← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 116

Sashe 64

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yi mana shiru ko in taka ruwan cikinki"
"Wallahi ba zan yi shiru ba, wayyo Allah mama yaya Aliyu yaya usy dan Allah ku zo ku
aukeni zan mutu, wayyo Allahna" kuka take sosai kamar wadda wani iftila'in ya afkawa.

Wata mata ce ta din ga rarrashin ruma tana bata ha
uri da
yar ta yi shiru, ta cigaba da nanata addu'ar nan.

Mai sunan Baba kuwa yadda yaje ya tarar da gwaggo ne ya sanya jikinsa yin sanyi, ya tarar iya ma tana asibitin ita da mijinta, gwaggo sai kuka take ba ta ko cin abinci, likitoci na ta fama jininta ya sauka abu ya gagara, saboda yadda ta addabi kanta.

Tana ganin mai sunan Baba ta sake rushewa da kuka, "Dan girman Allah ku yi ha
uri, ku yafe mini umaru ban zaci abin zai kasance a haka ba, tsananin
aunar da nake yi wa
an uwana ce na mayar kanku, ban yi hakan dan ba
anta muku ba, son da nake wa ruma ya sanya na hanata, da na san haka za ta faru da ba zan ce ma azo da ita ba, ku yafe mini dan Allah" gaba
aya suka fashe da kuka, har su iya da su Lawisa da aka sace ruma a gabansu.

Ganin yadda dattijuwar ke cikin tashin hankali ita da iyalanta ya sanya ya ji duk jikinsa yayi sanyi, idan ya ce zai
aga musu hankali bai yi musu adalci ba, tun da suma ba da son ransu hakan ya faru ba.
arasa ya zauna a gefen gadon gwaggo sannan ya ce "Ki daina kuka, ko dan saboda a samu jininki ya sauka, yanzu ya ake ciki an sanar da jami'an tsaro ne ko kuwa ya ake ciki?"
Dagaci ya ce "Ka san garin namu, jami'an tsaro ba su fiye bamu agaji ba, mu da su mutanen muke yin sulhu, duk abin da muka saka jami'an tsaro wata
arnar suke yi mana, amma dai saboda ita rumaisan mun sanar da jami'an tsaro, amma sun ce mu jira abin da 'yan bindigar suka ce sai a sanar musu, muna nan muna jira haryanzu dai ba su yi mana aike ba".

Mai sunan Baba yayi shiru ya ma rasa abin da zai ce,
arshe ya yanke shawarar a kai shi wurin 'yan sandan domin ya ji meye abin yi.
anlami ya
auki mai sunan Baba suka tafi, sai dai daga
auyen da aka sace su ruma zuwa wurin 'yan sandan uwar tafiya ce mai zaman kanta, da ko menene zai samu 'yan garin ba lallai su samu
aukin jami'an tsaro.

Ganin girma da kwarjini da kuma ganin cewa Umar ba
an garin bame ya sanya DPO garin tsayawa ya saurare shi.

"To
an uwa idan zan baka shawara ka koma gida kawai ku yi addu'a, bin bayan mutanen nan aikin sojoji ne bana 'yan sanda ba, mu mun yi iya namu
arin, sai dai mun bar sallahun idan sun yi wata magana a sanar mana, haryanzu dai ba su ce komai ba"
Shiru kawai mai sunan Baba yayi, ba zaka
ara sanin lamarin tsaron
asarmu ya ta
are ba sai wani iftila'i ya afka maka.

Ba tare da samo wata mafita ba, mai sunan Baba ya kamo hanyar kano.

Gidansu ruma kuwa tamkar an yi mutuwa, ko magana mai sauti ba sa iya yi, tun da mama ta
an samu
warin jikinta ta hau sallaya, canza alwala ce kawai take
agata, yunwa kuwa ko jinta ba ta yi.

Ba yadda ba su yi da mama ba a kan ta ci abinci, ta ce su
yaleta kawai.

Ko da ta ji sallamar mai sunan Baba, ji ta yi kamar zai ce mata ga ruma nan ya dawo mata da ita, amma ko da ya shiga
akinta ta kalleshi ta ganshi shika
ai, sai ta sunkuyar da kanta
asa, ta ji zuciyarta ne neman karyewa.
arasa gaban mama ya zauna, su Abdallah duk suka zubo masa ido, amma ya rasa ta ina zai fara yi musu bayani.

Mama ta sake
aga kai ta kalli ta mai sunan Baba, ya girgiza mata kai ya ce "A dage a cigaba da Addu'a kawai"
Wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya mama ta sauke, ta sake sunkuyar da kanta
asa.

Huzaifa ya fashe da kuka, Yasir ma ya taya shi.

Cikin dakiya mai sunan Baba ya ha
e rai ya ce "Meye haka kamar wanda ba su je islamiyya ba, ba ku yi imani da
addara bane?

Yanzu kuka ne ya kamace ku ko kuma addu'a?" Haka ya din ga yi musu fa
a alhalin shima da zai samu space kukan zai yi.

Ya tashi fuuu ya tafi
akinsu, yana zuwa ya tarar da Abubakar a zaune yayi shiru ya lula duniyar tunani.

Mai sunan Baba ya zauna a kusa da shi, ya ce "Akhi na dawo?"
Banza yaya Abubakar ya yi masa bai kula shi ba.

"Na san na yi maka laifi, amma yakamata ka yi mini uzuri, ba a hayyacina nake ba, idan ka gama fushin sai mu yi magana" ya yin
ura zai tashi Abubakar ya ce "Yaya ku ka yi da ka je, an samu labarinsu?"
"Babu wani labari mai da
in ji, sai ma kayan takaici, ance mu saurara idan sun kiramu sun ce mana wani abu shikenan sai mu sanar".

