← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 116

Sashe 10

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da yarinta ta ce "Nan da kwana biyu ranar asabar kenan, in Allah ya yarda zan tuna miki ki gaya mini"
"Ba wanna kwana biyun nake nufi ba hansai, sai kin
ara girma da hankali"
Cikin mamaki Ruma ta ce "Yaushe kuma zan
ara girman da hankali, wancan karon ma fa na ta
a tambayarki menene MATA MAZA, ki ka ce mini sai na girma, na tambayeki menene haila ki ka ce mini ba yanzu ba, amma da zan yi wani abun sai ki ce ina girma amma bana hankali wane irin girma ki ke son nayi to?"
"Ke tashi ki wuce ki kwanta dan uwarki, kawai kin saka mutane a gaba da tambayoyinki na shirme, ko a gidan uban wa ki ke jiyo wannan manyan maganganun oho miki, wuce kan na karya ki biyu, ba zaki tambayi abu daidai da hankalinki ba sai wanda ya fi
arfin kanki" sai da ta kalli in da Yake zaune yana bata umarni, bayan da fari yayi kamar bai san me suke yi ba.

A hankali ta tashi ta nufi
aki, tana tunanin menene aibun tambayarta?.

Tafiya ta yi
aki, ta gyara shimfi
arta ta kwanta, tana tunanin meyasa kullum tayi tambaya sai ace mata ba yanzu ba sai an kwana biyu, ko ace wai tana tambayoyin da suka fi
arfin
walwarta me hakan yake nufi kenan?.

Da wannan tunane-tunanen bacci yayi awon gaba da ita.

Da safe tana kwance tana baccinta, duk samarin gidan sun gama komai, har abin karyawa, Kasancewar Asabar ce Ruma tana ta baccin asara, ba aikin fari balle na ba
i, har
asan ranta tana matu
ar jin da
in rashin zuwa makarantar allo da ba ta yi, saboda tana samun isasshen lokacin bacci.

Ji take ina ma ace bokon ma ta daina zuwa, idan tayi baccinta ta
oshi da yamma ta kfa suyar wainar fulawa a
ofar gida ta tara 'yan ku
enta.

Baccin yayi mata da
i, tayi nisa sosai a duniyar mafarkai kala-kala, ta ji kamar daga sama ana taka mata
afa.
e ido tayi a hankali, amma ta
i motsawa, tana son ta tabbatar da a zahiri ne ko duk cikin mafarkin ne.

Ji tayi an kuma zungurarta da
afa, ba tare da ta waiwayo ba ta ce "Wallahi Huzaifa zan maka rashin mutuncin da baka ta
a tunani ba, kar ka sake takani"
Bai ji kashedin ba, ya sake haurinta da
afa, "Allah ya isa wallahi, kuma ba zan tashi ba" tayi maganar tana sake dun
ulewa a wuri guda.
ashin bayanta ya kuma daka da
afarsa, ta yin
uro a matu
ar zafafe, da nufin ta kafa masa ha
ora ko a ina ne, amma me tayi tozali da Umar a tsaye a kanta.

Jikinta ne ya hau tsuma, ta ma rasa me za ta yi, ko ta ce.

Shiru yayi yana nazartarta, daga bisani ya ce "Ki tashi ki je ki ki yi wanka ki karya ina jiranki, kuma idan ki ka
ata mini lokaci kin san sauran"
Saroro tayi tana kallonsa, da ba ta gama fahimtar me yake nufi ba.

"Za ki tashi ko sai na yi ball dake?" Cikin hanzari ta tashi, ta
auke katifarta ta nufi ban
aki tana mamakin to ina zasu je, kar dai boarding
in zai kaita kamar yadda ya ce.

Gabanta ne ya fa
i ta fara tunanin ko ta gudu.

Kai tsaye ta nufi ban
aki, tana shiga ta tarrar da an ha
a ruwan wanka, ba tayi tunanin ko ruwan waye ba, ta rufe
ofa ta hau wanka da shi.

Yasir ne ya nufo ban
akin da sauri, wuyansa
auke da soson wankansa, zai shiga ban
aki saboda ya kai ruwan wankansa, amma yana zuwa ya ga
ofar a rufe.

Iya
arfinsa ya hau dukan
ofar yana fa
in "wani
an rainin hankalin ne ya shiga bayan na kai ruwa?"
Gyran murya tayi masa, tsaki ya ja ya ce "Ki hanzarta zan yi wanka na fita na kusa makara.

Tun yana saka ran zata fito har ya tashi ya fara zaginta yana bugun
ofar.

Ba ta da tabbacin wankan da tayi ta fita, ta bu
ofar ban
akin, zagi ya dinga surfa mata, bai kai ga rufe baki ba, idonsa ya sauke a kan bokitin da ya ha
a ruwa, Ruma ta zubar da komai.

A hasale ya zura hannu ya janyota tsakar gida ya ce "Wallahi yau mai
watarki sai Allah, na zuba ruwa na kai zan fita makaranta kina can kina bacci, amma ki zubar mini".

Babu alamar nadama ta tsuke fuska ta ce "To ba Yaya Umar ne ya ce nayi wanka ba"
Wani ran
washi ya yi mata a tsakiyar ka, da azabar zafinsa ya sanya ta dur
usa a kan gwiwoyinta, tana sakin wani irin kuka mai sauti.

Yaya Umar ya
aga labulen taga ya le
o ya ce "
yaleta tun da ka daketa" ba
aramin
aci ran Yasir yayi ba, dan niyyarsa sai ya yiwa Ruma dukan da duk taurin kanta sai ta bashi ha
uri.

