun safe nake tahowa, da
yar na zo gidan nan, dan na ga sabir, amma da na zo aka hanani shigowa, wai ya ce idan na zo kar a sake barina na shigo, sai kuma na ganshi ya zo wucewa zai shigo gidan nan, tare muka shigo na bar shi a waje, amma kuma da na shigo na ganshi a nan a zaune, a waje da
anan kaya na ganshi, amma kuma a nan na ganshi da wasu kayan".

Tayi maganar tana kallonsa.

Adam bin rumaisa ya yi da kallo, yana mamakin anya kanta
aya, jin ta ce da
afa ta taho, kuma yanayinta ya tabattar da hakan.

Ammi ta ce "Ohh Mahmud ya shigo gari kenan?"
"Waye Mahmoud?

Ba shi na gani a waje ba kenan?".

"Ba shi ki ka gani ba" Ammi ta bata amsa.

Rumaisa ta gyara zamantaz tana shafan kan Sabir, sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce "Allah sarki, Allah ya sa idan na fita na ganshi na bashi ha
uri ban san ba shi bane ba, na yi ta masa masifa*.

"Amma rumaisa ba makaranta zaki je ba na ganki da uniform?".

"Makaranta zani, amma na kasa jurewa, ba bu abun da nake so sai in ga sabir, amma na zo wai an hanani shigowa, ban da dalilin sabir ma ni mai zai kawoni gidan nan, ina ga ma alhakin yaran mutane da nake cin zali ne ya kamani, Allah ya jarrabeni da son yaron da ake wula
anta ni a kansa, bakomai wataran sai labari"
Maimakonsa ammi ta ji maganganun rumaisa sun yi tsauri, sai ma wani irin tausayinta da ya kamata, lallai rumaisa tana cikin jarrabawa ta gaske saboda sabir.

Ammi ta ri
e hannunta ta ce "Rumaisa, babu mai wula
antaki a kan sabir, sabir
anki ne, ki yi ha
uri zan
au hukuncin da ya dace a kan Adam, amma daga yanzu duk lokacin da ki ke son ganinsa, akwai lambata a wayar mamanki, ki kirani ni kuma zan saka a kawo miki shi, ko na kawo miki shi da kaina, kin ga yanzu kin yi missing school, bari ya mayar da ke gida, tun da dama wurin aiki zai koma"
Rumaisa ta girgiza kai ta share hawaye ta ce "A'a, zan koma gida da kaina, kuma ba zan sake zuwa gidan ba, balle masu gadi su ci mutuncina a waje kamar yadda aka yi mini yau kamar
ar maula" tayi maganar tana sake fashewa da matsanancin kuka.

"Kiyi ha
uri, in sha Allah hakan ba zata sake kasancewa ba, babu mai sake wula
anki a kan sabir, ko shigowa gidan nan, tun da gidanku ne, bari a kawo miki ruwa ki sha, ki ci abinci sai ya mayar da ke gida".
Chapter 115 · 0% Book details