"Idan kuma ba su kira ba a haka zata cigaba da zama a hannunsu?"
"I have no idea" mai sunan Baba ya fa
a cikin damuwa.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Aki meye abin yi?"
"Addu'a" ya bashi amsa a ta
aice.

Dare ya tsala, wasu daga cikin al'umma sun kwanta suna hutawa, yayin da wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da iyalansu suke kwanan zaune, ciki har da mama da yaranta maza yayyen ruma gaba
aya mama ta manta da wani abu wai bacci a wannan halin da take ciki, a zaune take tamkar an dasata tun tana iya lazimin da addu'a har ta kasa ta rasa abin da ma zata ja.

Zuciyarta sai zafi take mata, da tunanin a wani hali ruma take ciki.

Wurin baccin ruma ta kalla, da yanzu tana nan mama tana faman gyara mata kwanciya ko tashinta fitsari, da yanzu ta yi
ai sauro na cizonta mama tana mita tana sake gyarata, ko ta
aro fanka idan ta fuskanci zafi yayi mata yawa, ko ta kashe fanka ta lullu
eta idan sanyi yayi yawa.

"Ruma ko a wani hali kike?

Ko kina raye?

Ko kin ci abinci?

Ya in da ki ke kwance?

Sanin gaibu sai Allah, ya rabbilarshil azim, dan girmanka Allah ka tsare mini 'ya ta da sauran 'ya'yan musulmi, Allah ka dawo mini da ita cikin aminci" ta
arasa addu'ar kuka yana kufce mata, sai a lokacin ta
an ji nutsuwa da ta samu hawayen idonta ya zuba.
akin 'yan mazan ma gaba
aya idonsu biyu, wasu da Alqur'ani wasu a kan sallaya, wasu suna kuka, dan basu ta
a tsintar kansu a cikin mummunan tashin hankali kamar wannan ba.

Ruma ta yi rigingine a filin Allah, wani irin sanyi yana ratsata ga cikinta kamar ya ha
e da bayanta saboda azabar yunwar da take ji, ga
ayi da jikinta yake mata saboda rashin wanka, ga wani irin sauro na bala'i da
wari suna gasa mata cizo.

A hankali ta furta "Mama, mai sunan Baba" sai kuma ta yi shiru hawaye ya fara zirarowa ta gefen idonta.

Tana tsaka da tunanin, wurin yayi tsit, mutanen sai kewayasu suke yi da manyan bindigogi.

Wani irin sauti ruma ta din ga jiyowa na motoci
asa-
asa, daga bayan dutsen da ke nesa da su.

"Sha tara ga motocin smoke can suna aiki fa" cewar
aya daga cikin 'yan bindigar.

" 'yan wahala ba, ni mamaki nake yadda suke iya fitar da sabgar nan ba wata matsala"
ayan ya bashi amsa.

"Haba, sun gama sai ta komai nake gaya maka, babu wanda ya isa ya tare musu hanya, babban controller na
asa ma fa nasu ne, kuma akwai na sa kason a ciki mu suka mayar 'yan iska kawai".

Sha tara ya ce "Aikuwa sai mu yi tawaye, ko dai su yi wani abu a kai ko mu bujure, haba ma'adanan nan fa da suke kwasa ba dan muna gyara musu aikin nan ba da ba zai yiwu ba, amma kura da shan bugu gardi da kwashe ku
"Kai ni ba wannan ba ma, oga nake jira ya zo ayi wadda za ayi a san yadda za ayi da mutanen nan"
"Eh gobe zasu shigo ai"
Haka suka cigaba da hirarsu, amma kan ruma ya
aure, wasu ma'adanai ake kwasa meye ma ma'adanan?

"Zan yi fitsari" ta fa
a cikin rawar murya".

"Yi a nan"
ayan ya bata amsa.

"Ina jin yunwa ma"
"Idan ki ka kuma magana sai na taka ruwan cikinki"
Guntun tsaki ruma ta yi, tayi juyi wani abu da ba ta san menene ba gasa mata cizo, wata uwar
ara ta saki, ta mi
e tana kuka.

"Wai wannan wace irin iblishiyar yarinya ce meye kuma?"
"Wani abu ne ya cijeni" ta yi maganar a gigice tana soshe-soshe.

"Nemi wuri ki zauna ki rufewa mutane baki, ni wallahi da oga ya zo da na da
e da harbe wannan shegiyar yarinyar da ba ta rasa matsala".

"To ku mayar da ni in da kuka
auko ni mana, meyasa zaku kawo ni nan" tayi maganar a sangarce
Hasketa
ayan yayi da hasken fitila, ta saka hannu ta kare tana motsa baki, saukar wani abu ta ji a goshinta mai nauyin tsiya, daga haka ba ta sake sanin in da kanta yake ba.

Bayan sallar asuba, su Abdallah suka sanar da abin da yake faruwa a masallaci, tare da ro
on bayin Allah su taya su da addu'a, Allah ya fito da rumaisa cikin aminci da
oshin lafiya.

Mutane da yawa sun ka
u da jin abun da ya samu ruma, dan ruma ta mutane ce, da yawan mutane sun santa, kan gari ya gama haske unguwar su ta cika da labarin yin garkuwa da ruma.

Gari na gama yin haske aka din ga sintirin zuwa yi wa mama jaje, tare da addu'ar Allah ya bayyana ta.
Chapter 64 · 0% Book details