← Book details Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 116

Sashe 14

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hanya ta biyo ta filin ball
in su Yaya Aliyu, maza sun yi cincirindo, ana kallon ball, ta tsaya tana le
awa ko zata hango yaya Aliyu.

Kutsawa ta dinga yi, sai gata ita
aya a cikin maza.

"Ruma me ki ke yi a nan?" Ta
aga kai ta kalli mai maganar, abokin Aliyu ne.

"Yaya Aliyu nake nema"
"To ai yana cikin fili, ball yake"
"To ai na sani, kallonsa zan yi"
Ya jinjina kai ya ce "To ai shikenan"
Kamar daga sama ya ji ana kiran sunansa, da 'yar siriryar muryarta.

Duk da yadda ya taso ball
in a gaba, amma sai da ya tsaya ya waiwaya.

Ruma ya hango a gaban garada, tana
ago masa hannu.

Waro ido ya yi, ya nufi in da ruma take.

Coach
in su Aliyu ya fara masifa, dan ajiye ball
in da ya yi, ya waiwaya aka ci su
aya.

"Ke me ki ke yi a nan?"
"Wucewa zan na ce bari na zo na ganka"
Ya dafe kai ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ki wuce ki tafi gida"
"Dan Allah ka bari na gani"
Hankalinsa na kan ruma, coach kuma na ta masifa.

"Kai dalla wacece wannan, ku koreta daga wurin nan".

"Wallahi ba inda zani, ai wurin yayana na zo".

Aliyu ya kalli abokinsa ya cewa "Aminu, dan Allah jire mini yarinyar nan" ya koma cikin filin yana waiwayenta.

Aminu ya bata wata
atuwar jaka ta zauna a kai, ita ka
ai mace a cikin maza.

Yana ball
in amma hankalinsa yana kanta.

Ta dinga yi masa tafi tana bashi
warin gwiwa, kusan duk hankali ya dawo kanta, gaba
aya ta bawa wasu dariya a wurin.

Da yaya Aliyu ya ci ball kuwa, ta dinga tsalle tana murna, ya ci ball biyu.

Da aka tashi har hoto aka yi mata, ita da Aliyu ta ri
e kofin da suka ci, kasancewar ball ce ta cikin unguwa.

Ba a tashi daga ball
in ba, sai ana kiran sallar magariba, mama tana can ta sa an yi sahu ya kai uku a makarantar su, ana nemanta.

Suna tafe a hanya tana yabawa yaya Aliyu, abokansa sai tsokanarsa suke yi a kan ruma.

"Yaya Aliyu, akwai wani wanda kuna ball
in, ya dakar maka
afa, na ji haushi idan na ganshi sai na buga masa dutse wallahi".

"Ni ban saki ba, kuma baki ga an bamu pk ba da ref ya gani"
"Oho ni na san wani pk, amma da ka tsaya ja masa duka ka rama, daga wasa sai cin zali"
Haka suka
arasa gida, mama na tsaye da carbi a tsakar gida, tana tunanin ta ina ruma zata dawo.

Sai gata ita da Aliyu, yana ri
e da hannunta.

Mama ta kalleta ta ce "Ke daga ina?"
Sai a yanzu ta tuna daga islamiyya ko gida ba ta zo ba, ta kalli ya ya Aliyu ya kalleta.

"A ina ka ganta?" Mama ta tambaye shi tana kallon ruma.

Aliyu ya ce "wallahi mama nima kawai ganinta na yi a filinmu, ban san ina za ta tsaya ba idan na ce ta taho, shi ya sanya na ce ta tsaya"
"Kina mace uban me ya kai ki filin ball?" Huzaifa yayi maganar a
ufiule, dan takalminsa har tsinkewa ya yi saboda nemanta.

Hararsa tayi ta sake no
ewa a jikin Aliyu.

Duka Huzaifa ya kawo mata, Aliyu ya tare ta, ya ce laifina ne duk Allah ya baku ha
uri.

Mama ta fara tunanin anya ba zata kai ruma wurin malaman ru
iyya ba, abin na ta ya fara bawa mama tsoro sosai da sosai.

Kamar yadda ruma ta saba kwatsa zance, bayan kowa ya halarra, haka yau ma sai da kowa ya halarran, an gama cin abinci sannan ta gyara murya ta ce "Yasir, wai yaushe ku gama karatun
azu da naje ajinku".

"Ban sani ba" ya bata amsa.

"Mhmm ai dama ba zaka sani ba, nifa gaba
aya mutuncin malamin nan ya zube a idona, wallahi mama idan kin ji me yake gaya musu sai kin ri
e baki, duk da wani abun bana ganewa, duk basu san daga waje ina jiyowa ba, kuma maimakon Yasir ya fito daga ajin nan, amma ina yana zaune ana koya musu abin da bai kamata ba.

Saroro yasir ya yi, ya ji me aka koya musu da bai kamata ba, suna ha
a ido da ruma, ya tuna karatun da aka yi musu, kan ya kai ga
aukar mataki ta ce "Ina ji ai yana ce muku, wai ko idan mutum ya rungume mace alwalarsa ba ta karye ba, ko kiss, dan Allah wannan mama ba iskanci bane da
ata tarbiyya, nan idan muna kallo aka nuno kiss
auke tashar ake yi, amma wai malaminsu yake gaya musu.

Kuma naga ai turawa ne kawai suke rungume-rungume da kiss, mu wannan ba
abi'ar mu ba ce amma yake gaya musu, wallahi makarantar nan
ata tarbiyya ake yi".