Kasa karyawa tayi saboda kuka, tana tsaye tana duru-durunta, Umar ya shigo hannunsa ri
e da leda ya mi
a mata ya ce "Maza ki shirya ki wuce mu tafi"
ar ledar tayi tana duddubawa, uniform ne na islamiyyar su Huzaifa, makarantar da ta ce ko aljanna ake rabawa a cikinta ba zata yi ta ba, saboda azabar tsaurinsu, asabar da lahadi tun tara sai biyar ake tashi, ba a fashi balle makara, ga haddar Alqur'ani ake yi da gaske ba wasa ba.

Saroro tayi tana kallon Yaya Umar, cike da rashin fahimta amma ta kasa yi masa Magana.

Wata uwar harara da ya yi mata ne, ya sanya ta shiga
akin Mama, ta saka uniform
in jikinta sai tsuma yake yi, ita ta san har ga Allah ba zata iya zaman makarantar nan ba.

Mama dai ba ta ce musu kanzil ba, ya tasa ta a gaba suka tafi.

A zuciyarta tana ta addur Allah ya sa makarantar suce ba zasu kar
eta ba, bata tunanin ko su Huzaifa sun san za a sakata a makarantar su, dan da sun sani cewa zasu yi basu yadda ba.

Tun da suka shiga makarantar, tashin karatun Alqur'ani kawai ka ke ji, daga kowacce kusurwa, kuma da alama
aliban makarantar a nutse suke.

A ofishin shugaban makarantar aka titsiye Ruma ana yi mata interview, amma ba abin da ta iya, izifi biyun da aka yi mata tambayoyi da
yar ta kai.

Umar ya shiga tunanin tsawon lokacin da Ruma ta shafe tana zuwa makarantar allon nan, me take yi da ta kasa izifi biyu.

Ransa ba
aramin
aci ya yi ba, ya hau ta da fa
a a gaban mutane.

Cikin kuka ta ce "Wallahi yaya na iya karatu"
"To uwar me ki ka iya, kin kasa izifi biyu"
an yi shiru sannan ta ce "Eh na iya, amma ba a allona na rubuta na iya ba, na allon wani almajirin malam babba ne, idan aka
ara masa nake iyawa, ni kuma sai na kasa nawa"
Murmushi malamin yayi ya ce to biya mu ji "Tiryan-tiryan da
ira'ar warsh, take karanta suratul Yusuf, ko tuntu
e babu"
Shugaban makarantar yayi mata kabbara ya ce "Ahh gaskiya 'yar baiwa ce, zamu san a in da yakamata mu sanyata, daga islamiyyar har tahfiz
in, zaku ga sauyi in sha Allah zata yi karatu"
Yaya Umar ya ce "To masha Allah, haka muke so" aka saka wani malami ya kai Rumaisa aji.

Tare suka fito da Yaya Umar, ya dubi Ruma ya ce "Ga makaranta nan na kawo ki, idan kin ga dama kiyi karatu, idan baki ga dama ba nan ma ki yi musu halin naki, kiga abin da zai biyo baya" ta sunkuyar da kai kamar ta Allah, yayi fa
ansa ya gama ya tafi.

Gaba
aya ba tayi murna da zuwa makarantar nan ba, haka aka kai ta aji ta nemi wuri ta zauna.

Gaba
aya
aliban sun mayar da hankali, suna ta zuba karatu, Ruma kuwa sanyin fanka ne ke nema ya sanyata bacci.

"Ke ya ba kya karatun?" Cewar malamin da yake kula da karatun nasu.

Kallonsa ruma tayi, shima uniform ne a jikinsa na
alibai, amma ya tsaya zai yi mata iyayi.

"Sabuwar zuwa ce ni, ban iya wurin ba" ta bashi amsa kanta tsaye.

Bai kuma saurararta ba, ya cigaba da tilawar tare da sauran
aliban.

Ta dubi wata
aliba ta ce "Ke, dan Allah nan aji nawa ne?"
alibar ta kalli Ruma sannan ta ce "Aji
aya ne"
"Kutmar, ban gane aji
aya ba, kina nufin aji
aya aka kawo ni?"
"Eh mana" yarinyar ta bata amsa.

Ruma ta jinjina kai ta ce "Lallai ma an raina mini hankali, wallahi ba zan zauna a aji
aya ba".
aliban suna ta tilawarsu, yayin da malamin yake jin haddar wasu, amma Ruma hankalinta na kan yadda zata fita daga ajin, dan zaman ajin ya isheta.

Daga bisani ta koma gefe ta hau gyangya
Lokacin da aka fita break, yunwa ta saka Ruma a gaba, dan ba ta karya ba Yaya Umar ya taso ta a gaba.
alibai ne masu yawa sosai a makarantar, dan makarantar sananniya ce sosai a unguwar, dan kusan babu ta biyunta.

Daga yanayin mayar da hankalin su Huzaifa da yadda suke bayar da labarin tsananin makarantar ya sanya ta ji ba ta son makarantar sam.

Tun da aka fita break da salla, wuri
aya ta samu tayi zamanta tana bin ko ina da kallo, sai da ta gaji ta tashi ta fara dubawa ko zata ga Yasir ko Huzaifa amma babu wanda ta gani a cikinsu.

Haka aka koma aji ba tare da ta samu komai ta saka a cikinta ba.

Aka dawo aji aka
ora da karatu babu
autawa, gaba
aya Ruma ta gaji da zaman makarantar.

Malamin ajinsu ya fara yi musu
ari, ta bu
e Alqur'anin ta ajiye, ta cigaba da gyangya
inta.

Tun da Ruma ta shigo ajin
azu yake kallonta, sam ya lura babu alamar son karatun a tare da Ruma, daga hamma sai bacci take yi.
arshe ta ha
a jakarta ta cewa malamin fitsari take ji, ya ce taje tayi, ta
au jakarta ta bar ajin.
Chapter 10 · 0% Book details