"DAN
ARI!!"
GODIYA GA TARIN MASOYA MASU BIBIYAR LITTAFIN
ANWAR MAZA, COMMENT
IN KU NA SANYA NI NISHA
I, KAR A MANTA DA SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL
IN MU DOMIN SAMUN DA
AN LITATTFAN HAUSA NA SAURARO.

AYSHERCOOL
08081012143
[25/06, 4:11 pm] JAKADIYAR AREWA:
ANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing
YouTube channel
@Cool Hausa Novels, domin samun da
an litattafan hausa na sauraro.

Dafe goshi Yasir ya yi yana murzawa a hankali, ruma 'yar bala'i ce, ba zata tashi yi maka hansfree ba a cikin jama'a sai kowa ya hallara kamar mai sanar da wani abu mai muhimmanci, in da ya gode wa Allah da ya kasance, a makaranta ta ji ana koya musu, da bai san da wasu kalaman zai amfani wurin kare kansa ba.

Ita kuwa ta za
ale tana ta jawabi, babu wanda ya tanka mata, karo da idanun Umar ne ya sanya mata aya a jawaban da take kwarowa babu
autawa.

"Zo nan" yayi maganar cikin bada umarni.

Kamar mara gaskiya haka ta tashi ta je gabansa ta dur
usa.

"Je ki
auko mini jakarki ta makarantar boko da ta islamiyya"
"Dummm ta ji gabanta ya fa
i, har gara jakar islamiyyar ta ma, tun da ba a da
e da sakata ba litattafan da mutuncinsu, amma ta makarantar boko dai kam sai dai Allah ya kyauta.

Jiki babu
wari ta je ta kwaso jakunkunan, ta zo gabansa ta ajiye su.

Ya kalli jakarta ta makarantar boko, duk ta ci ubanta da jagwalgwalon biro, har da zanen 'yan aljanu a jiki da su ABCD a jikin jakar, sunan 'yan gidan nan kuwa babu wanda ba ta rubuta a jiki bs.

Tun daga nan ya san cikin jakar ma ba za ayi abin arziki ba.

"Oyaa zazzage litattafan na gani"
Babu musu ta janyo jakar ta zazzage, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, litattafan nan sun ga duniya, tamkar
era ya ci rage mata.

Kaf litattafan babu bango a jikinsu, sun yi kaca-kaca, wasu ma nanna
e su tayi, wasu ta ninka su biyu, a ta
aice kai ka ce bolar wani office
in ce.

Sai uban fensura sun kai biyar a cikin jakar, ga su ulu da farar
asa da sauran goriba duk a ciki.

Umar ya kalli ruma, ya kalli bolar dake gabansa, dan ba zai ce litattafai ba.

"Yanzu wannan sharar ce litattafan karatun naki?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai.

Ya sanya hannu ya
au littafi
aya yana dubawa, ba uwar da take yi a ciki, littafi
aya sai ta yi duk subject
in da ta ga dama a ciki.

A hankali ya cigaba da duba litattafan nata, ga class work da tarin assignment, wasu tayi ta ci zero wasu makin da take ci ma gwanin ban haushi, subject
aya ya ga ta mayar da hankali tana yi yadda yakamata, kuma ba ta fa
uwa shine maths.

Yayi ajiyar zuciya ya
aga kai ya kalleta ya ce "Ashe asarar ku
in tara kawai ake a banza ko?

A biya miki ku
in makaranta idan zaki tafi sai an baki abin tafiya makaranta, amma ki je kina wannan jakancin, kalli wai wannan ne litattafan ki na karatu, kalli wannan wai 4\20 ki ka ci, ba zaki iya kawo abin da baki iya ba gida a koya miki, wasa da surutun banza fa
i ba a tambaye ki ba shi ki ka saka a gaba ko?"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
arya na yi miki kenan?

To bari ki ji na gaya miki, ina nan zan zuba ido a kan result
in da zaki kawo wannan karon, wallahi idan bai yi mini ba sai an miki repeating "
Ras!

Gaban ruma ya fa
i "Na shiga uku, dan Allah ka yi ha
uri, zan daina surutun in dinga karatu".

"Kar ma ki yi, wallahi primary 1 zan saka a mayar da ke, ki cigaba da da
anci, kuma ina samun information a kan abin da ki ke a islamiyya, ke kin zama jan wuya zaman ajinku ma ba kya yi, ke kin sakawa kan ki ba zaki iya karatu ba ko?

Oya bu
e Alqur'ani nuna mini a surar da ku ke"
Ai nan ma badan-badan tayi ta yi, domin kuwa ba ta san a ina suke
in ba.

Carbi ya bata, ya biya mata aya biyu, ya ce tayi ta maimaitawa sai tayi
afa dubu.

Da haka yaya umar ya
waci yasir, ta zauna ta dinga nanata karatu har barci ya fara
aukar ta, da ta fara bacci yake zuba mata carbi a
afa, ta tashi a gigice ta cigaba da karatun, da haka sai da ta haddace rabin shafi, bai
yaleta ta kwanta ba sai wurin
arfe
aya na dare, da kuka haka ta kai karatun nan, ya sa ta kwashe bolar litattafan ta ya sallame ta.

Washegari, har makarantar boko, yaya umar ya je ya iske ta, ya kai mata sababbin litattafai, ya sanya aka kirawo ta ofishin shugaban makaranta, nan ma ba abin da suke yi, sai wassafawa yaya Umar halin ta na rashin ji.
Chapter 14 · 0% Book details